A ZATO NA COMPLETE

Nayi shiru ina jinta amma hankalina bai kwanta da hakan ba, a tunanina da wani ido kuma zan iya kallon su Fatsu idan wannan maganar ta fita?.
Da lallami da nasihu ta shawo kaina na amince ta fadawa Fatsu ta fadawa Malam, sai da tayi alkawarin ba zata fadawa Yaya Mudatthir ba, amma nasan ko bata fada mishi ba, su Malam zasu fada sannan muka yi sallama da ita na kashe wayar.
Falo na koma naci gaba da jiran su Janan.
Sai wajen karfe sha daya da rabi sannan suka iso. Na fita waje na tarosu da doki na. Nan muka rungume juna muna juyi dasu, sai da muka gama dokin sannan naja su muka shiga ciki. Tunda muka dawo, sai yau suka zo. Baki a dage suka dinga kallon ko’ina suna santin gidan, sai dana musu tour din gidan suka gani sannan muka zube a kan kujerun falo. Na dauko cookies din dana musu da dambun nama da lemun kankana, lemun zaki dana yanka fresh strawberries a ciki, na ajiye musu. Kafin na leka dakin Yaya na sanar dashi sun iso, na koma wajensu.
Muna zaune muna ta hira ya fito, duk suka zame daga kan kujeru suna gaida shi. Ya amsa har yana hadawa da tsokanar su Harira suna ta dariya. Kujerar da nake zaune mai daukar mutum biyu ce, a tsakiyarta na zauna, fulullukan kujerar kuma a gefe da gefena, amma a haka ya kutsa ya zauna kusa dani. Na janye filo daya na kara matsawa gefe na bashi waje sosai.
A nutse suke hirarsu ta yan uwa wadda rabinta maganar makarantarsu ce sai kuwa zancen dangi da yan’uwa, bayan sun gama gaisawarsu, ya koma dakinshi bayan ya umarceni da shima in kai mishi cookies da lemun, nace to.
Bayan sun gama, muka koma dakina, sai da suka leka ta dakin Raheemah suka gaidata sannan muka wuce dakin nawa. Nan na barsu suna ta kara santin dakin, na koma na kaiwa Yaya cookies din, da kyar ya barni na koma wajensu. A cewarshi ba haka na sabar mishi ba. Nace “ni da zamu zo ma mu fita dasu yanzu? Ballema, na yau ne fa kawai!”.
Ya wani turo baki har ya bani dariya. A haka dai na samu na zame na koma wajensu muka cigaba da hirarmu.
Tare dasu muka shiga kicin muka yi abincin rana, muna yin sallah azuhur muka fita rabon katin gayyata. Sai wajen karfe hudu muka dawo, don dama ba wasu gidaje masu yawa muka je ba, muna dawowa suka koma.
Washegari sai ga Fatsu ta kira, nasan akan maganar ce, da kyar na iya dagawa, kunya kamar kasa ta tsage in shige. Nan ta bani shawarwari da wasu addu’o’i da tace inji Malam tace mu dinga yi kullum daga ni har Yayan, ta maganin sihiri ce da sammu. Sannan tace akwai wani magani da za’a kawo mana hade da rubutun da aka saba kawowa, wanka ake yi dashi, mu gwada yin amfani dashi mu gani. Nace to, tare da mata godiya. Taci gaba da min nasiha game da rayuwar aure, tun ina jin kunyarta ma har nazo na daina don ita kam babu ruwanta. Mun jima sosai akan wayar kafin muka yi sallama.
A hankali bikin yana ta matsowa, kwanaki kuma suna wucewa. Na samu da kyar da jibin goshi an barni inje wajen biki inyi kwana hudu, daga can in wuce Katsina in musu kwanaki biyu. Zan dawo Abuja inyi sati biyu ko uku, sai in je Gashua. Duk yadda naso akan ya barni inyi ziyarar gabadaya, ki yayi, dole na hakura musamman da naga yana nema ya rufe ido yace bikin ma na fasa zuwa.
Ranar Laraba zasu fara shagulgulan biki, don haka nayi niyar tafiya ranar talata. Idan aka gama biki assabar, Lahdi in wuce Katsina.
Ranar litinin, ana washegari zan tafi. Ranar babu aiki saboda ranar hutun ma’aikata ce.
Da yake girkina ne yau, bayan mun gama karyawan safe, na koma daki na. Na cire kayan barcin dake jikina, na fada bandaki nayi wanka, bayan na fito na tsaya a gaban mirror na shafa mai, yau ko hodar ban shafa ba sai dan wet lips kawai, na bude wardrobe ina laluben abinda zan sanya.
Daga karshe dai idanuna suka sauka akan wata rigar atamfa, cikin dinkin da Janan ta kai min ne, ban taba sanyata ba sai yau.
Na fiddota tana ta tashin kamshin turaren kayan dana sanya a cikin wardrobe din kafin in shirya kayana.
