A ZATO NA COMPLETE

Nace “ai kamar tun ranar da ka tafi itama ta tafi, bata dawo ba har yanzu”.
Rubutaccen mamaki ya zanu a fuskar Yaya, ba karami ba kuwa. Bai ce komi ba sai kai da ya girgiza, yace “ok!”. Sai dai daga jin yadda yayi maganar kasan cewa ranshi yayi matukar baci.
Nima ban samu na iya cewa komi ba saboda bani da abin cewar, sai kawai na kara kwanciya a jikinshi. Muka cigaba da kallonmu ni dashi, babu wanda yake iya magana a cikinmu, sai sannu da yake yawan jefo min a duk lokacin da na motsa.
Sai da aka kira sallar La’asar sannan muka tashi, kafin ya fita ya umarceni da in sama mishi abinda zai ci kafin ya dawo. Bayan nayi sallah, na shiga kicin na dafa mishi abinci mai kyau, daya dawo muka ci tare. Shi ya dauko laptop dinshi ya fara aika bayanai akan ayyukan da yaje yi a Niamey, ni kuma na zauna a gefenshi.
Anan ne Maryam ta kira ni daga gida, mun jima muna hira da ita, har su Anty Alawiyya da su Kulsum sai da muka gaisa dasu. Tunda labarin cikin nan ya same su, kusan kullum sai munyi waya dasu, ko su ko Janan. Ummah ma da Yaya kusan kullum muke yin waya dasu, kullum maganarsu daya, yadda zan kula da kaina da dan cikina, abinda ya kamata in ci da wanda bai kamata in ci ba, kulawar da muke samu daga wajensu ni da abinda ke cikin cikina ma kadai ta isheni, balle kuma ta wajen uban gayya, Baban baby na.
Karfe shida ta dan gota na yamma, lokacin da muka ji an shigo cikin falon. Lokacin mun koma kasan carpet din falon, har yanzu Yaya yana fama da rubutu a laptop dinshi, ni kuma nayi matashin kai da cinyarshi. Ayaba ce a gefena ina barewa ina ci, shima idan na ci na kan kai wata bakinshi ya ci.
Ameerah ta shigo da waya sarkale a kunnenta tana amsa kira, hannunta mai rike da wayar rataye da jaka, dayan kuma yana jan karamin trolley.
“… Yanzun nan na shigo gida fa ko daki ban karasa ba. Idan na huta zan kirak…”, ta kasa karasa maganar da zata yi sakamakon ganin Yaya zaune ya zuba mata idanunshi.
Bata san lokacin da wayar hannunta ta zame daga hannun nata ta fadi a tsakiyar dakin ba, tayi sak kamar wadda aka kafe da wani abu a wajen.
Da kyar sautin “baby….!!”, ya fita daga bakinta. Daga ganinta kasan cewa ta rikice, ta kuma tsorata da ganin Yayan a gida.
Yaya yayi zaune very calm and collected, yana kallonta yadda kasan ranshi ba a bace yake ba. Ganin babu wanda yayi yunkurin ce mata kala, yasa ta durkusa ta dauki wayarta data fadi, ta tashi tsaye tana kallonmu fuska dauke da wadataccen murmushi kamar ba ita bace aka kure tayi satar hanya ba. Tace “baby… Banyi zaton cewa yau zaka dawo ba ai, ya hanya? Yaushe ka da…??”.
Yaya yayi saurin katseta ta hanyar cewa, “daga ina kike?”.
Ko kadan bata girgiza da tambayar daya jefo mata ba, tace “kasan cousin dina Mubeenah ko? Kanwar Mommy. To ita ce tazo ganin gida daga Switzerland, na fada maka ai ko?”.
Yaya ya hade fuska iya hadewa, ban taba ganin zallan bacin ranshi irin na yau ba, ko lokacin da muke cikin je-ka-dawo kafin mu shirya kuwa.
Yace “zan kuma iya tuna abinda na fada miki a lokacin, ban yarda ki taka kafa ki bar nan gidan ba, ko ba haka na fada miki ba?”.
Ta wani marairaice fuska kamar karamar yarinya, “amma Baby… Sai dana fada maka fa daddy ne yace inje mu gaisa da ita saboda mun jima bamu hadu ba. Kuma ma, kai da baka gidan, menene a ciki?”.
