A ZATO NA COMPLETE

Tayi shiru kanta a kasa, da alama bata ji dadin abubuwan daya fada mata a gabanmu ba, murya can kasa kamar wadda aka shake, tace “idan na tambayi daddy, zan fada maka duk yadda muka yi”.
Ya tabe baki, da alamu abin bai dameshi ba, ko kuwa tsananin sabo ne? Yace “wannan kuma ku kuka sani, illa iyaka ina son ki san cewa idan na sanya kafa na tafi, kuma ba’a baki izinin biyo mu ba, kada ki saka ran zaki dinga ganina a Zaria kamar yadda kika saba don na gaji da wannan jigilar. Akwai wani me abin cewa ne kuma?”.
Duk muka yi shiru, yace “idan mutum yana da matsala gwara ya fito tun da wuri ya fadi, bana son abinda sai daga baya za azo ana damuna da wasu kananun maganganu”.
Ina so in tambaye shi maganar internship dina, tsoron abinda zai fita daga bakinshi ya hana ni daga baki. Idan ya yiwa ta gaban goshinshi fada irin haka, ina ga ni kuma da dama yake shake dani a wuya? Nasan kiris yake jira ya min wankin babban bargo. Don haka na ja bakina nayi shiru.
Raheemah ta daga baki itama cike da tsoron yin maganar, amma hakan bai hanata cewa, “uhmm.. har su Salama zamu tafi ne?”.
Ba Yaya Bilal kadai ba, ni kaina sai dana kalleta baki a dage, meye hadin biri da gada kuma?
Yayan yace “a kan me kuma?”. Tayi shiru tana muzurai.
Ya sake cewa “ba karatu suke yi ba wai? Meye na wani biyoki gidan aurenki? Ko kuwa tare aka daura muku auren ne?”.
Sai ta kama in-ina, “dama.. wannan.. Adi nake nufi”.
Ya kalleta sosai, “to wai ita Adin an miki wahayi da ita ne? Ko kuwa dole sai da ita zaki yi zaman aure ne? Wai bata da gidan iyayenta ne ita din? Ke kadai aka daura min aure da ita, ke kadai kuma nake bukatar gani a gidana. Don haka ke kadai zaki shirya ki bimu. Su Salama su koma gida mana? Dama can dalilin makaranta yasa suke zama anan, kuma ba zuwa suke yi ba, ita kuma Adin ta koma gidansu haka nan itama”.
Sai tayi kus, tana gunguni can kasan makoshinta.
Yace “shikenan babu wani mai magana a cikinku kuma?”.
Jin munyi shiru yasa ya gyada kai, ya rufe mana taro da addu’a.
Ya mike tsaye yana kallonmu mu duka, yana cewa, “don haka sai ku fara shiri. Ki tashi ki koma sashen ki, ke kuma zo in maida ki gidanki”.
Ya fara tafiya, Ameerah ta tashi ta take mishi baya. Nima tashi nayi sadaf-sadaf na bi bayansu, muka bar Raheemah har yanzu a zaune a inda take babu alamun zata motsa.
Muna fita suka wuce wajen gareji, ni kuma na nufi sashena.
Janan bata nan lokacin dana koma dakin. Har na shiga bandaki na watsa ruwa, na fito na shirya cikin kayan barci, ban ji motsinta ba.
Na dauki waya na kirata tare da tambayar inda take, tace “makwanci mana”.
Nace “ban gane ba, nayi zaton tare zamu kwana dake?”.
Tace “rufa min asiri mana, in koma wajen Ummah na a yadda nake. Kinga, yanzu naji dawowar angonki, ki dauki jikinki ki tafi kije ki taro shi sai da safe”.
Ta kashe wayar ba tare data bari nace wani abu. Na bi wayar da kallo, kafin na ajiyeta a gefen gado.
Shiru ina zaune ni kadai, ban ma san zaman me nake yi ba, daga karshe dai na fita na kaso wutar falo da kayan kallo, na koma na lalubi gefen gado na kwanta tare da kashe wutar dakin. Addu’ar kwanciya barci nayi na shafa a jikina, na lumshe idanuna.
F.W.A
*☆⋆36⋆☆*
Ina rufe idanuna, naji an turo kofar dakin an sake kunna wutar dana kashe yanzu. Na bude idanuna da suka fara yin nauyi saboda gajiya da barci, na saukesu a bakin kofa.
Yaya Bilal yayi tsaye a bakin kofar hannunshi harde a kirji, da alama har ya dawo daga maida Anty Ameerah din. Kayan jikinshi ne na dazu har yanzu bai cire su ba, casual outpit ne, shigar da ban saba gani a jikinshi ba. Yawanci daga suits sai manyan kaya, riga da wando na shadda, watarana ma ko hula baya dorawa.
