A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Har yanzu yana kwance yana shakar barcinshi. Nayi zaton motsina zai tashe shi, amma har na gama dauke kayana da aka watsar dasu can gefen gado, na linke nashi, na dauko wasu kayan na sanya, bai ma san ina yi ba.
Na zauna a gefen gadon, na fara daddabar filon da yayi matashin kai dashi a hankali, ina kiran sunan shi.

A hankali ya fara motsi, ya bude kyawawan idanunshi suka dira a kaina. Murmushi ya saki mai taushi, “baby. meye haka nake gani?”.

Nima na saki murmushin, “lokacin sallah ya wuce”. Abinda nace mishi kenan, na mike tsaye.
Ya fara kokarin tashi zaune shi kuma, ina ganin haka na juya da sauri kamar zan kifa, na wuce inda na shimfida abin sallah na tada kabbara. Ina jin sautin dariyar daya saki a hankali yana wasu maganganu da kunnena bai jiyo ko menene ba, kafin ya shige bandaki na.

Kafin in gama sallah har ya fita zuwa masallaci.
Ina gamawa na yaye zanin gadon dake kai, na jefa shi cikin washing machine na shimfida wani, sannan na fita da hanzari domin in dora abincin rana. Duk da dai yanzu kowa yana dafa abincinshi na rana ne, na kanyi kokari a ranakun da muka samu hutu ko weekends in hada abincin gidan gabadaya.

Ina fitowa daga dakina, Raheemah ta fito daga nata dakin. Tayi tsaye hannu a kirji tana kallona ina kokarin rufe kofar dakina da mukulli, har na gama na wuce ta gefenta, sannu kawai nace mata wadda ban tsaya naji ta amsa bama na wuce.
Cikin sauri na hau yanke-yanken abubuwa, na fara sanwa.

Ina cikin yin girkin Yaya ya dawo, kai tsaye kicin din ya fado don ta karamar kofa ya shigo kamar yasan a kicin din zai sameni.
Ina tsaye ina kada miyar kubewa a cikin tukunya. Ya rungumoni ta baya, kanshi yana sauka a gefen wuyana. Na fara kokarin zamewa daga jikinshi, amma ko motsi bai yi ba.

Yace “bai kamata ace kina aiki ba yanzu, in fact kamata yayi ace yanzu kina kwance ne kina hutawa. Are you okay?”.

Kunya ta rufo ni kamar kasa ta tsage in shige, nayi kasa da idanuna tare da daga kai.
Murmushi yayi, “ni fa kada ki fara min wani sadde-sadden kai, don ba zan laminci hakan ba. Zaki iya yin girkin? Idan ba zaki iya ba kinga ki barshi, bari in tura yanzu a siyo mana”.

Nace “ni fa lafiyata lau, kuma zan iya yin girkin. Yanzu kawai kaje ka zauna, ko kaci gaba da wasu ayyukan naka, yanzu abincin zai sauka”.
Maimakon ya sake ni, sai ma kara janyoni jikinshi da yayi, “na ki wayon”.

Nace “Yaya…”.
Kafin in karasa fadin abinda zan fada, muka ji anja wani irin tsaki, duk muka juya muka kalli Raheemah dake tsaye a bakin kofar kicin din.

Fuska a murtuke take kallon Yaya, “wallahi an dai fadi babu nauyi, girma kuma ya fadi. Ban da tsabar jaraba ma da masifa, da tsakiyar ranar Allah Ta’ala ma ba za’a daina jaraba ba? Mu dai bamu saba ganin wannan jarabar ba, idan ma ta wanke ta baka ka sha ne, to Allah ya tsare ka”.

Ni baki a dage nake kallonta, me yasa matar nan ta saka min idanu ne a cikin rayuwata? Kada dai ace… ta san abinda ya faru yanzu? Na kalleta cikin zare idanu.
Yaya ma bai ce mata komi ba, sai ma kara nutsa kanshi da yayi a wuyana yana peppering wajen da kananun sumba, kamar bata wajen.

Ta sake doka wani tsakin, “wallahi an dai ji kunya, ya biyewa yarinya karama suna shirme a cikin gida!”. Ta fita daga kicin din tana cigaba da mita da zazzaga masifa.
Na ture shi daga cikin jikina a hankali, wannan karon ya ja da baya ya tsaya yana kallona, cikin turo baki nace “don Allah ka tafi dakinka ka huta, yanzu zan kawo maka abincin”.

