A ZATO NA COMPLETE

Har Janan ta gama wayarta, ban yi motsin kirki ba. Ina ji ta dawo gefena ta kwanta a inda take da, tana kiran sunana, nayi shiru kamar mai barci ban tanka mata ba.
Sai da aka kira sallah sannan muka tashi, lokacin Mimah ta koma sashen su. Muka yi sallah, na zauna akan abin sallar ina karanta suratul-Yasin, ita kuma Janan tana lazumi har aka kira sallar isha’i muka yi.
Naci gaba da zama akan abin sallar bayan na gama, har Janan ta kammala tata ta fita, bata jima ba ta dawo da kulolin abinci ta zuba mana. Duk da kamshin da abincin yake fitarwa, da dadin da yayi, kasa wani ci nayi da yawa, sai tsakura na dinga yi. Har sai da Janan ta kai ga tambayata lafiya? Nace mata bana jin dadin jikina ne.
A haka muka gama, ta wanke kayan ta fita dasu zuwa kicin.
Sai data dan jima, har sai dana tashi daga kan abin sallar na koma gefen gado na zauna, sai gata ta shigo. Ina so in bude baki in tambayeta ko Yaya yaci abincin shima? Amma na rasa ta yanda zan fara dauko maganar. Don haka nayi shiru, na bita da kallo har ta zo itama ta zauna a gefen gadon.
Tace “Yaya yace ki same shi a dakin Anty Raheemah yanzu”.
Nace “ban gane ba? Ya shigo gidan ne?”.
Ta girgiza kai, “a’ah, ya dai kira ni ne a waya”.
Da wani haushi yazo ya tokare ni a wuya, duk yadda naso in danne kamar yadda na dinga yi cikin satin idan ya kirata instead of ni, ya bata wani sako kasawa nayi.
Nace, “wai ni meye amfanin wayata ne da ba zai dinga kirana ba sai dai ya wani bada sako a bani? Ko ban kai wannan matsayin bane kuma yanzu?”.
Janan ta daga kafada, “to Hajiya, ni kuma ina zan sani? Shi ainihin maigidan naki zaki je ki tambaya, ni dai yar sako ce, na kuma kawo. Yana can kuma yana jiranki, kin kuwa san shi baya son jira don haka ki kwashi jikinki da kafafunki ki tafi tun kafin ya shaka”.
Na mike tsaye ina guna-guni, “haka kawai sai a dinga wa mutane wani gani-gani da iko-iko? Ace kai da mijin aurenka wai sai an dinga wani kai da kawowa ana ajiye sakonni kamar a zamanin da?”. Na ja tsaki.
Janan data kwanta dai-daya akan gadona, ta kyalkyale da dariya, “ku dai kuka sani!”. Na wurga mata harara.
Na bude wardrobe na ciro hijabi doguwa, na saka.
Janan ta kalleni, “wai sai kace wadda zata je wani bikin gidan malamai, ba wajen mijinki zaki je ba da zaki wani kama hijabi ki zurma a jiki?”.
Na kara jefa mata harara, “to wai ke ina ruwanki ne?”.
Ta sake sakin dariya tare da sake mike kafa har da min gwalo. Na girgiza kai kawai ina dan murmushi. Na fita zuwa inda aka kirani.
Na tura kofar falon nata na shiga bakina dauke da sallama. Na kula da takalmin da na fi kyautata zaton na Yaya ne a ajiye a waje, da kuma wani hadadden bakin takalmi mai tudun duduniya daga ganinshi na mata ne. Ban kawo komi a cikin raina ba, na cire nawa takalmin nima na shiga cikin falon bakina dauke da sallama.
Sai dai ina shiga na danyi turus, ganin mutane a cikin falon. Mutanen da suka kasance uku, Yaya Bilal da matanshi.
Muryarshi kadai naji wadda ta amsa min sallamar, itama a hankali don da ba don shirun da falon yayi ba babu abinda zan iya ji.
A hankali na taka har zuwa tsakiyar falon, ina jin idanunsu a kaina suka biyo ni da kallo. Sai da naje tsakiyar falon, naja tunga na tsaya ina raba idanu a tsakanin kujerun falon da kuma matan nashi dashi kanshi, cikin tunanin inda zan zauna.
Shi zaune yake akan kujera mai daukar mutum biyu, Anty Ameerah kuwa na gefenshi kugu da kugu kamar zata haye kan cinyarshi, tazarar data bari a gefensu, idan aka samu mutum mara kiba tsaf zai yi fitting a wajen. Taci kwalliya kamar wadda zata je wajen biki, dama gata tubarkallah, kyakkyawa ce, kuma fara mai kyawun jiki, kayan data saka ma sun matukar karbarta. Ga mai karamar zuciya, tuni zata juya baya hannunta aka tana ihu, kallonta kadai a hakan nan kan iya tsoratar da mutum.