Rigar doguwa ce, hannuwanta kanana ne da suka tsaya a damtsen hannuna, daga saman kafadar rigar an yi wani irin yanka ta yadda duka fatar wajen take a waje, haka daga bayan rigar ma anyi wani irin show me, rabin bayana a waje yake, daga tsakiyar rigar kuma daga baya, anyi tsaga tun daga kasa har tsakiyar rigar, idan na daga kafa ina tafiya tun daga gwiwata har kafafuna a waje suke.
Ni kaina dana saka rigar sai dana tsaya ina kallon kaina kamar ba ni ba yadda rigar ta fito da duk wata kira ta jikina kamar sai da aka auna ni, abin ya bani mamaki ya kuma kayatar dani.
Na kalli waje ta tagar dakin, naga yadda hadari yake ta kara gangamowa, tunda safe a haka muka tashi. Yanzu garin yayi luf, ya kuma dan yi duhu. Na dan sauke ajiyar zuciya tare da daukar comb na taje gashin kaina, na dauki dankwalin na daura kawai, gashina kuma ya tsaya a tsakiyar bayana yana ta sheki.
Ina cikin fesa turare, da niyar ina gamawa zan wuce dakin Yaya da nasan yana can yana jirana, sai naji an turo kofar dakin.,
“Bab…!”
Maganar daya fara ta tsaya mishi a makoshi. Na juya cikin mamaki na kalleshi, yana tsaye a bakin kofar dakin, baki a dage yana kallona, with admiration.
Na saki murmushi a tausashe, ko bai fada ba, nasan kwalliya ta biya kudin sabulu.
Na danyi juyi a gabanshi kamar wata wadda take fashion parade, na sake juyawa ina kallonshi, “nayi ne?”.
Ya girgiza kai kamar yana shaking wani abu daga kan nashi, ya maida kofar ya rufe tare da takowa zuwa inda nake a hankali, ya tsaya a gabana. Hannu yasa ya kamo habata, na daga kai ina kallon idanunshi da suke karewa ilahirin jikina kallo, “Subhanallah! Just Masha Allah, baby na ba zaki gane irin kyawun da kika yi bane wallahi. Fatabarakallahu ahsana khaliqeen!! Dama haka kike, amma shine baki taba yi min irin wannna kwalliyar ba baby!”.
Na saki yar dariya, “to yanzu ba gashi ka gani ba?”.
Ya sake ni tare da ja da baya yana kara kare min kallo, ni kuwa nayi humoring dinshi ta hanyar sake yin wani juyin, na kara wani. Ina juyowa, tun ma kafin in samu damar daga idanuna in kalleshi, in ga wani hali yake ciki, naji saukar lebenshi akan bakina.
Abin ya daukeni a ban shirya ba, na dan yi sak na yan sakanni kafin na biye mishi na kara kawata abin. Lokaci mai tsayi, kamar ba zai bari ba, kafin ya sakeni a hankali tare da sake dagowa ya kalleni. Hannuwanshi biyu yasa ya tallabo kumatuna, “baby…!”, kadai ya iya furtawa cikin wata irin murya dana kasa tantance idan tashi ce, kafin ya sake lalubar bakina. Wannan karon hannunshi yasa cikin gashin kaina yana yamutsawa. Ban tantance ba naji an daga ni sama cimak, anyi kan gado dani.
Wani abu a tattare dashi yau ya banbanta da sauran lokutan da muka kasance tare, bai taba zurfafa wasanninmu irin na yau ba, ban taba jin intense abu irin na yau ba. Haka kawai naji zuciyata ta hau bugu, babu kakkautawa.
Daidai lokacin da naji an saki ruwan sama mai karfi, lokacin na jiyo ana jan wata certain addu’a, kafin in gama tantance ainihin abinda yake faruwa, wani irin zafi da ban taba jin kamar shi ba ya ratsa ni, na dan saki ihu, a lokaci daya yatsun hannuna suna lumewa cikin fatar bayanshi cikin azaba….
…….
(Ehhhemmm!!).
*☆⋆40⋆☆*
Karfe biyu ta gota lokacin dana farka daga barcin daya daukemu. Yaya yana gefena, kaina yana kan hannunshi daya, dayan kuma ya zagayo bayana dashi yadda na shige jikinshi sosai. Yanayin garin yayi sanyi mai dadi sosai, saboda ruwan da aka gama yi.
Nayi dabara na zame a hankali ba tare da nayi motsi mai karfi da zai tashe shi ba.
Zanin sallata dake ajiye a gefen gadon na dauka na daura, na shiga bandaki.
Duk da ciwon da nake ji a jikina, amma ba wani sosai dinnan bane da zai hana ni tafiya. Yaya Bilal was very gentle.
Na hada ruwan wanka, na shiga ciki nayi duk abinda ya kamata. Na dauro alwala na fito Zuwa yanzu kuma normal nake jina, duk gajiya, ciwon jiki da wani zafi ya tafi sai dan kadan wanda zan iya manejin shi.