A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Yace “wai kin koyi rashin magana ne yanzu ko kuma rowar muryarki kika fara ne? Kodayake, har da laifina ma. Saboda ba’a sayi bakin ki bane ba ko?”.
Nayi saurin girgiza mishi kaina ina dan murmushi, ya sake girgiza kanshi, “uh uh?!”.
Nace “a’ah, ba haka bane”.

Sai lokacin ya sakeni, yace “to ko ke fa? Ki dinga hana ni jin muryarki, baki san muryarki tana da dadin saurare bane?”.
Ni na rasa ta ina Yaya Bilal ya zama frank and blunt ba, ko kuwa dama can haka yake?. Ina shirin bashi amsa wayata dake gefena ta shiga yin kara, kafin in kai hannu in dauka, Yaya ya riga ni. Ya kalli sunan mai kira, ya kalleni girar sama data kasa a hade.

“Waye kuma wani Hamza cm?”, ya tambaya cikin hade fuska.
Nace “classmate dina ne”, tunda aka daura min aure nake samun kiran waya daga yan ajinmu da muka gama makaranta dasu suna taya ni murnar yin aure.
Bai ce komi ba ya kashe karan wayar, ya saka ta cikin aljihun rigar shi. Yace “bari in fita”.

Na mike na mishi rakiya har bakin kofa, nace “Allah ya tsare, a dawo lafiya”.

Yace “ameen baby na, sai na dawo”.
Ya wuce, ni kuma na maida kofar na rufe ina murmushi kamar wata kuntacciya. Damn, why does it feel so good to be his baby again?!.

Bayan ya tafi, gidan na rufe na tafi sashen Anty Sarah. Janan da Mimah na falo suna karin safe lokacin dana shiga, Anty Sarah kuma da alama tana daki.
Muka gaisa dasu, Janan ta min tayin abinci nace na koshi, na nemi waje na zauna ina kallo har suka gama. Nan Janan ta dawo wajena muna hira da ita, har Anty Sarah ta fito daga dakin Yaya Jameel, Yaya Jameel din yana bayanta hannunshi dauke da Rabi’ah.

Muka gaida su, suka amsa, Yaya Jameel din yana ta tsokanata har dai ya fita. Anty Sarah ta zauna muka cigaba da hirarmu.
Sai da azahar sannan muka koma bangarena ni da Janan. Bayan na dafa mana abinci mai sauki, muka ci. Janan ta tafi karbo min dinkin data kai mana, ni kuma naci gaba da zama anan har ta dawo.

Dinkunan sunyi kyau matuka, tace “sauran sai dai ko zuwa ranar juma’ah ne ko asabar aje a amso miki, na yiwa Is’hak magana zai je ya amso miki”.

Na gyada mata kai cikin daukewar hankali lokacin dana daga wata riga, na hangame baki da hanci cikin mamaki, nace “meye haka nake gani wannan Jan? Wannan show me din ai yayi yawa”.

Tace “ke ja can! Wani irin yawa kuma? Ba mijinki zaki yiwa kwalliya dasu ba?”.

Ban kulata ba na tashi na hau gwada kayan. Na cire wata doguwar riga da tsabar tsagar da aka yiwa hannuwanta, baka banbanceta da vest sai idan kaga dogayen lebatun da aka mata, na ja tsaki, nace “gaskiya baki kyauta min ba Janan, wannan ai bata min kaya kawai kika sa aka yi ba wani abu ba”.

Janan tayi murmushi, tace “kada ki damu matar Yaya, zaki gode min ne nan gaba”.

Haka dai na hada kayan naje na shirya su cikin wardrobe, sai dai bani da niyar sanya su a cikin raina koda kadan. Kawai na riga na gama rayawa raina asarar kaya da kudin dinki Janan tayi.

Na koma falo muka cigaba da hirarmu ni da ita, har yamma tayi, Is’hak da zai kaita gida ya mana sallama da yake yau zata koma gida. Na rakata har bakin motar muka yi sallama da ita cike da kewa da kauna.
Anan muka hadu da Mimah itama tazo mata sallama, naja hannunta muka koma sashena, na kunno mata cartoons tana kallo, ni kuma na shiga kicin na fara hada dinner.

Da dare sai ga Yaya Bilal ya dawo da sabuwar waya kar a kwalinta, da sabin sims guda biyu.
Nace “ita fa waccan wayar tawa?”.

Bai ko kalleni ba, yana ta tura abincin dana girka mishi, yace “nayi kyauta da ita!”.

Na turo baki gaba kamar zanyi kuka, nace “amma fa akwai lambobin mutane da dama da zan rasa, kuma za ayi ta kirana ba’a samuna!”.

