A ZATO NA COMPLETE

Ni kaina abincin yau haka nan dai naci shi cikin dauriya kawai. Mun saba idan muna cin abinci, haka zai yi ta yabon girkin da na mishi, wasu lokutan kuma yana ta tsokanata da yan wasannin shi.
Yanzun ma a hankali naji hannunshi yana min tafiyar tsutsa a bayana ta dan slit din da aka bari a bayan rigar dana sanya. Na daga kai na kalleshi a hankali, ya daga min gira challengely, cikin nuna alamun yana jiran yaga reaction dina.
Nayi dan murmushi, ina kokarin ganin cewa ban bari abinda ya faru yau ba ya hana ni samun farincikin raina dana mijina ba.
Don haka na biye mishi. Cikin kankanin lokaci munyi gefe da kayan abincin, sai gani a saman ruwan cikinshi ina kokarin daukar alewar bounty daya boye a bayanshi.
“Baby na…. Zaki karya ni fa, kinyi nauyi da yawa.. Baby, wayyo!”.
Amma kuma dariya yake yi cikin shessheka, nima dariyar nake yi lokacin da naci sa’ar dauko sweet din.
Na koma na zauna a gefenshi ina bare ledar, shima ya tashi zaune yana maida ajiyar numfashi kamar wani wanda ya kwashi wani dambe.
Ina bare ledar na kai baki na hau taunawa, ya kalleni cikin zare idanu, “ba dai cinyewa zaki yi ki hana ni ba ko baby?”.
Murmushin tsokana nayi tare da saka gabadaya sweet din cikin bakina.
Yace “kam, gaskiya ban yarda ba..”.
Ganin yayo kaina gadan-gadan yasa nayi dan ihun tsokana naja da baya, amma duk da haka sai daya damko ni.
Yayi amfani da karfin jikinshi yayi trapping dina a jikinshi ta yadda babu yadda za ayi in kwace, bakina yake kokarin hadawa da nashi da niyar zakulo sauran alewar data rage a bakina, lokacin da aka turo kofar falon aka shigo.. Da sauri na daga kai naga Ameerah ce. Idanuna suka sauka akan agogo, naga karfe tara ce saura. Wani haushi yazo ya cika ni, kowa yasan a cikin gidan nan idan karfe tara ta gabato a cikin gidannan, kowa ya nemi makwancinshi, sai a bar mai girki ita da mijinta. To me kuma ya kawota yanzu?.
Kallon dana bita dashi baki a dage ne ya ba Yaya damar cikashe abinda yayi niyar yi. Sai lokacin ya sake ni, ya koma gefena yana tauna alewar a bakinshi.
Ameerah ta nemi kujera ta zauna, “sannunku da hutawa”. Ta furta cikin fara’a.
Muka amsa mata, ni ciki-ciki, Yaya kuma yana dan murmushi, yace “baki kwanta bane har yanzu?”.
Tayi wani fari da idanu tana rangwada, “wallahi kuwa baby, ban san me yasa na kasa yin barcin da wuri ba yau, shine nace bari dai in zo in rage dare anan”.
Yaya ya daga kai distractedly, hankalinshi gabadaya akan tv, ana hasko wani labari akan wata sharia da ake kwasa tsakanin wani dan uwa da dan uwanshi.
Na mike tsaye ni kuwa na nade ledar dana shimfida mana na kaita inda ake ajiyeta a cikin falon, na dawo ina hada plates da kulolin, sai lokacin na dan saci kallon inda take, ta canza kayan dazu dana barci yanzu, riga da wando na cotton masu kyau da suka bi jikinta, ta dora hular beanie da tattausan silifas mai buzuzun gashi a kafarta. Nayi kwafa tare da kwashe kayan abincin na tafi kicin.
Ina gamawa da kicin na koma dakina. Na shiga bandaki nayi wanka, brush, na dauro alwala. Duk da cewa ina period, hakan baya hana ni kwanciya da alwala a jikina idan zan kwanta.
Bayan na gama, na dauko kayan barci masu kyau da bayyana surar jiki na sanya, na shafe ilahirin jikina da turaruka masu kamshi da nutsar da zuciya, na dora hijabi doguwa akan kayan nawa na fita daga dakin bayan nasa makulli na rufe dakin.
Har yanzu Yaya da Anty Ameerah suna falon suna hira, sai dai yanzu maimakon kujera, ta sauko kasa kusa dashi. Sunyi nisa a hirar da suke yi sosai, basu ma ji lokacin dana shigo ba.
Nima na lalubi waje kusa dashi na zauna. Ban yi kokarin tsoma musu baki a cikin hirar da suke yi ba, na kurawa tv da take ta aiki kallo ba tare da ina fahimtar komi da suke yi, ko suke fada ba.
