A ZATO NA COMPLETE

Idan nace ta bani abinci ta ki, sai in shiga har kuryar dakinta in zubo abina. Idan Baba ya dawo ta fada mishi, inyi kyar da idanu ince hana ni tayi, baya da yadda zai yi dani.
Cikin haka Yaya ya dawo gida. Gabadaya taso ta maida mu yan aiki a tsakiyar gidannan. Kayan fitsari da kashin Aliyu da nata har ma dana Maryam haka zata libgo mana su tace mu wanke, Yaya ne yake zama yayi aikin wankin nan, watarana yana gamawa ma zata ce sai ya sake wai bai yi ba. Idan nace ya daina mata, sai yace wai ai bamu da yadda zamu yi, matsayin mahaifiyarmu take. Sai inyi tsaki in ce Allah ya kiyaye. Kuma fa kada ku ce hakan shi yake hana ta zage mu, ko kadan. Haka kawai zata hau zaginmu, watarana ma haka har sunan Mama zata kira ta kare mata zagi, a gabanmu kuma.
Da naga ya matsa kuma ya ki saurarena, sai na kyale shi yake ta mata aikace-aikacen. Ni dai na ki. Koda ya koma makaranta, idan ma ta kawo kayan wankin sai in tsere abina, watarana ma fakat zan ce ba zan yi ba. Idan an gayawa Baba naki yin aiki, ince yankewa nayi, ko yatsa ta take ciwo, ko kuma wani abu dai. Na dai zame mata karfen kafa kiri-kiri kamar yadda nima ta zame min. Koda wasa ban bari ta juya ni ba.
Wannan yana daya daga cikin manyan dalilan da yasa kullum nayi sallah sai na daga hannuna sama na roki Allah Ya kareni daga sharrin kishiya. Allah ya kiyaye ni da haduwa da ita a gidan aure.
A cikin haka aka wa Baba kari da kuma canjin wajen aiki. Dama lokaci zuwa lokaci ana mishi canjin wajen ayyuka, amma kuma ba mai nisa bane. Wannan karon Katsina aka kaishi. Saboda haka muka fara shirin kaura zuwa Katsina. Yaya yana ajinshi na karshe lokacin a sakandire, don haka aka barshi a can. Ni kuwa da nake aji daya, aka min canjin makaranta zuwa Ulul-Albab.
Babu yadda banyi ba akan a barni a gaban su Bako, fir Baba ya ki. Ranar da za’a tafi din kam da kuka muka rabu. Da kyar aka tura ni cikin motar da Baba yayi shata ta kwashe mu zuwa Katsina.
Mun dauki lokuta kafin mu saba da yanayin sabon garin da muka je. Musamman gari inda babu dangin Uwa balle na Uba kuma ko abokai, yana da wahalar sabo, amma a hakan dai muka zauna muka fara sabawa dasu din. Anan kusa da inda muka koma, wata Ummu-Kulsum, itama kimanin shekaru na ce, mun fara sabawa da ita da mutanen gidansu nake jin labarin itama a Ulul-Albab din take, nan na makale mata sosai. Nan da nan abota ta kullu a tsakaninmu. Ya zamana na gwammace in yini cur a gidansu maimakon inyi gidanmu, saboda idan ma na zauna a gidan me zanyi? Habaici ne nake sha da bakar magana, sai kace ni ce kishiyar ta ba diyar kishiyarta ba.
Da na samu ma baba ya sai min form din islamiyar da Kulsum take zuwa shikenan, sai muka kara gamewa da ita.
Suna kare hutunsu na bita muka tafi. Duk da ba wasu kayan azo a gani aka hada min ba, naji dadin dan abinda yayi din, ban raina ba. Allah Ya taimakeni term daya kadai nayi missing, dana maida hankalina kan karatuna sosai, tuni na wuce aji biyu.
Mun koma gida hutu, na tarda amarya Alawiyya a gida. Abin ya bani mamaki, ko kadan ban ji labarin auren ba, wanda a yadda ake fada min, kusan watanta uku kenan a gidan.
Kodayake, daga bakin wa ma zan ji labarin? Tunda aka kaini aka ajiye a makarantar, ban kara ganin kowa ba. Ni da visiting dama sai in su Inna – mahaifiyar Kulsum sun je, sannan nake ganin na gida. Ni da Baba dama sai dai in ina bukatar wani abu, in ari wayar wani malami in kira shi in fada mishi. A hakan ma sai ya dauki lokacin shi kafin ya turo abinda zai turo din, kudi ne ko kuma abin bukata. Watarana kuma sai dai ya ba su Inna su kawo min kam.
Na sha shigewa bandaki in shaki kukana, ko kuma in haye can kan gadona in yi kukan. Abin yana da matukar cin rai da ban takaici, na rasa dalilin da yasa ni hakan take faruwa dani. A kaika makarantar kwana na wata da watanni amma ka rasa naka wanda zai leko ka ko da wasa? Rashin uwa ne ya janyo haka ko kuma rashin dangi? Saboda na tabbata cewa da a gaban su Bako nake, da lallai sai na ma gaji da ganin dangina. A hakan nake ta cijewa ina danne komi a cikin raina, har muka koma gida hutu.