Yace “manufar hakan kenan ai dama, ba zai yiwu in zauna in rabbe hannu a kirji ba ina kallo wasu gardawan kawai na kira min mata ba. Ban yarda ki ba kowa lambar wayarki ba sai wanda ya dace, kina ji na?”.

Duk da na jinjina wannan karfin iko da mallaka, hakan bai hana ni amsa shi ba, nace “to, nagode, Allah ya kara budi”.

Ko baiyi tunanin zan amince cikin sauki ba ne? Ya kalleni cikin mamaki, kafin yayi murmushi yace “yauwa baby na, ko ke fa?”. Muka cigaba da cin abincinmu.

Bayan mun gama, ya wuce dakinshi zai watsa ruwa a cewarshi, ni kuma na koma dakina nima. Nayi brush, na fito na sanya kayan barci, nayi shafa’i da wutiri, sannan na kwanta.
Ban jima da kwanciyar ba sai gashi ya turo kofar dakin ya shigo. Ya kashe wutar dakin tare da hayowa kan gadon da nake, ya janyo ni cikin jikinshi.
Gabana dukan uku-uku yake yi, musamman lokacin da naji ya fara aika min nauyayan sakonni a cikin sassan jikina. Sai da tafiya tayi nisa, ni a kaina na fara fita daga hayyacina, naji tausassan sautin minshari yana tashi a kusa dani. Sai dai wannan karon, ban samu kaina da darawa kamar jiya ba, daga kai nayi ina kallonshi cike da mamakin abinda yake faruwa. Wani abu a tattare da wannan lamari just seems off.

*

Wasa-wasa abin dariya fa yake neman juyewa ya zama abin kuka. Kullum haka abin yake kasancewa, wani abin mamaki ma shi Yayan kamar bai san hakan tana faruwa ba. Saboda washegari normal zamu tashi ni dashi, babu wata alama ta ya tuna abinda ya faru a daren daya gabata a tattare dashi. Damuwa ta fara lullubeni, tunani ya fara addabata, tabbas akwai wata a kasa. Sai dai kafin in tono abinda yake a kasan, har ranar Lahdi ta zagayo, ranar dana fita girki, ranar da zamu koma Abuja kuma.

Ranar tun da safe na gama hada duk wasu kaya da zan tafi dasu. Duk wadanda yakamata mu yi sallama dasu, mun riga mun yi.
Karfe hudu Yaya ya leko yace min in fito zamu tafi, tun dazun aka fitar da kayan dana riga na shirya. Su kuma kayan dakin na samu manyan ledoji na lullubesu saboda kura.

Na fito tare da kulle kofata, na saka makullin cikin jakata.
Na leka sashen Anty Sarah na sanar da ita zamu wuce, ta saba Rabi’ah a kafadarta muka fito ni da ita.
Yaya Bilal da Yaya Jameel suna tsaye a gaban motar suna tattaunawa, muka tsaya anan gefensu muna jiran Raheemah ta fito. Sai yau kannen nata suka hada kan kayansu suka tafi. Da safe naga ana ta fita da kaya da tarkace, kusan zaryarsu biyu. Wani saurayin Salame ne yake ta zaryar kai kayan da dawowa ya lodi wasu. Na fito daga sashen Anty Sarah da safen, naci karo dasu sun fito kowacce na jan akwati kamar zasu je ci rani. Suna ta kwashewa mai motar albarkar saboda ya tsaida su suna ta jiran shi, suka daka min harara lokacin da suka ganni, ni kuwa na daga kafada na wuce abina.

Sai da muka kusa yin mintuna biyar muna jiranta a wajen, har sai da Yaya ya kai ga kiranta ya tunatar da ita muna jiranta fa, amma babu ita babu alamunta.
Yaya ya shaka, ya bude min gaba tare da umartata akan in shiga mu tafi, Yaya Jameel yace “kai kuwa ayi haka? Ku dan kara jiranta mana”.

Yaya yace “yo ai ko aikina kenan zaman jira, yaci ace an zo an sallameni. A kanta zan kare ne?”.
Yana tashin motar, sai gata ta fito tana takunta dagwas-dagwas kamar bata shanya mutane suna jiranta ba. Tazo ta gefen inda nake a zaune, ta bude kofar tayi wani kerere, ita bata juya ba, ita kuma bata ce komi ba, sai muzurai.

Yaya ya kalleta cikin kullewa, “idan ba zaki tafi bane, ki maida mana murfin motar mu mu wuce”.

Bata ce komi ba, ta maida murfin motar da karfi ta rufe kamar zata balla shi. Ta bude baya ta shiga tana harare-harare da muzurai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button