Ran Yaya ya baci iyaka baci, ya tashi tsaye cike da matsanancin bacin rai, jikinshi har wata rawa yake yi, “akan meye zaki tsallake dokar dana kafa miki kamar wani sa’an wasanki, ko kuma wanda baki dauki maganar shi da mutunci ba, kodayake, dama yaushe kika taba girmama wani abu dana fada miki? Wai saboda Allah, ke nake aure ne ko kuma iyalan gidanku gabadaya?? Kwata-kwata an maida min rayuwar aure wasa, ni da matata, amma ban isa in zauna in gindaya mata sharadi ba tare da an san yadda aka yi, aka yi watsi da lamarin ba? Shin ni din ba mijinki bane? Idan ma baki sani bane, ki san cewa yanzu duk wata hidima da dawainiya da komi naki ya tashi daga hannun iyayenki, ya dawo hannuna. Baki da wani hurumin bin maganar mahaifinki ki tsallake tawa. Amma gabadayanku kun rufe idanunku, kuna abusing kalmar aure, saboda kun dauketa a ba a bakin komi bane ko me? Kin dauka rayuwar auren, abar wasa ce? Rashin sani ne yasa haka ko kuma rashin sanin yakamata??!”.
Ameerah bata iya cewa komi ba saboda yadda taga ran nashi ya baci fiye da tunaninta.
Yaya yaci gaba da cewa, “na gaji da yadda kuke take min rayuwar aure haka nan. Ban isa dake ba, ban isa da komi naki ba. Saboda haka daga yau a gidannan, zaki zaba, umarnina ko kuma na mahaifinki? Idan har kin ce ba zaki bi umarnina ba, to tun kafin tafiya tayi nisa, ki koma inda kika fito. Idan kuma kin shirya yin zaman rayuwar aure kamar yadda yakamata, to daga yau sai yau, ban yarda ki taka kofar gida ba tare da kin nemi izinina ba Ameerah idan kuwa har hakan ta sake faruwa, duk abinda ya biyo baya, ki zargi kanki!. Zabi ya rage naki!”.
Ya hada kan kayanshi ya wuce daki a fusace.
A hankali ta duka ta janyo akwatinta ta shigo cikin falon sosai, na mata sannu da zuwa, bata amsa ba, sai ma la’adar harara da nasha. Taja akwatinta ta wuce dakinta kamar tashin duniya, na bita da kallo cikin tabe baki. Meye laifina anan, ni da bani na kar zomon ba? Na sake tabe wani bakin.
Yaya bai fito ba sai da aka kira sallar magriba.
Kiri-kiri yaki cin abincin data dafa ranar, a gabanta ya kira wata hadaddiyar restaurant ‘cloirassantz’ daya saba yi mana odar abubuwan tande-tande, yayi placing order aka kawo mishi abinci, ya zauna yaci kayanshi ya wuce daki abinshi.
Washegari ina daki ina shirin fita ya leko dakin, na gaida shi. Yace min idan na dawo inyi girki, in kuma cigaba da yi har sai shi da kanshi yace min in ajiye. Ban iya cewa komi ba sai ‘to’, na kula hukuntata yake so yayi tun karfinshi.
Ban sanya bakina cikin fadansu ba, ko tambayarshi dalilinshi na damka min girki gabadaya ban yi ba.
Kwana biyu suna ta fadansu, fadan masoya hutu, ban san ta yadda ta samu ta shawo kanshi ba, naga dai sun koma sun dinke kamar tif da taya, nan ma ban ce komi ba, na damka mata girki taci gaba da yi.
Ya karbe motar hannunta yace ta maidata gida, ya kuma hanata yawan fita gatsar, dokoki sosai ya kafa mata, duk tace taji ta amince.
A haka Raheemah ta dawo muka cigaba da bugawa dai. Ta kawo mana souvenirs na bikin, ga hoton Haleemo nan da Umar ya sha uniform dinsu na sojoji radam a jikin komi, memo ne, jaka ce, calender ce, kai tarkace dai. Lokacin data bani, dariya nayi tare da musu fatan alkhairi na kai daki na ajiye. Ko tayi tsammanin haushi zan ji ko kishi??.
*
Cikin jikina yana ta tasawa cikin koshin lafiya, yanzu yana cikin satikan shi na goma sha daya.
Har yanzu muna cigaba da gwabzawa da matan Yaya, duk da cewa yanzu da Ameerah muke yi. Raheemah sam yanzu ba na ta tata, fada ne, bana biye mata.
Wata tsirfa data dauko ma sabuwa, haka zaka ganta a dakin Yaya ranar girkina tun da safe, ta kuma ci kwalliya ba ta wasa ba. Har magana sai da na yiwa Yaya akan haka, nace ya daina biye mata suna yin haka, suna shiga hakkin mai yin girki.
Amma maimakon yace wani abu, sai yayi dariya, wai “menene abin shiga hakki anan Baby? Mu da babu abinda muke yi sai hira kawai? Idan kika tafi yin girki, kadaici yana damuna, kinga tana taya ni dauke kadaicin”.
Da naga dai bashi da niyar daukar mataki, sai na gyada kai nace “to babu laifi”.