Amarya ko in ce bazawara Alawiyya ta shiga da rawar kai da jiji da kai, sai dai bai je ko’ina ba ya sauka. Saboda Ramata ba kanwar lasa bace ba. Zama a gabansu sai ya zama kamar zama da wasu kishiyoyi ne, suka sako ni a gaba. Ni abin yana bani mamaki, ban tsarewa kowa komi ba, amma ni kuma ace na tsare? Shima din taso taga tayi dani, taga dai daga ita har Ramata din na jefa su a kwandon shara, sai ta saddakar, ta koma kan Ramata din.
Matsala ta farko a cikin wannan gida, ita ce rashin adalci. It was obvious Baba yafi son Ramata akan Alawiyya, zata iya yiwuwa so ne na tsakani da Allah, ko kuma wanda ta nemo a wajen malamai da yan tsibbu, koma dai wannene, amma kuma bai san ta yadda zai daidaita ko ya boye son nata ba domin samun adalci a cikin iyalansa, hakan yasa a kowane abu ne sai ya fifitata akan Alawiyya da ‘ya’yansu. Ita da ‘ya’yanta sun fi kowa kima da mutunci a idanun Baba.
A hakan ma kuma bata bar Alawiyya din ta zauna ba, ta hana ta zama lafiya da mijinta, ta hana ta sana’a. Kudi duk yawansu idan ta tarki sana’a dasu, zasu kare ne kafin a je ko’ina. Wani abu ne da naji suna kira wai ‘mai rariya’, duk yawan kudin da zasu shiga hannun mutum to zasu koma kamar an cinna musu wuta, nan da nan zasu kare ka rasa ta inda suka shiga. Abubuwa ne da ni na sha gani da idanuna. Wani lokaci na tashi cikin dare zan yi sallah inji ana kurumtu ko a bayan dakin Baba ko na Alawiyya, watarana shara zan shiga yi a dakin Baba in ga kulli-kulli na magani ko dami na layu da dai tarkace a lungu da sako na dakin, sai dai in daukesu in shiga wajen su Inna in kona su.
Bazamar da Alawiyya tayi wajen malaman Allah da Annabi domin neman kariya da kuma karyewar abubuwan dake kanta, itama ta fada cikin taskun bin malamai da yan tsibbun har ma da yan bori. Wannan masifa dana gani da idanu na, ta tsorata ni fiye da tunani na.
Duk sallar duniya idan nayi, sai na roki Allah ya raba ni da zama da kishiya. Ya zamana tunanin zama da kishiya kadai kan sa inji kamar zuciyata zata rabe biyu. A zamanin budurcina, saurayi yana zuwa daya, tambaya daya ce: kana da ra’ayin zama da mata biyu nan gaba? Idan yace eh, to sai in ce Allah ya kiyaye hanya tun ma kafin tafiya tayi nisa. To da yake ma ba kula samarin nake yi ba, saboda a lokacin hankalina yana kan in gama sakandire da sakamako mai kyau, in samu in shiga jami’a.
Allah Ya taimakeni sosai, gabadaya jarabobina na waec da neco suka yi matukar kyawu, sai dai kasancewar banyi jamb ba, -a cewar Baba in bari sai sakamakon jarabawar ya fita sannan-, yasa da Baban su Kulsum ya tashi sai mata form din makarantar SBRS, kasancewar ita bata ci jamb ba, yasa na roke shi akan ya nusar da Baba nima ya sai min. Allah Ya taimaka ya siya min, muka samu admission muka tafi.
*☆⋆03⋆☆*
A SBRS muka hadu da Janan. Haduwa irin ta wajen registration, daga tambayar zuwa wajen signing, sai kuma muka ji cewa ai duk dakinmu daya, nan muka hade. Ita Janan wanda yake auren Yayarta shine ya mata hanyar zuwa can, a lokacin shine DG din makarantar ma. Amma da yake irin mutane ko in ce iyayen nan ne na da, bai barta ta zauna a gida ta huta ba, da kanta tayi komi na registration.
Kasancewarmu a daki daya yasa zumuntarmu gaba daya tayi karfi. Yayarta, Anty Sa’a anan cikin makarantar suke zaune ita da maigidanta da ‘ya’yansu, duk da cewa suna da gida a Zaria, amma bata taba zuwa can ta kwana ba, wani abu da Anty Sa’a din da maigidanta suka ce wai zai sa ta dinga slacking akan karatunta.
Abotarmu tasa muka saba da danginsu sosai, har ma watarana Yayansu Bilal yazo ya daukar mana excuse, ya daukemu zuwa can gida Kaduna lokacin da aka yi bikinshi da Anty Ameerah. Yan’uwansu mutane ne masu mutunci kwarai, karimci da kyautatawa, jininmu ya hadu dasu sosai. Wannan shine ganina da Yaya Bilal na farko.