A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Falon shi kamar nan ne wajen shakatawarmu da hutawa, Raheemah bata cika shiga ba musamman ma ranar da ba girkinta bane, ni kuma ina kokarin kaucewa wajen ranar girkinta saboda shiga hakkinta. Ranar girkina kam acan nake yini musamman idan Yaya yana gida, mu yi ta hirarmu, ko wasanninmu, watarana kuma sai dai mu kwanta kawai, watarana kuma idan yana aiki in barshi yayi aikinshi ni kuma inyi busying kaina da wasu abubuwan.

Yanzu tashar CNN ya kunna yana kallo, ina gefenshi muna cin naman a hankali, lokaci zuwa lokaci zamu dan tattauna akan wani case da zamu ji an fada a tashar ko kuma wani abu. Har muka gama ci, na dauke kayan. Na dawo falon, nayi matashin kai da cinyarshi har dare yayi, ya kashe kayan kallon muka wuce dakinshi.

                           ~~~

Da kyar ya bari muka yi sallama dashi wahsegari na tafi Kaduna. Da kasa ya kekashe akan cewa sai dai in bari mu tafi dashi ranar juma’ah, kamar zan mishi kuka haka na dinga rokonshi ina magiya, nace “idan ma na zauna me zan maka ne Yaya? Ba fa ni zanyi girki ba yau”.
Da kyar dai, muka yi sallama ya tafi wajen aiki. Wajen karfe goma sha daya, muka bar garin Abuja.

Tuni gidan biki ya fara cika da yan biki. Gida ya cika ya tumbatsa Masha Allah. Bayan mun gaggaisa da mutane, wasu yan uwan nasu ba da basa cikin kasar ko kusa da gari, sai yanzu muka samu muka gaisa dasu.
Muka lume can kuryar dakin Yaya ni da amarya Janan muna hirar yaushe gamo. Tayi ta min shakiyanci, wai nayi fresh, meye sirrin, ko har an bani ajiya ne?.

Na kuwa danna mata harara, “wai don Allah meye matsalar ki ne? Kullum kiyi ta lakaba min abinda bani da?”.

Ta kuwa kwashe da dariya, “to Malama, alamu ne suka nuna haka ba wani abu ba. Ki duba fa yadda kika wani ciko tubarkallah, kin kuma yi haske da abubuwa, idan ba ciki bane to menene?”.

Na kada mata idanu, “kiwon Yayanki ne kawai!”.
Ta saki ihun dariya, abinda ya janyo su Harira dake falo kenan suma suka fado, suka cigaba da shakiyancinsu. Dana gaji sai na janyo wayata, na dannawa Yaya kira na koma can gefe muka kwashi hirarmu ta masoya.

Washegari aka yi kamu anan cikin gidan. An dauko masu decoration da masu raba abinci, abokanmu da yawa sun zo, haka dangin ta dana Almu sunyi kara ba kadan ba. Gida ya dauki jama’a sosai. Har karfe goma na dare ranar muna kan kafafunmu a tsaye muna kokarin gyara gidan.

A dakin su muka yi parking, baki duk an kaisu dakunan dake cikin gidan, wasu kuma suna dakin Yaya da Ummah.
Ummah ta kawo mana damammiyar fura da kanta, da tasha nono ga sanyi sosai. Tun bayan aurenmu da Yaya, kamar an kara mata kaunata haka nake gani, tunda nazo take ta nan-nan dani, abincin da zan ci ma daga dakinta ake kawo min. Sai naji nima kimarta da mutuncinta sun karu a cikin idanuna.

Bayan munyi wanka don mu dan warware gajiya, muka sha furar data kawo mana, sannan fa kowa ya nemi makwanci. Lokacin karfe sha daya ta wuce. Naso in kira Yaya kafin in kwanta, tun da safe da muka yi waya dashi bamu kara yi ba, amma sanin suna tare da Raheemah yanzu yasa na daure zuciyata. Sai na rubuta sako mai cike da kalamun nuna kewa da kauna, na tura mishi. Cikin sakanni talatin da shigar sakon wayarshi, ya dawo min da amsa.

Nan muka kwashe kusan mintuna arba’in muna musayar kalaman soyayya, kafin muka yi sallama dashi.

Washegari aka yi mothers eve, sai ranar Anty Ameerah tazo. Anty Sarah ita tun jiya tazo, sai dai bata kwana a gidan ba, gidan Yayarta dake aure anan cikin Kaduna taje ta kwana.
Ana gama taro Anty Ameerah ta koma Zaria.

