A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Har muka isa Zaria idanuna basu daina digar kwalla ba. At some point zan daina kukan da nake yi, sai dai da na tunano yadda rayuwata zata kasance a cikin gidan Yaya Bilal, sai inji wata kwallar tana zubowa babu kakkautawa. Ji nake kamar in cewa direban ya juya damu mu koma gida, zama gaban su Ramata da duk rashin kirkinsu ya fiye min rayuwar dake shirin tunkaroni, sai dai nasan hakan ba zai yiwu ba.

Wajen karfe goma sha biyu muka shiga gidan Yaya Bilal. Motocin suka yi fakin, duk muka firfito. Janan, Anty Sarah da wasu daga cikin yan’uwansu yanmata sa’anninmu, har dasu Harira, suka fito suka tare mu tare da mana jagora har zuwa sashena. Shine na kusa da na bangaren Anty Sarah, duk da haka babu nisa dana Raheemah.

Janan ta tura kofar, na shiga da kafata ta dama kamar yadda suka umarceni, bakina dauke da tarin addu’o’i. Suka ja ni har zuwa bedroom dina, daga nan kuma masu yiwa amarya sannu da zuwa suka fara shigowa. Masu shakiyanci nayi, masu maraba nayi, masu addu’a nayi.

Kayan dakin da aka jera min ba karamin kyau suka yi ba, babu abinda zan ce da Baba da yan’uwanmu sai dai fatan gamawa da duniya lafiya.
Bayan mun gama hutawa, munyi sallah, Janan dasu Harira suka daukemu zuwa tour din gidan. Dakuna hudu ne da babban falo, sai kicin da main toilet, sauran dakunan ma duk suna da nasu bandakunan, inda biyu daga cikin dakunan aka shake su da jeren kayana. Gado, mirror, closet, da dai sauran tarkacen kayan daki. Haka ma falon, ya sha saitin kujeru masu kyau, babbar plasma, dinning table, har da wajen hutawa daga can gefe. Aka shimfida tattausan rug carpet, aka watsa tuntuna da sofa kwara daya jal, sai katoton vase na fulawa.
Kicin kuwa ba’a ma yin magana, duk wasu kaya da ake bukata a cikin kicin an zuba min su, dangin su electronics da sauran kaya na nunawa sa’a. Ban taba tunanin haka gidan aurena zai kasance ba, a yadda Baba yake, nayi tunanin kila gado ma sai an kai ruwa rana zai sai min, dana gayawa Anty Halima haka dariya tayi ta min, wai bani da saiti.

Komi na gida dai yayi Alhamdulillah, sai godiyar Allah kawai. Daga nan kuma suka ja ni zuwa daya dakin na kusa da nawa, shi babu komi a ciki sai tattausan carpet da aka shimfida, katifa, da desktop table da kofofi. Daga gani babu tambaya nan ne dakin maigida Bilal. Nan suka nuna min akwatunan da aka kawo min, Janan tace “Yaya Sa’a ce zai fi a barsu anan kawai, in kin zo kiga kayanki tunda idan ma an kaisu can din hidimar kai da kawowa ce za’a sha”. Na gyada mata kai cikin nuna fahimta.

Akwatuna ne irin na zallar leather dinnan, maroon, dai-daya har guda goma, kowanne shake da kaya. Tun daga na sawa, atamfa ce, laces, materials, yadika masu kyau da armashi, you name it. Kayan kwalliya kuwa kamar za’a bude shago. Harira da suke bude kayan, ta kalleni tana murmushin tsokana, “sai fa kin dage, mijinki mai dan banzan son kwalliya ne, ke kuwa naga alamu kwalliyar ba’a kanki ma take ba, kamar sauran taron matan can nashi daya ajiye dai. Idan kina so kiyi zarra, sai kin koyi amfani da kayan kwalliyar nan”.

Nace mata “to waye yace miki so nake inyi zarra a gidannan?”.
Tace “duh, lokacin da zaki fara shirin yin zarrar waya sani? Kawai ina baki head-ups ne idan lokacin yazo”. Duk suka kwashe da dariya, ni kuma na bisu da harara.

Suka ci gaba da bude akwatunan, dangin jakunkuna, takalma tun daga vincci, gucci, chanels, LV, babu wanda babu. Turaruka, gyale, hijabai, babu abinda babu. Kada ma fannin fashion ear rings da sarkoki su ji labari. Kayan yawansu har yayi yawa, I was very overwhelmed. Yayin da masu ba idanu abinci suke ta zubo addu’o’i, idanuna cike suke taf da kwalla da hawaye, sai fakar idanu nayi na goge su.

