A ZATO NA COMPLETE

Bayan na tashi daga asibitin, na tsaya a wani babban pharmacy anan cikin asibitin. Nayi zarya a wajen tafi sau ashirin, daga karshe dai na tattaro duk wani kwarin gwiwata na shiga ciki. Na sayi abinda zan saya, sannan na wuce gida.
Ina zuwa ko hutawa ban yi ba, na dora musu abincin rana. Ni ko ci ma banyi ba, kankanar dana siya a kofar asibiti, ita na yini ina sha abuna.
Sai dana gama duk abubuwan da zanyi, sannan na fada bandakina na rufo kofar.
Gabadaya jikina rawa yake yi lokacin dana bare ledar teat strip din dana siya a pharmacy, na sakata cikin kwalbar dana dauki sample din fitsarina, na tsaya cikin rawar jiki ina kallon tsinken kamar ina jiran yayi magana.
Ina tsaye, har na kula da canjin da abin yayi. Na dauko shi tare da dubawa.
Ban san lokacin dana koma jikin bangon da nake tsaye ba na jingina. Na kasa yarda da abinda idanuwana suka gani, da gaske? Ya Allah, ko dai mafarki nake yi?.
Ban san iyaka lokacin dana dauka anan ba, har sai dana ji karan turo kofa an shigo dakin, ina jin Yaya yana kwala min kira, amma na kasa motsawa balle in amsa mishi. Daga karshe dai ya turo kofar bandakin ya leko.
Ganina a haka, ya rikice. Da sauri ya saki kofar ya fado bandakin, ya tallabo ni cike da matsananciyar damuwa, “baby, lafiya, me ya faru ne?”. Ya jero min wadannan tambayoyi.
Amma na kasa motsawa har yanzu. A hankali na daga hannuna da yake rike da tsinken awon, na mika mishi.
Ya amsa, fuskarshi dauke da alamun tambaya da mamaki, “menene wannan kuma?”.
“Positive… positive…”, kadai na dinga fada ina nanatawa kamar wani karatu.
Ina ga a hankali ya fara fahimtar abin, saboda daga baya naga ya kamoni yana jijjiga ni cikin zakuwa, “me kike son fada min ne baby? Are you…??!”, muryarshi ta katse ya kasa cewa komi, yayi gyaran murya tare da sake cewa “…cikina? baby…?”.
A hankali na hau daga mishi kai alamun ehh.
Rasa bakin magana yayi, sai kallona daya tsaya yana yi. Mun jima a haka, kafin daga baya ya daga ni sama cak, sai gani ina shawagi a sama yana juya ni. Ban san lokacin da muka fita daga bandakin ba, sai dana ji ni a tsakiyar gadona.
Ya janyoni cikin jikinshi ya kankame, jikinshi yana masifar rawa kamar ana kada mishi mazari, “baby da gaske? Da gaske kina dauke da cikina? Ya Allah, me zan ce maka ni kam? Ya Allah… Ya Allah…”.
Nayi shiru ina saurarenshi yana sambatun godiya ga Allah ina ta murmushi.
Ya dago yana jero min tambayoyi, “me kike so? Me zaki ci? Kina marmarin wani abu? Ki fada min duk abinda kike so baby kinji?”.
Na girgiza mishi kai, “barci nake ji”.
Da sauri ya hau gyara min wajen kwanciya, ya kwantar dani akan gadon tare da sanya bargo ya rufe ni, “kiyi barcinki kinji? Sannu baby na…”.
Ina yada kai akan filo, barci ya dauke ni.
Washegari wayar Janan ce ta tasheni daga barci, daga nan nasan babu wanda bai ji labarin samuwar cikina ba.
Da alama matan nashi kuma basu sani ba. Idan ma sun sani ni ban ga alama ba. A ranar Raheemah ta tafi wajen bikin Haleemoh, sai tayi kusan sati biyu lokacin an gama bikin sannan zata dawo. Gida ya rage daga ni sai Ameerah da Yaya.
Yadda yake lallashina, yana riritani, yana nan-nan dani kamar wata karamar yarinya, Ameerah da kanta ta cafko da wani abu a kasa, da kanta ranar naji tana tambayarshi lafiyata lau kuwa? Shi kuwa yace mata cikine dani. Tunda muke da matar, sai ranar ne naga bacin ranta. Ranar ko dan murmushin yaken data saba yi, kasawa tayi. Da kyar ya iya kakaro sautin “Allah ya raba lafiya”, ta tashi daga wajen da sauri.
Wata tafiya ta kama Yaya zuwa Niamey, wani bincike da aka tura su wajen aikinshi. Da kyar ya iya tafiya ya barni, a cewarshi sai dai mu tafi tare, ni kuma nace mishi a’ah, da kyar dai ya tafi da har yace ya fasa zuwa sai dai wani daga wajen aikin yaje a madadinshi, na dai samu ya tafi da kyar.
Yana barin gidan, itama Ameerah ta janyo akwati ta bar gidan, daga gani dama jiran ya tafi take yi. Gida ya rage sai ni kadai.
*☆⋆44⋆☆*
Satin Yaya daya da tafiya, sai gashi ya dawo. Babu sanarwa kawai sai ganinshi nayi a cikin gidan.