Ita kuma Raheemah ta zauna a daya kujerar dake gefenshi, itama dai tasha tata kwalliyar. English wears da suka matukar fitar mata da surar jiki. Kitson da aka mata da yasha karin gashin kanti, ya sauka har gadon bayanta da kuma saman kirjinta inda yayi matukar kokari wajen rufe shafaffen kirjinta da ko brazier acuci maza bata iya tado shi, tana ta wani kwarkwasa.
Idan har zan zauna kusa dashi, hakan yana nufin sai dai in zauna akan kujerar da Raheemah take, ko kuma in zauna a daya kujerar da take fuskantarsu, wanda idan nayi hakan ba zan samu damar jin abinda zai dinga fada ba sosai tunda sauran kujerun sunyi nisa da nan center table ya shiga tsakani. Sai dai kuma idan a kasa zan zauna.
Ina shirin neman wuri a kasar in zauna, naji muryar Yaya yana cewa “zo ki zauna anan”.
Na daga kai na kalli inda yake, sai naga ashe ya tashi daga inda yake a zaune, yanzu yana tsaye ne. Na kalli inda yayi min nuni, kusa da Anty Ameerah da uncertainty, kafin na murje nayi ta maza naje na zauna. Sarai na kula da yadda ta matsa daga tsakiyar kujerar ta koma can karshe ta lafe, amma hakan bai dameni ba.
Yaya ya dauko kujerar dinning table guda daya, ya ajiye a tsakiyar falon yadda yake fuskantar mu gabadayanmu, ya zauna.
Da dai kamar inyi shiru yadda su ma suka yi, wani fanni na zuciyata dai ya tunatar dani ba haka aka yi min nasiha ba da zan taho daga gida, don haka na daga bakina da kyar na gaida su, idan sun amsa min, to ban ji ba har ga Allah.
Yaya yayi gyaran murya, tare da bude taron da salatin annabi. Ya janyo wasu ayoyi daga cikin Al-Kur’ani mai girma ya fassara, ya kawo hadisai, yayi sharhi, ya kare da nasihohi. Duk akan zaman aminci da zaman lafiya a tsakaninmu. Kaina a kasa, cikinmu babu wanda yayi motsi a cikinmu har ya gama.
Bayan dogon lokaci daya dauka yana bayanai, ya gabatar dani a matsayin matarshi. Sai lokacin daya ce ni din kamar yar uwa ce a garesu sannan naji Raheemah tace “tabdijam!”, a can kasar zuciyarta. Ameerah kuma ta sake gyara zamanta. Duk yayi kamar bai ga ko ji abinda suka yi ba, yaci gaba da bayanan shi. Ya gama da cewa “kun fahimta?”. Duk muka amsa da ehh.
Yace “good. Sannan maganar zama da zancen girki, ina so gabadayanku ku shirya, ranar wannan Ladin da zata zo zamu koma Abuja gabadayanmu. Komi an riga an tanada a can, saboda haka baku da bukatar daukar wani abu sai yan abubuwan da ba’a rasa ba. Any complain?”.
Na daga baki cikin mamaki na kalleshi, Ameerah ma haka take kallonshi kamar wanda yace lahira zai kaita, ita kuwa Raheemah ta dan saki ihun murna cike da farinciki wanda bana tunanin tasan cewa tayi hakan.
Duk cikinmu babu wanda ya iya yin magana, sai Ameerah ce ta iya daga baki bayan lokaci mai tsayin tace, “amma ni fa Daddy bai san da wannan maganar ba, ka fada mishi ne?”.
Ya kalleta kamar wata sabuwar mahaukaciya, yace “ni da Matata kuma, don zan zartar da hukunci a kanta sai na tambayi mahaifinta? Wai ma, me kike yi ne a Zaria? Ke ba aiki ba, ke ba karatu ba. Kada ki manta wancan karon da na miki maganar, karatunki kika kawo as an excuse, na kuma kyaleku har kika gama, amma baki sake tada min zancen ba. Na kuma kawo idanu na zuba miki, amma saboda baku san annabi ya faku ba, ko a jikinki. Shikenan ni kullum ina yawo da jele akan titi kamar wani mara galihu, an fada miki a kanki zan kare ne? To bari kiji, wannan itace magana ta karshe da zamu yi akan komawa Abuja, idan muka tafi wannan karon, babu abinda zai dawo dani Zaria sai dai idan wata hidima ta taso a cikin dangi don haka ki yanke shawararki”.