A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Sai can da yamma sannan na iya tashi, wani abin mamaki kuma babu gajiya balle ciwon jiki, sai lokacin nayi wanka, na dauki wata doguwar riga yar Saudiya, ruwan madara na saka a jikina. Nasan lokacin Yaya ya kusa dawowa daga wajen aiki, ranar Raheemah ce take yin girki.
Falon Yaya na wuce, wayar hannuna a hannuna. Sai da yammar nan sannan naga tarin kiran dana rasa da sakonni, tunda na dawo wayar take cikin jaka, ban daga ta ba sai yanzu.

Yaya Bilal naso in fara kira ganin kiranshi har sau uku, da sakonshi da yake tambayar lafiya ban dauki wayarshi ba? Sai dai ina zama, sai gashi ya fado falon. Da alama yau ya tashi da wuri daga wajen aiki.
Na mishi sannu da zuwa, daidai lokacin da Raheemah da Ameerah suka shigo suma kusan a lokaci guda. Ya amsa yana kokarin cire neck tie din shi, “lafiya nayi ta kiran wayarki baki dauka ba?”.
Nace “gajiyar hanya ce ta hana ni ko motsi yau wallahi, sai yanzun nan na gani”.
Yace “ok”, ya shiga daki, Raheemah ta bi bayanshi, Ameerah kuma ta samu waje ta zauna.

Babu wanda yayi magana a cikinmu, ni Janan ma na kira da naga nata missed call din, muka sha hirarmu da ita har sai da Yaya ya fito zai tafi masallaci, sannan muka yi sallama. Nima dakina na wuce da niyar yin sallar na bar su anan.

Sai da naji motsinsu a babban falo sannan na fita nima.
Yaya na zaune akan kujera, su kuma sun sanya shi a tsakiya. Sai naja kujerar dake fuskantarsu na zauna.

Raheemah tana bude kwanon abincin, wani kamshin kifi daya bugo min hanci, ba shiri na ja da baya ina yatsina fuska. Wani irin yawo naji diyan hanjina suna min a cikin cikina.

Kwana biyu na kula yanzu tana kokarin zubawa Yaya abinci da kanta ba kamar farkon dawowarmu ba. Ko kuwa don taga daga ni har Ameerah ba ma barinshi ko ruwa ya zuba da kanshi? Ita dai ta sani.

Sai dana bari duk suka zuba nasu, ina kallo Ameerah tayi wancakali da nata plate din, ta tsoma cokalinta a cikin abincin Yaya. Na jinjina kai kawai tare da jan plate nima na fara zubawa kaina. Macaroni ne jollop, da ya sha kifi da nama sai lemun exotic na abarba da kwakwa, da ruwan gora. Duk yadda nayi ganin cewa na hana warin kifin nan damuna, kasawa nayi, don haka abincin ma kadan na zuba kawai. Idan da ba don yunwar da nake ji bama, babu abinda zai saka ni cin abincin nan. Haka nan dai na cije baki na kai cokalin farko bakina. Tun ma kafin in saka shi a bakin nawa, wani irin amai ya tuko ni kamar me.

Da sauri na ja kujerata baya na tashi cikin sauri na fada bandakin dake nan cikin falo, ina shiga na fara amayar da duk abubuwan dake cikin cikina.
Yaya daya biyo bayana da sauri, ya fado bandakin shima. Shi ya taimaka min na tashi saboda yadda nake jin gabadaya gabban jikina sun kasa motsi ga wani jiri da ciwon kai. Ya taimaka min na wanke bakina, ya gyara wajen dana bata sannan ya tallabo ni muka koma falon. Matan nashi na zaune, suka biyo mu da kallo har ya kwantar dani akan kujera.
Ya juya ya kallesu yace “Raheemah miko min ruwa”.

Bata ce komi ba, ta dauko gorar ruwa daya ta tashi ta kawo mishi. Ya tallabo ni na dan tashi zaune, ya kafa min gorar a baki, dan kadan na sha na koma na kwanta. Ya rufe gorar ya ajiye, ya dafa kaina da tunda muka fito nake dafe dashi.
Murya cike da damuwa yace “me yake damunki ne? Dama baki da lafiya ne?”.

Na girgiza kai a hankali, “a’ah, ciwon kai ne dai nake ji kadan, da alamu na gaji ne da yawa”.

Yace “me zaki ci to, zaki iya cin abincin in kawo miki wani?”.
Gabadaya na rasa kuzarin yin magana, kai kawai na iya girgiza mishi.
Yace “to me kike son ki ci?”.
Nan ma na sake girgiza mishi kai, ya dan yi frowning, “kin san ba zan taba barinki ki kwana da yunwa ba ko baby? Ki fada min abinda kike son ci idan na dafawa ne sai a dafa miki”.

