A ZATO NA COMPLETE

Yaran gida sun sha ihu da murnar ganina, aka min masauki a dakin Anty Alawiyya. Da yake ranar Lahdi ce, Baba yana gida.
Aka kaiwa Is’hak abinci yaci, a ranar ya koma Zaria, ranar talata zai dawo ya maida ni.
Ranar haka muka raba dare ni da kannena muna ta shan hira. Sai washegari na shiga gari gaishe-gaishe.
Kulsum ta fara zuwa makaranta abinta, wai wani lecturer ya kyalla idanu a kanta yana ta bibiyarta. Nace mata “kema ki saurare shi mana, sai kiga kun daidaita”.
Ta girgiza kai, “ba yanzu ba Na’ilah, ba zan kara yin sake irin wanda nayi ba gaskiya. Ke dai kawia ki taya ni da addu’a”.
Nace “to shikenan”.
Wannan zuwan nawa naji dadinshi sosai, sai da naji kamar kada lokacin komawata yayi.
Ramata kanta wannan lokacin naga ta sassauto sosai, ko kuma zata iya yiwuwa rashin lafiyar da take yi ce ta sanya hakan.
Ranar talata sai da yamma sannan muka yi sallama dasu cike da kewa, muka wuce. Dole sai a Zaria muka tsaya muka kwana, washegari Laraba muka wuce Abuja. Amma sai da na tsaya a Kaduna sannan.
Na koma gida muka cigaba da gudanar da rayuwarmu. Babu abinda ya canza har yanzu, sai ma wata tsirfa. A gidan na tarar dasu Salame ranar dana koma, wai suna ta shirye-shiryen bikin Haleemo. Sai ranar assabar suka bar gidan, habaici dai har sai dana gaji da ji, amma babu wanda na taba tankawa a cikinsu.
*
Ranar Lahdi da yamma, muna babban falo a zaune, Raheemah ce take yin girki, Yaya ya fita zuwa cikin gari da wannan yammar. Don haka daga ni sai ita, duk da ita tana ta zarya ne ma tsakanin kicin da falon saboda girki da take yi.
Kawai sai karar turo kofa muka ji, mu daga kai haka, sai ganin Anty Ameerah muka yi ta fado falon, wasu matasan yanmata biyu na take mata baya, yayin da maigadi da mai ban ruwan fulawowi suke turo akwatunanta.
Raheemah data mike tsaye zata shiga kicin, tayi tsaye kyam tana kallonsu, nima na bi su da kallon.
Yaya har ya fita bai yi magana akan dawowarta ba, ko kuwa bai san da zuwan nasu bane? Oho!.
Ita kuma ko da wacce tazo?.
Suka mana sannu da gida, Raheemah ta zungura baki gaba ta shige kicin, na amsa musu a sanyaye. Muka gaisa kadaran-kadahan dasu, suka ce sunyi waya da Yaya yace su tambayeni makullin dakinta, na tashi na shiga dakinshi na dauko musu, na nuna musu dakin, suka yi godiya suka tura kai suka shiga ciki, ni kuma na koma falo cikin wani irin yanayi.
Sai da dare Yaya ya dawo. Da yake ranar Raheemah zata fita daga girki, aka yanke shawarar Ameerah zata amsa. Da haka muka aka tashi kowa ta wuce dakinta.
Har ta fita daga girkin, wani ya sake zagayowa, babu wata matsala. Zama muke kadaran-kadahan da ita, idan muka hadu a falo, ko a dakin Yaya, za’a gaisa da ita a mutunce, haka babu ruwanta da shiga harkar da babu ruwanta. Ban taba jin bakinta yayi wata mita ba, ko ya tado magana. Kai ita kwata-kwata ma baka ganinta sai ranar girkinta, sauran ranakun a daki take yini cur, idan ta fito sai dai kicin, ta kwashi kayan makulashe ta koma daki.
Sai nake ganin kamar hakan yafi akan ka wuni kana zage-zage da yada habaici. Har nake cewa kila zata fi Raheemah saukin kai.
Little did I know….
*☆⋆41⋆☆*
Ranar Juma’ah na karbi girki a hannun Ameerah. Kamar yadda na saba, idan ina aikin rana na kan yi iyaka bakin kokarina in ga na dawo da wuri domin in dora abincin dare.
Yau ma aikin dare nayi, na samu wata nurse da muka fara gaisuwar mutunci da ita, Hanifa, na roketa akan ta shigo da wuri ta rike min nawa aikin tunda ita aikin dare take yi, ta amince. Bazawara ce in her 30th. Kirkinta yasa muka fara gaisawa sama-sama da ita, har dai aka fara gaisawa ta sosai. Yanzu yawanci ita take taya ni rike aikina idan zan fita da wuri. A gurguje na mata godiya na wuce. Na riga na kira direban da yake kaini, yana waje yana jirana. Don haka ina fita muka wuce.
