A ZATO NA COMPLETE

Sai daya gama, ya dago kanshi ya kalleni. Nayi sauri na kauda kaina daga kallonshi da nake yi.
Yace “ba zaki ci bane?”.
Nayi shiru ina kallonshi kamar ba zan ce komi ba. Bai sake ce min uffan ba, yayi bismillah ya fara cin abin shi.
Da naga uwar bari, sai na silalo daga kan gadon a hankali kamar wadda kwai ya fashewa a jiki, na lallaba na zauna a gefenshi.
Ina kallon murmushin daya saki a hankali, na turo baki gaba. Ya turo min plate din kusa dani da kofi daya. Kaina a kasa na fara ci bayan nayi bismillah.
Shirun da duk muka yi ni dashi, babu mai motsin kirki a cikinmu shi ya cika min ciki, sai kuwa taraddadi daya kara cika min ciki.
Na kara tsiyayar madarar dake ajiye a gefenmu bayan na shanye wadda ya zuba mana. Ina kallonshi yana cin namanshi hankalinshi kwance, har ya gama. Lokacin nima na shanye madarar dana tsiyaya.
Ya zari tissue ya goge hannunshi, tare da kokarin fara hada kan kayan. Da sauri na riga shi fara daukar kayan, nace “uhm, ka bari zan hada”.
Bai ce komi ba, ya dai sakar min kayan, ya tashi ya nufi hanyar bathroom dina. Na bishi da kallo cikin sanyin jiki, haka kawai naji ina tausayawa kaina. Haka tawa rayuwar auren zata kasance kenan?.
Na dauki kayan dai gabadaya na fita zuwa kicin dasu. Na wanke plates da kofunan, sauran kazar da bamu kai ga cinyewa ba, na nade a foil paper na saka cikin fridge. Sannan na koma dakin.
Wayyo faduwar gaba! Zuciyata tayi wani irin bugawa lokacin dana ganshi kwance dai-daya akan gadona, ya dago daga kan wayarshi ya kalleni da alama cikin mamaki ganin yadda naja tunga na tsaya kyam, kamar wata wadda taga wani abin tsoro. Sai dai bai ce komi ba. Ni wannan silent treatment da yake bani ya fara bani tsoro kuma maimakon haushi.
A hankali ya kauda kanshi ya maida kan wayarshi kamar ma bai ganni ba. Ni kuwa naci gaba da kafewa a tsaye a wajen. A kalla nafi minti goma a wajen har sai da naji kafafuna sun kage. Har ya gama latsa wayarshi, ya kashe hasken tare da ajiye wayar a kan bedside drawer.
Ya kalleni yace “idan kin gama, ki kashe wutar dakin”. Daga haka ya juya min baya.
Na kara wasu mintunan a tsaye ina kallon bayanshi, kafin daga karshe na yanke shawarar wannan tsayuwar da nake yi anan babu abinda zata kare ni dashi, ga barci da gajiya da suka dabaibaye ni. Idan kuma ba so nake yi inyi barci a tsaye ba, ina bukatar wajen da zan kwantar da hakarkarina.
Na lallaba na kashe wutar dakin, a hankali, cikin sanda na taka zuwa kan gadon kamar mai tsoron a kamata, na kwanta a gefen gadon nima na juya mishi baya. Na sake yin addu’ar kwanciya barci tare da lumshe idanuna. Sai dai wannan karon babu alamun yin barci a cikin idanuna, zuciyata cike take da tsoron abinda zai je ya dawo. Ban san lokacin da barci ya kwashe ni ba. Cikin dare na farka na jini kwance luf akan kirjin Yaya, ban san ko ni ce na gangara wajen da yake ba ko kuma shine ya gangaro inda nake ba, ban kuma damu da in janye jikina ba. Sai ma kara lafewa da nayi, saboda a lokacin ji nayi kamar duk duniya babu abinda ya kai kirjin Yaya Bilal dadin kwanciya sai dumi.
Lokacin dana tashi, ni kadai ce kwance a tsakiyar gadon. Sai kuwa tarin fululluka a gefena da ban san yadda aka yi suka zo wajen ba.
Dan hasken da dakin yayi da kuma motsi da naji a bandaki ya tabbatar min da cewa Yaya yana can. Na juya na kalli agogo, karfe biyar babu mintuna goma, asubahi ta riga tayi kenan. Daidai lokacin da naji karan bude kofar bandaki ana fitowa, nayi sauri na koma na kwanta kamar mai barci.
Ina kallon Yaya yazo ya tsaya a gefen inda nake yana kallona ta idanuna dana dan lumshe.
