A ZATO NA COMPLETE

Nace “hmm, Anty sai ki dinga yi kamar baki san komi ba wallahi. Ki duba fa irin zaman da kuke yi da taki kishiyar a nan gidan. Sannan ki fa duba yadda yanzu aure yake mutuwa, abin har ya zama kamar yayi. Idan kuma kika yi duba, mafi yawa rabuwar auren kishiya ce take haddasa shi. To idan kishiya daya ta fitar da mace daga gidanta, ni da zan zauna da kishiyoyi biyu fa? Ai ko barbashin toka ta ba za’a gani ba”.
Anty Alawiyya da Janan dake gefena a zaune suka kwashe da dariya, na harareta abinda nafi yi tunda aka daura min aure.
Anty Alawiyya tace “ke yanzu zaman gidan nan namu har zaki iya kiranshi zaman kishi?”, ta girgiza kai, “ba zaman kishi muke yi ba Na’ilah, zamane muke yi irin na mutanen farko. Kafin hasken musulunci ya sauko, zama na rashin adalci, amma ba kishi bane. Ai ba haka kishi yake ba. Kishi shine inda zaki fito ke da kishiya, ku hada kirji ke da ita, ku rikita mijinku da ririta ta hanyar kissa, ladabi da biyayya, domin neman fada a cikin zuciyarshi. Kishi ba bin bokaye da malamai bane domin neman gurbi a cikin zuciyar miji, a kuma muzgunawa wadda ake zaune da ita, wannan jahilci ne.”
“Ni kaina daga farko wannan shine tunanina akan kishi, sai daga baya na fahimci sam ba haka bane, ashe shirme ne. Shi yasa nake matukar kokarina wajen ganin cewa kin fahimci shi zama da kishiya, wallahi ba matsala bace, ba kuma damuwa bace. Matukar kina da gurbi a cikin zuciyar mijinki, kin kuma kama shi kam kin rike, to abinda kike bukata kenan. Me zai yi ruwanki da wata kishiya can? Ita dai ba ita ta zaunar dake ko take ciyar, da shayar dake ba. To menene abin tada jijiyoyin wuya? Yanzu baki ga yadda muke namu zaman ba ne? Ita ce babba, amma wa kika gani yana jan ragamar gidannan gabadaya yanzu?”.
Nayi shiru ina jinta, da gaskiyarta. Yanzu ita ce take juya gidannan son ranta, har shi Baban. Ko hidimar bikin nan da aka yi, komi a hannunta yake, kowa ita yake nema idan wata bukata ta taso. Babu ma wanda yake wani tunkarar Ramata, dama bata saka kanta cikin hidimar bikin. Na kuma kula tunda na dawo gida hutun sallah dama kamar fadarta tayi kasa a wajen maigidan, har yanzu dai Anty Alawiyya ce take murza kambun mulkinta.
Tace “bana so ki bi hanyoyin da zafin kishi ya sanya ni bi Na’ilah, hanya ce halakakkiya mai halaka mutane, sai wanda Allah ya tseratar ne kadai yake tsira. Don haka ne nake so ki kwantar da hankalinki, ki tattara shi waje daya ki mayar kan mijinki, ki maida wata matsalar kishiya gefe, zaki ga duk su din ba wasu abubuwa bane, zaki kuma ce na fada miki watarana. Amma kafin nan sai kin kai zuciya nesa, kin kuma yi hakuri, amma da yardar Allah watarana sai dai ki tuno kiyi dariya kawai. Sai dai hakan ba zai faru ba, sai kin tashi tsaye, dole sai kin nemi taimako da tsari daga ayoyin Allah. Tsafi gaskiya ne, kuma a yadda nake jin labarin wannan kishiya taki, ba karamin dabi za’a sha da ita ba. Dole sai kin dage”.
Wadannan maganganu su suka kwantar min da hankali. Na karbi kofin rubutu data bani, nayi bismillah na sha. Daga nan kuma naci gaba da amfani da sauran magungunan.
Cikin ikon Allah, kafin zagayowar sati, ni a karan kaina naji canji a cikin jikina sosai. Mafarkan da nake yi ba daina yin su. Haka naji a hankali idea din zama da su Raheemah da Ameerah ya daina terrifying dina sosai. Da idan na tuno yanzu sun zama kishiyoyina, kuma zan zauna dasu, sai inji har numfashi nake fitarwa da kyar. Amma a yanzu, sai inji idea don’t is not that bad. Har zama zamu dinga yi ni da Janan muna hira a kansu, tace zata so taga expression din Raheemah lokacin da Yaya zai fada mata ya kara aure, kuma ba wata bace ya aura face ni. Ni kaina da nayi kokarin yin picturing yadda zata yi a lokacin sai naji ina fashewa da dariya. Muka hau kyalkyala dariya ni da ita kamar wasu sababbin kamu, sai da Anty Halima ta leko tana fada sannan muka dan saurara.