Hirarsu suke tayi akan wani cousin dinta daya samu aiki da wani babban kamfani da yake kera motoci a kasar Germany, hirar ta gangara ta koma kan businesses da mahaifinta yake yi, har ta sake gangarowa kanta, wai itama tana so ta fara yin business, amma bata san akan abinda zata yi ba. Nan suka fara muhawarar abinda yakamata tayi.
Da dai naga karfe goma ta wuce, sai na tashi na musu sallama na wuce uwar dakan Yaya.
Anan dinma nafi kusan mintuna goma da shigowa kafin naji ya shigo dakin. Ina jinshi ya shiga bandaki yayi abinda zai yi ya gama, sannan ya dawo dakin. Ya kashe wutar, kafin ya hayo kan gadon inda nake, ya janyo ni cikin jikinshi.
*☆⋆42⋆☆*
Gidan shiru, baka jin motsin komi lokacin dana fito daga dakin Yaya na shiga kicin, duk da cewa karfe tara ne lokacin. Nasan hakan baya rasa nasaba da cewa yau din ranar karshen hutun mako ce.
Na tsaya a tsakiyar kicin din ina tunanin abinda yakamata in dora, daga karshe dai na kunna gas na hau aiki.
Sai wajen karfe goma da rabi sannan na gama. Na dauki na Yaya na tafi falonshi na kai na ajiye, sannan na dauki na matan nashi suma na kai falo na ajiye. Lokacin Raheemah har ta fito, tana zaune akan daya daga cikin kujerun falon tana waya da daya daga cikin kannenta.
Na leka dakin Yaya, baya kan gadon amma da alamu yana bandaki yana wanka saboda karan ruwa da naji yana tashi. Na karasa na gyada dakin tsaf, na kawo airfreshner na fesa. Sannan nima na koma dakina.
Kai tsaye wanka nayi, na fito nayi amfani da hand dryer na kafar da gashina, sannan na zauna akan dresser na fara bin duk wani lungu da sako na jikina da turaruka masu kamshi, wadanda nasan suna rikita min Yaya. Kamar kullum, yau ba ban wani tsaya yin kwalliya ba, bayan yar hoda dana goga, wani lip balm kawai na shafa a bakina. Mai kamshi da taste din strawberry. Wani zuwa da Anty Sarah ta taba yi nan, ta kawo min shi. Ban ma taba shafa shi ba sai yau. Na kalli kaina a madubi, nayi dan murmushi ganin yadda na fito tsaf a cikin kayan dana sanya. Riga da siket ne na wani material mai taushi, yanayin dinkin kamar wasu English wears. Rigar mai dogon hannu ce, amma an tsaga hannun tun daga kafada har tsintsiyar hannu, shima siket din anyi tsaga a tsakiyar shi ta yadda bayan kafafuna suke a waje idan ina tafiya. Nayi daurin dankwalina fanka, gashina dana kame a cikin band ya fito yana ta sheki da tashin kamshi. Na fita daga dakin.
Har yanzu Yaya bai fito ba, don haka na wuce dakinshi kai tsaye.
‘oh please!!’, na fada exasperatedly, lokacin idanuna suka sauka akan Ameerah dake zaune akan kujerar hutu dake fuskantar kofar dakin.
Yaya yana gaban dresser da ruwan tokar jallabiya a jikinshi, mai yake shafawa a sumar kanshi, gefe guda abin sallah ne a shimfide, da alamu tashin shi kenan daga kai. Kila sallar walaha yayi.
Yayin da matar tashi take sanye da riga da wando, English wears, kai babu dankwali balle hula, kitson da aka yi mata ya kkwanto har dokin wuyanta. Jarida ce a hannunta tana dubawa, Yaya kuma nata zuba mata hira.
Na girgiza kai a hankali ganin sun zubo idanuwansu kaina, Allah kadai yasan irin takaicin daya ciko min ciki, haka nan na daure na kakaro murmushi tare da karasawa cikin dakin. Yaya ya bini da kallo yana murmushi.
Na karasa gabanshi na tsaya, “Barka da safiya Yaya, har ka tashi?”.
Yayi murmushin nan nashi mai burgewa, “na tashi tun dazu, har na gaji da jiran kizo ki taya ni shiryawa”.
Nayi tunanin yanzu ma cewa zai yi an hutar dani, har na fara plotting irin rashin mutuncin da zan manna musu, nace “kasan fa girki na fita inyi, idan ka gama shiryawa kazo muje ka karya”.
Ya gyada kai, “na kusa, gani nan zuwa. Kinyi kyau fa!”.