Ya jima a tsaye yana kallona, har dai naji kallon ya isa haka nan, na danyi motsi. Da sauri naga ya ja da baya, na bude idanuna a hankali na sauke su a kanshi.
Ya wani yi kici-kicin da fuska har yaso ya bani dariya, kamar ba shine ya gama kare min kallo ba yanzun nan.
Yace “lokacin sallah yayi”. Na gyada mishi kai tare da tashi zaune, shi kuma ya juya ya fita daga dakin.
Bayan ya maida kofar ya rufe, na sauka daga kan gadon ina yin mika, strangely feeling good and relaxed. Kamar wadda ta samu dadadden barcin data jima bata yi ba. Na shiga bandaki na dauro alwala na fito na tayar da sallah.
Ina nan a zaune har gari ya gama yin haske, Yaya Bilal bai dawo dakin ba. Wani barcin na sake komawa. Sai karfe tara na safe na tashi.
Wanka na fara yi, cikin kayana na fiddo wasu riga da wando na Pakistan na sanya. Na bade jikina tun daga kafa har kaina da turare. Show glass babba guda aka cika min da kayan kamshi iri-iri yan asali irin na mutanen Bare-bari, dama su ba baya ba. Kamshi mai dadi da sanyayar da zuciya. Na dauki gyalen na nada a kaina, na fita falo. Lokacin karfe goma na safe. Babu kowa a falon, kamar yadda naji babu hayaniya a cikin gidan.
Tunda na tashi cikina yake kiran yunwa, na duba kicin da dinning table ko Janan ta shigo da abinci lokacin da nake yin barci, naga wayam. Ina shirin juyawa in koma daki in dauko wayata in kirata, kofar dakin Yaya ta bude.
Ya fito, da alama shima wankan yayi. Ya sanya wandon jeans navy blue da farar rigar top wadda ta dan kama kirjinshi. Sai bada kamshi yake yi. Ya zauna akan kujera yana lalubar remote ya kunna talabijin.
Na duka har kasa na gaida shi, ya amsa yana wani fuskewa. Na girgiza kai a hankali, wannan basarwa ta Yaya Bilal na kasa gane kanta balle dalilinta.
Yace “miko min abinci”.
Nayi shiru ina muzurai, ya kalleni cikin mamaki. “Abinci nace!”.
Yadda yayi maganar cikin rashin alamun wasa, yasa naji jikina ya dauki rawa cike da tsoro, nace “ai.. uhm… Da naga ana kawowa kwana biyu sai banyi ba”.
Ya dago ya kalleni sosai, “to ita wadda take yi girkin, tare aka kawo ku da ita ne ko kuma zata kare ne wajen girka miki abinci? Banda ma rashin tunani, a kawo ki gidan aurenki, ki zauna kina jiran wata ta dafa abinci ta kawo miki? Lalaci kenan ko kuma duk cikin rashin so ne!?”.
Na daga kai da sauri, kuma cikin kaduwa na kalleshi. Shima kallona yake yi, fuskarshi babu alamun nadamar abinda ya fada. Sai a lokacin na fahimci dalilin hade fuskar da yake tayi. Naji wata kwalla ta cika min idanu, a hankali nayi kasa da nawa kan.
Na daga baki da kyar, nace “kayi hakuri… Bari in dafa maka yanzu”. Na tashi cikin sanyin jiki, na shiga kicin.
Tsayawa nayi a tsakiyar kicin din ina share hawayen da suka fara zarya a fuskata, wace irin rayuwar aure ce haka muke yi ni da mijin aurena?. Sai dana dan nutsu, sannan na fara dube-dube ina neman abinda yakamata in dafa mishi mai sauki.
Da yake kicin din shake yake da kayan abinci kala-kala, sai na shiga store na dauko ledar cous-cous. Na bude fridge da yake shake da vegetables da abubuwan gwangwani, na ciro abubuwan da nake bukata. Fridges din guda biyu ne, daya na kayan miya, nama da sauransu, dayan kuma na ruwa da soft drinks.
Cikin sauri nayi vegetable sauce, na dafa cous-cous din, tare da hadawa da ruwan shayi.
Na zuba mishi komi, na dora akan tray na fita na kai mishi. Yana nan zaune a inda yake, na hada komi a gabanshi, na koma gefe na zauna.
Kasa ya sauko, ya dauki cokali zai fara ci, sai ya dakata ya kalli inda nake.
Yace “ba zaki ci ba ne ke?”.
A hankali na girgiza mishi kai.
Yace “me kika ci?”.
Ban ce komi ba, na sake girgiza mishi kai.