Ya shafa sumar kanshi, “but ke ce yakamata ace kin huta baby ba ni ba!”.
Abin nashi ya fara kokarin yin yawa, cikin sanyin murya nace “na fada maka lafiyata lau, don Allah ka tafi kawai”.
Ya daga kafada, “shikenan, tunda kin dage. Amma ki tabbatar yau babu wani aiki da zaki kara yi, ina jiran ki a falona”.
Sai daya manna min peck a goshi, sannan ya fita daga kicin din. Na sauke ajiyar zuciya a hankali, na juya naci gaba da ayyuka na.

A takaice sai bayan la’asar sannan muka ci abincin rana yau. A falon shi na shimfida mana ledar cin abinci, muka zauna. Yaya yafi son cin abinci a kasa, sannan cin abincinshi yafi son su ci tare da wani ko kuma matar shi, saboda haka yanzu abincin safe kadai muke ci a kan dinning. Na dare tun kafin ya dawo daga wajen aiki nake kaiwa falonshi in shirya mishi, muci kayanmu. Ita kuma sai in shirya mata nata akan dinning din.

Bayan mun gama cin abincin, hana ni motsawa ko nan da can yayi. Muna nan har aka kira sallar magriba, sannan ya tafi masallaci. Sai lokacin na dauke kayan abincin na kai kicin. Akwai yar aiki da take zuwa kullum ta mana sharar falo, wanke-wanke da kuma goge-goge, tana dai yin sharar ranar girkina, amma sauran ni nake yin komi da kaina. Musamman ma gyaran dakin Yaya Bilal da falonshi. Ranar girkin Raheemah ma Yaya da kanshi ya umarceni akan in dinga gyara mishi, tunda ita ta gwammace ta mike kafa dai-daya akan kujera tana murza channels, ko kuma ta shura takalmi ta bar gidan yawon gidan makota, akan ta zauna ta gyara dakin mijinta. Ni kuwa ban nuna kyashi ko jin haushina ba, na cigaba da gyara mishi daki.

Dakinshi na koma nayi sallah, ina karatun Al-Kur’ani har aka kira isha’i nayi.
Yau Yaya bai shigo da wuri ba, sai wajen karfe tara ya dawo. Muna babban falo daga ni har Raheemah muna kallo, ko in ce tana kallo, ni a zaune kawai nake.
Ya dawo da ledoji a hannunshi, na tashi na tarbo shi. Dama yace kada in damu da yin girki yau. Na bude ledar naga tsire ne da balangu, yoghurt da roll cakes.

Na ajiye su anan, na shiga kicin na dauko plates nazo na zuba mana. Da ya cewa Raheemah ta sauko, sai ta turo baki gaba, cikin alamun mita tace “uhmmmm! Da yake ita yar gaban goshi ce, dama mana. Yanzu ni har na isa in ce ba zan yi girki ba, ka siyo abinda zamu ci ba tare da ka bata min rai ba?”.

Na girgiza kai a hankali cike da takaicin matar. Aikin kenan fa kullum, sam bata da godiyar Allah. Baka taba yin wani abin arziki ba tare data gwasale ka ba, musamman Yaya. Yana iyaka bakin kokarinshi wajen ganin yayi adalci a tsakaninmu, amma bata taba gani ba. Yadda duk karshen wata yake bani dubu ashirin saboda hidimar zuwa da dawowa, musamman cin abinci a asibiti duk da na ce mishi bana bukatar su, amma ya ki, haka yake daukar ashirin dinnan ya bata, maimakon godiya sai ce mishi tayi, “wai ita yanzu shikenan sai ta albarkaci na zata dinga cin kudin hannunshi?”, abin ya bani haushi ya kuma bani mamaki kwarai.

Yaya ya daga baki zai amsa ta, nayi saurin tarar numfashinshi, nace “anan zaka ci ne ko kuma zaka koma karamin falo?”.
Yaya ya kalleni sosai, nima na kara kallonshi, da alama ya fahimci dalilina na tarar numfashinshi, yace “mu koma falona”.
Nayi murmushi tare da kanne mishi ido daya, wanda yasa ya saki murmushin shima tare da mikewa tsaye. Na dauki plate din dana zuba mana namu a ciki,na wuce na kai falonshi, na dawo da niyar daukar yoghurt da cake din.

Tana tsaye a gaban Yayan kamar wadda take tsare shi daga shiga falon nashi, ihu take tun karfinta, wai ya maidata mahaukaciya, tana magana ya dinga shareta.
Yace “wai ke me yasa ba kya son zaman lafiya ne ko kadan Raheemah? Me ma aka yi daya janyo fada da daga murya anan?”.
Tace “dama yaushe zaka gani tunda an rufe maka ido? Ni da ake wa rashin adalci ni nake gani, kuma wallahi ba zan yarda ba!”.
Yace “sai ki dauki mataki…”, ya zagayeta ya wuce. Nima na kwashe sauran kayan na bi bayanshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button