Ranar Alhamis aka yi min turaren jiki dana gashi, kasancewar wancan a kurarren lokaci ne, ba’a samu anyi komi ba. Bayan anyi turaren, wata kawar Kulsum tazo ta kama min gashi ta kitse shi sosai, karshen kitson sai data dinga sanya white gel tana kame min shi saboda kada ya warware da wuri. Ranar har dare muna tare dasu muna ta hira. Makitsiyar Nana, tana bamu labarin irin zaman kishin da aka buga a gidansu, su saboda tsabar damben da matan gidansu suka yi, gidan yan dambe ake kiran gidansu a unguwarsu.
“Amma yanzu gashi hakan ya zama tarihi, Anty ma Inna Hadiza take kiran babarmu yanzu”. Duk muka kwashe da dariya. Haka dai muka wuni muna shan hirarmu da abokanmu.
Washegari kuma ranar Juma’ah, Anty Halima da Janan suka riga mu tafiya Zaria jeren kayan daki. Sun ce wasu ma guda biyu da zasu tafi da kayan daki daga Gashua zasu je can Zaria din, zasu hadu. Muka yi sallama dasu.
Ranar assabar, karfe tara na safe, motoci biyu suka fara danna horn a kofar gidanmu. Dama sun ce da safe masu daukar amaryar zasu zo.
Tun da safe Anty Alawiyya tasa nayi wanka, ta dauko wata doguwar rigar gown ta wani yadi na saka.
Tun bayan da aka daura auren, aka mayar da duk wasu kudi da kayan Dr. Na Abba dake hannunmu. Wannan rana rigar ta jikina ma, Anty Sa’a yayar su Janan ce ta kawo min ina washegarin daurin aure da tazo, kala biyar ne ire-iren su masu kyau. Dama tana kawowa Janan ta zare wannan rigar tace ranar da za’a kaini zan sanya ta.
Bayan na gama shiryawa, muka tafi dakin Baba yin sallama. Tun lokacin idanuna suka fara raina fata. A dakin Baba, nasiha yayi min sosai akan rayuwar aure da kuma muhimmancin yin hakuri a cikinta, ya rufe da yi min addu’a da fatan alkhairi a cikin rayuwar aurena. Tun ma kfin ya gama, na kuka sosai na tashin hankali.
Ya dauko kudin da aka biya na sadakina, dubu dari biyu cif babu ragi babu kari, ban ma san abinda zanyi dasu ba, kai kawai na girgiza mishi.
Yace “ba zaki amsa ba nufinki?”
Na gyada mishi kai, yace “ai ba za’a yi haka ba Na’ilah, hakkinki ne. Amma tunda kin nuna ba zaki amsa ba, zan turawa Yayanki kudin, ba za’a rasa abinda za’a sai miki dasu ba. Hakan yayi?”. Na gyada mishi kai.
Yace “to madallah. Sai ku tashi kuyi haramar tafiya, Allah ya kiyaye hanya, Allah ya tsare. Allah yayi miki albarka Na’ilah!”.
Hakan shi ya sa na kara fashewa da wani kukan mai sauti, tunda muke da Baba, sai yau ne na taba jin kalmar sanya albarka ta fita daga bakinshi. Ban san abinda zanyi ba a lokacin, da yafi inyi kuka.
Kafin in fita daga dakinshi, Maryam ta fita da akwatuna biyu da aka shirya min kayana a ciki zuwa cikin mota, da sauran tarkace. Jiya aka tafi da duk wasu kayan bukata, tun daga kayan gara, kayan kicin da sauransu.
Daga dakin Baba, ko dakina ban koma ba, aka yi waje dani. Sai da muka fita sannan muka ga Ramata cikin tawagar masu bankwana da amarya, na matsa muka yi bankwana dasu ita da sauran yara da suke ta ihun kukan sai an tafi dasu, Anty Alawiyya ce take ta aikin lallashi da ban baki.
Baba da kanshi ya bude min gidan baya, na shiga. Kulsum, Maryam da Hauwa cousin dinmu da tazo jiya daga Gashua, suka shiga cikin motar da nake.
Dayar motar kuma sauran masu zuwa suka shiga. Ana ta daga mana hannu da addu’o’i iri-iri, direba yaja mota muka tafi. Kaina yana cikin mayafin da aka rufa min, hawaye kawai nake sharewa babu kakkautawa cikin tausayawa kaina. Ina ji Maryam ta kira Janan ta sanar da ita tasowarmu kenan, amma ko daga kai ban iya yi ba a lokacin.