Muka tsaya muna kallon-kallo ni dashi, kafin ya maida kofar dakin ya rufe. Kai tsaye bandakina ya wuce, ina nan a kwance a inda ya barni, ina jin motsin ruwa dai. Ba’a jima ba, ya fito daga bandakin yana gyara links din hannun rigar shi. Na bi shi da kallo.
Sai daya kawo tsakiyar dakin sannan ya kalleni, “kin yi sallar isha’i?”.
Wani kwarjinin shi ya cika min idanu, na kasa daga idanuna gabadaya in kalli tsakiyar nashi idanun. Kai na gyada mishi a hankali.
Ya sake cewa “kina da alwala har yanzu?”.
Na sake girgiza mishi kai, alamun a’ah.
Ya tsaya yana kallona ba tare da yace komi ba, kusan tsayin minti daya, har sai dana kai ga dan dago kaina na kalleshi. Wani irin abu a tattare dashi dana kasa fahimtar koma menene, bugun zuciyata naji ya dauka da sauri da kuma karfi.
A hankali ya juya zuwa wajen da muke yin sallah, da alama dama an tanadi wurin ne saboda sallah.
Yace “ki tashi kiyo alwalar ko? Muyi sallah”.
Ni wannan sabon attitude daya kirkiro na kasa fahimtar shi, kodayake ai dama can ba wani sanin shi nayi ba sosai, zata iya yiwuwa halin shi kenan. Na daga kafada tare da saukowa daga kan gadon. Kayan barcin dana saka a jikina dogon wando ne da riga karama top, wadda bata kama jikina ba. Na shiga bandakin na daura alwala kamar yadda ya umarceni.
Lokacin dana fito daga bandakin, har ya shimfida abin sallah. Na bude wardrobe na ciro doguwar hijabi na saka. Na karasa wajen da yake.
Ya tada sallah, na bi bayanshi. Raka’ah hudu muka yi dogaye, muka dora da shafa’i da wutiri.
Bayan mun gama, ya juyo ya dafa kaina, yayi addu’o’in da annabi S.A.W ya umarcemu da mu yi a lokacin da muka yi sabon aure. Neman alkhairan juna, da kuma neman tsari daga sharrin juna.
Bayan nan juyawa yayi, yaci gaba da janyo wasu addu’o’in, ni kuma na zauna muk’u a bayanshi, ban ma san kalar addu’ar da nake yi a cikin raina ba har ya gama. Ya tashi tsaye tare da linke abin sallar, nima na mike na nade wanda nayi amfani dashi na ajiye a inda muke ajiyewa.
Nayi tsaye anan kaina a kasa, ban san abinda yakamata inyi ba daga nan, it felt very awkward. Subhanallah! Haka kowace mace take ji idan aka barta da mijinta su kadai a dakinta, ko kuwa ni kadai ce nake jin haka?.
Shi kuwa gogan da alama ko a jikinshi, kamar baya jin komi, idan ma yana ji ba karamin kokari yayi ba wajen murje shi.
Yace “kin ci abinci? Kina jin yunwa?”.
Ai ko ina jin yunwa bana tunanin wani abu zai iya shiga cikin cikina bayan numfashi, yadda nake jin shi dinnan yayi knotting da nerves, fargaba da rashin sanin abin yi. Na sake girgiza mishi kai. Ina tunanin dai na zama kurma yanzu, ko kuwa?.
Bai sake cewa komi ba, ya juya ya bar dakin. Na sauke numfashin da ban san na rike ba. Na jima a tsaye sosai, kafin na cire hijabin jikina na linke na maida inda take, na sake komawa na kwanta. Sai dai wannan karon ban kashe wutar dakin ba tunda bani da tabbacin zai dawo ko ba zai dawo ba.
Zuwa can, sai gashi ya sake dawowa. Wannan karon ya canza kayan jikinshi zuwa jallabiya fara kal, hannunshi kuma dauke da leda babba. Ya ajiye a tsakiyar dakin ya sake fita, can ya dawo da plates da kofuna guda biyu, ya janyo karamin carpet dake jingine acan gefe ya shimfida ya zauna.
Ya fara fitar da kayan ciki, tatacciyar madarar hollandia da gasasshiyar k’afaffiyar kaza. Kamshinta ya hade dakin gabadaya, cikina ya fara juyawa saboda yunwa, amma na kasa motsawa. Ina kallo yayi amfani da wuka karama ya yanka kazar ya zuba a cikin plate, ya kuma tsiyaya madarar a cikin kofunan biyu.