Daga nan muka koma dakina, wasu kuma suka tsaya a falo. Aka fara shigo da tarin abinci kala-kala, muka zauna muka ci. Zuwa lokacin da muka gama cin abincin, aka fita da kwanukan abincin, karfe hudu tayi. Lokacin yawancin wadanda suka zo duk sun tafi, ya rage daga ni sai su Janan kawai dasu Maryam da zasu koma Katsina gobe.

Anty Halima ta sanya ni nayi wanka, na sanya riga da zani na atamfa, ruwan goro mai zanen manyan furanni, aka dora min babban gyale a kaina, na saka takalmi flat, muka tafi sashen Raheemah, a cewarsu kai amanar amarya.

Suna zaune a falonta ita da gang dinta, har ma da uwarsu. Taci daurin dankwalinta irin wanda ta saba yi na yan duniya, ‘ya’ya sun zagayeta ana ta hira da shewa babu ko kunya.
Muka yi sallama muka shiga falon. Suka yi tsit, kamar ba su bane masu neman tada falon da hayaniya ba.
Babu wanda yayi mana masauku, suka nemi kujera suka zauna, ni kuma aka zaunar dani a kasan carpet. Kaina yana kasa cikin gyalena, naji su Anty Halima suna gaidasu. Babu wanda ya amsa, sai sautin “hummm” da “uhummmm” daya dinga tashi.

Basu daddara ba dai, Anty Halima tace musu “ga amanar diyarmu mun kawo muku, muna fata za’a rike mana ita cikin aminci da amana”.

Sai da suka shaki iska, sannan naji muryar Adi, “to ku kunji fa, maciya amanan wai sun kawo muku amana”.
Salame ta cafe, “Kaji ma wani rainin wayau fa anan wajen, Momcy. Sai da suka gama shuke-shuken munafurcinsu da kitsa rashin mutunci sannan wai suke kawo amana. Amanar me kuma? Ko roki a maida muku yar ku yadda kuka kawo ta mana, in one piece!”.
Momcyn tasu kuma ta kara da, “ku ne ma kuka zauna wani yi musu karin bayani. Ku bari idanunsu su gane musu mana, kishi da ahalin gidanmu ba karamin aiki bane, kuma duk wanda yace zai ja da gidan iko, to ba jikinshi kadai ba, na uwatai ma da ubanai sai sunji labari!”. Suka kuwa kwashi ihu har da sowa jin abinda tace.

Ganin abin yana wuce gona da iri, Anty Halima tace “to Allah ya baku hakuri, Allah ya gani mun sauke hakkin dake kanmu. Ku tashi mu tafi”.

Sai lokacin Raheemar ta sanya baki, ta tashi tsaye tana wani jijjiga jiki, “hakkin banza dana wofi! Ku har wani hakki kuka sani? Wato dama munafurcin zuwa nan gidan da take yi, tsaface-tsaface take zuwa tana binne mana a gida. Sai da tayi yadda tayi ta tsaface min miji. To wallahi bari kuji, karyarku ta sha karya. Idan kuna cin kasa ku kiyayi ta shuri. An shigo gidan kudi ana ta bude daddaudan baki da ya sha miyar kuka, ana murna an auri mai kudi. To murnar ku zata koma ciki, gwanda ma tun kafin a maida muku diyarku a nakasce, ku dauketa cikin salama ku maidata inda ta fito, idan kuma ba haka ba… tammm!!”.

Anty Halima tace “a’uzubillahi, mai kike fada ne haka? Allah ya tsaremuda aikata wannan danyen aiki. Mu ahalinmu babu masu aikata wannan danyen aiki, bamu taba ba, kuma ba zamu taba ba in Allah ya yarda”.
Nan fa suka yo mana caaa! Da ihu kamar zasu cinyemu danyu. Nan dai muka samu muka bar musu falon, muka barsu suna barazanar sai sun koya mana hankali gabadayanmu.

Muna fita Anty Halima ta kama baki, tace “ikon Allah, Allah sarki mai halitta. Mutane ku sanya kanku cikin uku babu gaira babu dalili? Yanzu banda duniya ta zama abinda ta zama, me zai sako uwa cikin lamarin auren diyanta, har ka ganta ta taka kafa taje gidan surukai tayi dororo?”.

Janan tace “Ai baki ga komi ba Anty Halima, idan har kina tare da mutanen nan, babu abinda zai dinga baki mamaki kuwa”.
Hauwa tace “aikuwa dai Girma ya Fadi wallahi, ba’a ji dadin rayuwa ba. Ai in an girma sai asan an girma, a barwa yara yarinta”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button