Sai karfe bakwai da wasu mintuna muka karasa gida.
Cikin sauri na shige daki, ina shiga na hau cire kayan jikina ina jifa dasu a tsakiyar dakin ba tare dana damu akan in linke su ba. Da yake bana yin sallah, a sukwane na fita daga dakin na fada kicin. Babu kowa a cikin falon.
Allah yasa da zan fita da rana nayi miya na ajiye. Ruwan zafi na dora akan wuta, na nufi dakin Yaya da sauri.
Wani lokacin idan ya fita sallar asuba ya kan dawo kafin ayi isha’i ya ci abinci, idan yana jin yunwa kenan. Idan kuma ya ci abinda ya rike mishi ciki a wajen aikinshi ya kan jira sai bayan isha’i.
Yanzu so nake in ga idan yana falonshi, in ga ko yana bukatar ko da snacks ne yaci kafin in sauke abincin kamar yadda nake mishi sau tari, a ranaku irin wadannan idan ban gama abinci da wuri ba.
Tun kafin in karasa falonshi nake jin sautin karar talabijin, sai kuma sautin magana kamar ana yin hira da yake tashi kadan-kadan.
Nayi sallama a kofar falon tare da turawa, kamar yadda nayi zato, Yaya yana falon a zaune akan kujera.
Sai dai zaune a kasa, daf da kafafunshi, don idan ma wani ya kuskure zai iya cewa akan kafafun nashi take a zaune.
Amma ba ma wannan bane ya dauki hankalina ba, ba kuma dariyar dana tarar suna yi ba, kwalliyar data zabga ne kamar zata je gasar sarauniyar kyawu ta duniya, sai kuwa wani zagayayyen kyakkyawan ceramic plate da yake ajiye akan cinyarta shake da waffles da aka kwarara jam daya nutella akai, ga kuma fresh berries. Abin ya bani mamaki har na kai ga dan dakatawa.
Shirun da suka yi suna kallona ne ya sanya na dawo da hankalina kansu. Na danyi murmushi kawai tare da takawa na karasa wajensu. Sannu na mata ta amsa fuskarta da sauran fara’ar dake kan fuskarta lokacin dana shigo cikin falon.
Yaya ya kalleni lokacin da nake zama a gefenshi, akan kujerar kusa dashi, cikin murmushi.
Na gaida shi ya amsa, tare da cewa “har kin dawo? Ya asibitin?”.
Nace “lafiya lau, yanzun nan na shigo. Dama lekowa nayi in ga ko kana bukatar wani abu kafin in gama girki sai kuma naga…”, na kakare ina karewa plate din hannun Anty Ameerah kallo. Daga ganin yadda yayi fresh, kamshi yana tashi, kasan ba’a jima da gama yin shi ba. Probably bayan Yayan ya dawo daga wajen aiki.
Maimakon ya nuna wani abu, ko ita, sai naga yayi murmushi. Yace “ai Yayar ki ta hutar dake, sai ki sanya ranki a inuwa…”, ya dauki daya ya sanya a bakinshi, ya gutsira ya tauna har da hadawa da lumshe idanu, “… kuma yayi dadi sosai. Bismillah, ki taba mana”.
Na girgiza kai a hankali ina kokarin danne wani abu daya taso ya tsaya min a makogaro, kwacen girki kuma da rana tsakiya kiri-kiri?.
Nace “a’ah, na gode. Bari inje in karasa girkin. Anty Ameerah nagode fa!”.
Idanunta akan allon talabijin tace “babu komi Na’ilah… Yiwa kai ne!”.
Ban ce komi ba na tashi na fita daga falon.
Spaghetti na dafa, nayi warming miyar da nayi. Kafin Yaya ya dawo na kai mishi abincinshi falonshi. Su kuma matan nashi na ajiye musu nasu akan dinning table.
Daki na koma, na shirya kayan dana yasar, na gyara dakin nawa sannan na koma falon Yaya ina jiran ya dawo daga masallaci.
Yana dawowa na shirya abincin, na zauna a gefenshi na zuba mana muka fara ci. Yau abincin kadan yaci, a cewarshi Yayata ta cika mishi ciki. Murmushin yake kawai nake binshi dashi, saboda maganar gaskiya abin ya bata min rai. Akan me ni da girkina, ni da mijina, kawai tazo wai ta mishi girki? Ina so inyi magana, sai dai dole haka nayi shiru saboda bana son yace ina neman tada mishi zaune tsaye a gida, ko kuma bana son zama lafiya, ban godewa abinda ta min ba. Don haka nayi ta kauda maganar ina turata can bayan raina.