Lokacin ina kwance ma a falonshi, kallo nake yi da plate cike da dambun nama a gabana ina ci, ban ma san lokacin da barci ya dauke ni ba. Ji nayi kawai ana shafa gefen fuskata a hankali.
Na bude idanuna da suka yi nauyi, na sauke su a kanshi a nutse. Mamaki ya kama ni, a yadda muka rabu dashi a jiya ta waya, sai gobe da safe sannan zai dawo. Cikin mamakin na fara kokarin tashi zaune, yayi sauri ya maida ni na koma na kwanta, “uhm uhm koma barcinki abinki, I’ll join you in a bit”.
Sai lokacin na kula da suits din dake jjikinshi da kuma akwatun kayanshi da yake ajiye a gefe, da alama ko daki bai karasa ba.
Ya tashi ya ciccibi akwatinshi ya shige daki. Bayan tafiyarshi kuma sai na kasa komawa barcin, na tashi zaune da kyar ina hamma da mika. Idanuna suka sauka akan agogo, karfe daya na ranar Laraba. Kamata yayi ace Ameerah ce kuwa da girki ranar tunda ranar daya tafi girki ya fita a hannuna.
Na tashi na zauna akan kujerar tare da daukar filo na rungume naci gaba da cin dambun nama na ina kallo.
Zuwa can sai gashi ya fito sanye da kayan hutu, jar rigar T-shirt mai buttons da bai yi buttoning duka maballan ba, ya bar guda biyu na sama, hakan yasa ake iya hango fara kar din singiletin daya sanya daga ciki. Sai ya sanya car-go pants baki, na kuwa daga baki na bishi da kallo cike da burgeni din da yayi.
Zama yayi a gefena yana dan murmushi, “kada dai ace na tashe ki?”.
Na girgiza mishi kai a hankali, idanuna manne da talabijin inda suke nuna film din ‘Gentleman’, “ko kadan, dama can ba wani barci bane. Ya hanya Yaya?”.
Yace “Alhamdulillahi, mun iso lafiya lau, shine kawai”.
Na dan turo baki gaba, “kuma shine baka fada min zaka zo ba?”.
Ya janyo ni cikin jikinshi yana yar dariya, “kada fa kice zaki fara yi min rigima yanzu. Ganin mun gama muhimman abubuwan da suka kaimu, yasa na baro sauran a baya na taho. Na kasa jira har sai gobe kafin in ganki. Ya baby na, baya takura ki dai ko?”. Na girgiza mishi kai.
Yace “yau baki leka asibiti bane? Naga kamar morning kike yi wannan satin ko?”.
Nayi hamma tare da kara komawa cikin jikinshi na langwabe, shi kuwa ya kara rike ni, nace “sister Hanifa taga ina ta layi saboda barci, shine tace in taho gida kawai zata kula min da nawa aikin”.
Ya shafa sumar kaina, “ta kyauta gaskiya, ki tuna min idan muka hadu da ita nan gaba in mata godiya sosai. Wai ina Ameerah ta shiga ne, ko barci take yi? Naji dama tana cewa kwana biyun nan ta cika yin barci”.
Nayi shiru ina muzurai don ban san me ya kamata in ce mishi ba, bana so yaji mutuwar sarki a bakina. Ganin yadda nayi shiru ina kallonshi, yasa ya fara dube-dube kamar wanda yake neman wani abu.
“me ya faru ne? Ko bata jin dadi ne?”.
Naga dai duk wani boye-boyena babu abinda zai sa ko ya hana, Ameerah dai bata gidan, Yaya kuma gashi nan a gidan, idan ma nace zan kareta zata iya karewa in kwana a ciki, tunda babu ranar dawowarta.
Nace “bata fada maka ranar da zata dawo bane?”, Allah ya gani, banyi don in hada su ba, don dai babu yadda za ayi in kaucewa hakan shi yasa.
Yace “ban gane bata fada min ba, ina ta tafi, kuma yaushe?”.
Na dago na kalleshi, haka kawai naji tausayinshi ya ratsa ni. Ban ga amfani, ko dalilin da zai sa haka kawai mata ta bar gidan aurenta ba tare da ta nemi izini daga mijin aurenta ba, akan wane dalili? Kodayake, rashin tsoron Allah yayi karanci a zukatan mutane a yanzu. Rayuwar auren an maidata kamar wata wasan yara, matan aure basa girmama mazajen aurensu. Gani suke yi kamar yan kananun abubuwa kamar tambayar miji zuwa anguwa wani kankanin abu ne. Bayan babbar magana ce, kuma babbar matsala wadda idan muka yi da wasa, zata iya kaimu wuta. Balle kuma, fita unguwa har ki kwana ki wuni a wani waje can daban? Shi mijinki yana can ya bude baki da hanci, yana tunanin ya baro ki a gida a zaune, cikin tsarewar bangon gidan aurenki, ba tare da yasan abinda yake faruwa ba. Ko tunanin yanayin rashin tsaro da wannan duniyar tamu take ciki bata yi, idan ace wata matsala ta samu, misali hatsari ko kidnapping Allah ya kiyaye, me zata ce mishi; me kuma zata cewa Allah?.