A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Ita kuwa Ameerah, ita ce ainihin ma’anar kissa da iya lallabin miji. Ta kowane fanni ba za’a kirata wadda ta gaza ba, ta iya kwalliya, girki, uwa uba iya kula da miji. Matsalar, bata san miji ya gindaya mata doka ta bi ba, sai dai tayi abinda taga dama kawai, babu ruwanta. Akwai lokuta da dama da zai hana ta fita, amma yana saka kafa ya fita, haka itama zata dauki makullin motarta ta fita Wata latest Benz da mahaifinta ya aiko mata da ita, da Yaya yace ta maida, a cewarshi me zata yi da mota bayan ga motoci nan ya ajiye mana? Sai tace mishi su duk gidansu, babu wanda yake tuka Honda da vibe. Ina wajen lokacin da hakan ta faru, sai na kama bakina kawai ina girgiza kai.

Akwai ma wata rana da zai tafi wata seminar ta kwana uku Gambia, tace mishi zata je gida kafin ya dawo, yace mata a’ah. Sai dai yana tafiya, sai ga wannan yar uwar tata data rakota ranar data dawo, da alama anan cikin Abujar take, suka fita babu ko sallama, lokacin itama Raheemah su Salame sun zo, sun shiga gari yadda suka saba, ban ce musu komi ba nima. Ashe Babanta da kanshi ne ya sai mata tikitin jirgi suka tafi kasar France wajen graduation din dan gidan kanin Babanta. Sai ranar da Yaya zai dawo da yamma, ita kuma ta dawo da safe.
Ire-iren wadannan abubuwan dai, ina kula dasu. Ban taba daga baki na fadawa Yaya ba, saboda na farko bana so ace ina tada rigima da zauni tsaye, na biyu kuma bana son ya kasance daga bakina ya fara jin wannan danyen aiki, nasan zai iya cewa kawai na fada ne, don haka na kame bakina na bame.

Tunda dai yanzu duk na karanci halayensu daya bayan daya, ina zaune da kowaccensu ta yadda ta bullo min. Na kan bi duk hanyar da zan bi wajen ganin cewa na kaucewa cece-kuce dasu, idan daya daga cikinsu ta min abinda bai kwanta ba, na kan san yadda nayi na maida musu da martani a aikace ba tare dana bari fatar bakina ta motsa ba.

Ameerah irin mutanen nan ne macizan sari ka noke, sai lokacin na fara yarda da maganganun Janan akan cewa gwanda zama da Raheemah akan Ameerah. Saboda ita Ameerah, sha yanzu ce magani yanzu, idan abu bai mata ba, zata fito tsab ta fade shi, koda cikin masifa ne kuwa. Ita din kamar budadden littafi ce, mai saurin karantawa. Ameerah kuwa ba haka take ba, baka taba fahimtar inda ta sanya gaba. Hakan kuwa yana da nasaba da halinta na danne komi da murmushin da bai idanunta ba, ita ba kamar Raheemah bace sam. Raheemah idan mutum bai mata ba, to kawia bai mata ba, ko kallon inda mutum yake bata yi balle kayi tunanin ta damu da kai. Yayin da Ameerah baka sanin tana son ka ko tana kin ka, sai dai kaga hakan a aikace kawai ba tare da hakan ya nuna a fuskarta ba. Hakan yasa mafiya yawancin lokuta Yaya ya kan yi zaton idan ta aikata wani abu, mistake ne, saboda haka baka da damar da zaka yi korafi.
To a kowani hali dai, haka muke gudanar da rayuwar tamu, yau dadi, gobe babu.

Tunda na fara internship dina sai wannan satin suka fara biyanmu, saboda yar matsala da aka samu wajen shigar da takarduna, amma yanzu komi ya gyaru.

Ranar da aka turo min kudin na gansu kamar a mafarki, har sai da nayi hawaye. Yau dai wahalhalun nan da muka sha, sun fara biya. Na shiga kasuwa, siyayya tun daga kan su Auwal, har matan Baba da shi kanshi, babu wanda ban ssiyawa abu ba, haka su Fatsu dasu Yaya.

Anyi hakan da kwana hudu, na tafi Gashua. Yaya ya sai min tiket din jirgi wanda ya sauke ni a Yobe, daga can na wuce Gashua.
Ba karamin jin dadin yadda na samu su Fatsu nayi ba. Yan biyun Yaya suna ta guje-gujensu da surutu. Sai lokacin naji cewa ashe bayan aurenmu, sau biyu Yaya yana zuwa suna gaisawa. Bai kuma taba gaya min ba. Yanzu ma da zan taho haka ya hado ni da kudin tsaraba wadda sai da nazo nan sannan na siya abubuwan da zan raba. Kamar kullum, a gidan Fatsu na sauka.