Sai ranar juma’ah Yaya yazo shi da Raheemah. Tunda suka zo bata ma zauna a gidan ba, ranar walima muka yi. Yau ma kamar jiya, ana tashi wajen karfe shida Anty Ameerah ta wuce, ita kuwa Raheemah da tunda suka zo kayanta ma a dakin Yaya ta ajiyesu, ta wuce can. Bata shiga cikinmu ba mu kawayen amarya, muma kuma bamu nemeta ba.

Washegari aka daura aure, muka kai amarya gidan aurenta dake can unguwar rimi. Gini ne na kin karawa, idan ka shiga kamar kada ka fita saboda haduwarshi.
Yanmatan sun ce babu inda zasu tafi sai anguna sun zo sun sayi baki, duk da da yamma ne aka kaita. Na gama shan dariyata nace bari inyi tagging dai nima.

Wajen karfe shida na yamma sai ga kiran wayar Yaya, na fito daga cikin hayaniyar hirar da suke yi, na amsa kiran.
“ki sameni a kofar gida”, kawai yace ya kashe wayar.

Na bi wayar da kallo cikin mamaki, kafin na sake kiranshi, nace “muna fa gidan Janan yanzu haka”.
Yace “ehh, nan din fa”.

Cikin sanyin jiki na koma gidan. Su Anty Sarah da basu jima da zuwa ba, su ganin gida suka zo yi kafin su koma Zaria, ciki har da Anty Ameerah, suna cikin bedroom inda amarya take suna tasu kalar hirar suma.
Na matsa na radawa Janan zan tafi, tace “ina zan tafi yanzu bayan ba’a zo sayen bakin ba?” Nace mata “Yaya yake nema na, yace yana waje”.

Ta zaro ido, nayi gaggawar kai mata dukan wasa a hannu kafin tayi tunanin fadin wani abu silly, nace “kada ki wani kawo min wata maganar banza anan, sallama ce kawai zamu yi saboda yau zasu koma Abuja shi da Raheemah”.

Amma bata fasa ba, sai data yi commenting din dai. Na dauki jakata kawai na musu sallama akan cewa zan koma can gida, na fita.

Kamar yadda yace kuwa, yana kofar gidan. Na bude murfin motar na shiga, yayi murmushi tare da janyo ni jikinshi, mun dan jima a haka kafin ya dago ni yana kallona, yace “kai baby na, da alama ke ko kewata ma baki yi ba, ji yadda kika yi wani irin kyau kamar ba ke ba?”.

Nace “a haka din?”.
Yace “sosai ma!”. Ya fara kokarin tada motar.
Ban tambayeshi inda zamu je ba, ya fita daga unguwar. Sai gamu a kofar wani gida a can cikin GRA. Na kalleshi cikin mamaki lokacin da naga yayi horn mai gadi ya bude mishi kofar ya shiga.

Muka fito daga cikin motar, kai tsaye ya shige falo dani. Gidan a gyare da komi a ciki, sai dai babu alamun mutane a ciki.
Nace “nan fa?”.

Yana ajiye wayoyinshi akan center table yace “gidan da muke kawo baki ne idan aka yi, musamman ma lokutan biki irin haka”.

Bandaki ya nuna min yace in shiga inyi alwala, shi kuma ya tafi masallaci. Sai bayan isha’i ya dawo da ledar shake da kayan marmari da take away na abinci a hannunshi.
Ganin take-takenshi, nace “wai ba yau zaku koma ba? Kuma kada ka manta fa tare da matarka kuka zo”.

Yace “to sai me? Ina lissafe da yau zaki fita daga girki fa!”.
Na zaro ido ina kokarin ja da baya daga rarumar daya kawo min, amma duk da haka sai daya cafko ni yana dariya, yace “come on, anjima kadan fa zan maida ki”.
Nace “da gaske?”.
Yana murmushi cheekily, yace “da gaske”.

A takaice ban kara tunawa da wannan maganar ba sai da naga mun yi ido hudu kuru-kuru da hasken rana, washegari kenan.

Karfe tara Yaya ya shigar da motarshi gidan su Ummah, kunya kamar zan nutse a kasa, duk da dai babu wanda yasan abinda kenan.

Yana kashe motar, na fita da sauri na fada gidan. Allah ya taimakeni babu kowa a falon, da alamu baki sun wuce, na fada dakin su Harira daban. Nan ma FirdauFirdausi kadai na tarar tana gyara gado, ta kalleni cike da mamaki, “daga ina haka?”, nayi banza na kyaleta.

Karfe biyu na rana, muka wuce Katsina ni da Is’hak da Yaya ya umarce shi daya kaini. Munyi sallama dasu suna ta min sannu da Ala huta gajiya. Shi Yaya sai da yamma naji yace zasu koma.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button