Nayi shiru ina tunanin abinda zam ce mishi amma kuma ji nake kamar duk duniya babu abinda zai iya shiga cikin cikina yanzu. Ya fara jero sunayen abinci kala-kala, har da su Chinese da Italian, daga karshe dai nace mishi salad.

Ya shafa kaina har yanzu damuwar fuskarshi bata bar shi ba, yace “bari yanzu a siyo miki, sannu kinji?”. Na gyada mishi kai, shi kuma ya tashi ya dauki wayarshi. Ban san me yace ba, na dai ji yana maganganu kasa-kasa, yana gamawa ya dawo kusa dani ya zauna. Ba ayi minti talatin ba, aka kawo salad din a cikin take away, na tashi zaune shi kuma ya zauna a kusa dani. Da kanshi ya dinga bani, na kuma samu naci da yawa.

Ina gama ci, na tashi nace mishi zan wuce daki in kwanta, nan na musu sallama, yana biye dani har zuwa dakina. Da kanshi ya taya ni sanya kayan barci sai da yaga na kwanta sannan ya kashe min wutar dakin. Babu jimawa barci ya dauke ni.
Washegari na koma bakin aikina.

*

Kwanana biyu da dawowa, a hankali na fara lura da canje-canjen da jikina yayi. Misalin yadda fatar jikina tayi wani irin smooth da taushin da karya mutum yake yace na mayuka ne, ga wata kasala da nake yawan ji, yawan barci da jin yunwa duk da dai bana wani zabar abinci. Da dai sauran canji da na kasa kawar da kai daga garesu.

Na fara tunano maganganun su Sailuba da Janan, da irin assumption dinsu. Amma na kasa yarda da hakan.

Na fito daga bandaki jikina daure da towel, da kuma dan karami a hannuna ina kafar da lemar jikina. Na tsaya a kusa da doguwar mirror din dake cikin dakin, ina ganin ilahirin jikina tun daga tafin kafata har kaina.

A hankali na kai hannu na shafo shafaffe kuma damammen cikina da yayi kamar ba yanzu na gama dura mishi abinci ba. Saman hancina, kumatuna da kuma kasan habata sun fara fitar da wasu kananun fararen abubuwa, su kuma ba kuraje ba, (blackheads), lokaci zuwa lokaci na kan yi su, amma sai a halin da nake cikin stress, damuwa, ko kuma lokacin sanyi. Sai dai yanzu ba sanyi bane, bana cikin wata damuwa kuma ko stress, saboda haka fitowarsu a fuskata a halin yanzu, abin mamaki ne. Cikin wadannan tunanikan na kammala shiryawa. Na fito da uniform dina da suke a wanke a goge, na saka.

Ina cikin gyara zaman hijabita a jikina, Yaya ya turo kofar dakin ya shigo hannunshi rike da brief case dinshi.
Yace “kin gama shiryawa?”, nace “ehh, nayi zaton har ka tafi ne?”.

Yace “a’ah. Yau direban ba zai shigo da wuri ba, muje in sauke ki ko?”.
Ba musu na dauki jakata na rataya, muka jera ni dashi muka fita. Ya tsaya na rufe kofar dakina, sannan muka wuce. Ina ganin Ameerah tana lekenmu ta tagar dakinta lokacin da muka wuce, Raheemah kuma tana falo a zaune kamar wadda take jiran Yayan.
Da yake yau Ameerah ta fita daga girki, ni kuma na amsa, nasan ba lallai sun hadu ba.

Tana ganin fitowarmu ta tashi tsaye, a tsaitsaye ta amsa gaisuwar dana mata, ta kalleshi, “kasan bikin Haleemo next week ne ko?”.

Ya kalleta cikin nuna alamun rashin damuwa, yace “sai aka yi yaya kuma?”.
Tace “dama ina so ne inje in amso dinkin dana kai mana, daga can kuma zan shiga kasuwa in sayo wasu kayayyaki”.

Ya gyada mata kai, a lokaci daya kuma yana daga kafa ya fara tafiya, “sai kin dawo to!”. Ganin haka nima yasa na bi bayanshi.

Da sauri ta biyo mu, “bani da ko kwandala fa, kuma kudin dinkin da yawa”.

Ya dan dakata, kamar ba zai ce komi ba, kafin yaci gaba da tafiya, “babu cash a hannuna, zan turo miki idan na karasa office”.
Babu godiya kamar wadda ta bashi ajiya, ta juya ta koma ciki, mu kuma muka fita.
Har ya kaini asibiti yanayinshi ba irin wanda ya shigo dashi bane yau da safe duk sai naji na damu. A haka dai ya ajiye ni ya wuce.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button