Kwana na biyu ina yawon gaisuwa da ganin dangi, ana uku ne muka je Kauyen Alkali wajen Anty Halima. Ba karamin murna tayi da ganina ba. Muka mata yini ni da Sailu da twins, sai da yamma sannan muka koma. A gidan su Sailu muka sauka, na zube akan kujera ina nishin gajiya. Tunda nazo nake a gajiye, barci bai taba isata ba, wanda nafi danganta hakan da gajiyar mota.

Sailu kuwa tunda muka zo ta fada kicin ta hau girki, nan da nan gida ya bade da kamshi. Ina so inje in tayata yin girkin, amma kwata-kwata na kasa motsawa. Wani irin barci ne ya fara fuzgata ba tare dana shiryawa hakan ba.

Sailu ta fito daga kicin, ganina a kwance yasa ta dakata tana kallona, Malam da Abul-khairi suna ta wasan su a tsakiyar falon. Na dago kai a dan galabaice ina kallonta, tace “wai lafiyarki lau kuwa? Tunda muka dawo kika wani langwabe a kan kujera kamar wata mara lafiya?”

Nace “wallahi nima ban sani ba, ina ga kamar gajiyar hanya ce har yanzu bata sake ni ba”.

Ta kyalkyale da dariya, “hahh, ina ruwan ba sabon shiga ba! Idan ma zaki warware ki san abinda yake damunki, ki mike. Ko in zo inyi palpating dinki ne?”.

Na tashi zaune da kyar, “palpat… me??”, na zaro ido, “ba fa haka bane, bani da komi, da gaske”.
Ta gyada kai tana dan murmushi, “kada ki wani gaya min ba haka bane, duk ga alamu nan sun bayyana a jikinki?”.

Nace “kin dai san wannan abin fannina ne ko? To bani da komi da gaske”.
Tace “to ai shikenan, kada dai ki koma barci don an kusa kiran sallah”. Ta koma kicin, nima haka nan na tashi na bita kenan din ko jikina ya dan warware.

Kwana na biyar cur anan, sannan na musu sallama na tafi. Wannan karon motar Kaduna muka wuce kai tsaye, sai wajen karfe hudu muka shiga cikin Kaduna. Jikina yadda kasan an yi min dan banzan duka haka nake ji, ban taba jin wuyar tafiya ba sai yau.

Direban gidan su Ummah yaje ya dauko ni daga tasha zuwa gidan. Nan na samu tarba mai kyau daga wajensu. Su Firdausi suna makaranta, aka kaini dakinsu nayi wanka da sallah, sannan naci abincin da aka kawo min. Saboda gajiya ma ban iya cin komi ba, na koma na baje anan kusa da kayan.

Sai da Yaya ta leko sannan na tashi da kyar, ganin yadda nayi daidai yasa tayi dariya, tace “ki koma kan gado mana ki kwanta, kwanciya a kasa ba dadi, ga sanyin tiles. Ke kuwa yanzu sanyi zai iya cutar daku a halin da kike ciki”, ban fahimci komi take nufi da mu ba, na tashi na koma kan gadon na kwanta dai.

Washegari a gidan Janan na yini. Itama tunda na isa, zancenta daya, na harbu. Duk yadda naso in fahimtar da ita akan ba haka bane, kin yarda tayi.

Tana dariya tace “wai ki hakikance akan abinda baki gwada kin tabbatar da gaske bane ko ba haka bane? Ni naga abinda na gani, ke dai da idanuwanki suka rufe kika kasa ganin komi, sai kije kiyi tayi”.
Na kada mata idanu sama, na dauki kankarar da ta dalilinta ne maganar ciki ta taso, na kai baki ina harararta, “sai kuci gaba da lakaba min abinda bani dashi ai, ku zaku yi disappoiting din kanku!”.
Tace “to ai shikenan, zamu gani”.

Sai da nayi sallar la’asar sannan na mata sallama, muka wuce Abuja.

                         *☆⋆43⋆☆*

Saboda tsabar gajiya washegari ko asibiti kasa zuwa nayi. Yini nayi cur akan gado, ga yunwa da take ta rarakar min ciki amma na kasa samun kuzarin fita. Sai yoghurt da maltina nayi ta durawa a cikin cikina wadanda na jera su a cikin firjin, har sai da naji kamshinsu yana neman sanya ni amai sannan na kyalesu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button