A ZATO NA COMPLETE

Tayi kasa da muryarta sosai, “Momcy, na manta yadda zan sanya wannan maganin ne. Kin san kuma Malam yace idan ya wuce yau ba zai yi amfani ba”.
Na zare idanu sosai, amma sai na kara lafewa ina sauraronta.
Sai da tayi hamma sannan tace “wanne daga ciki? Na turaren ko kuma na ci?”.
Tace “na ci dai, ai na riga nayi na turaren tun yaushe…”, ta ja dan tsaki, “… amma ni har yanzu ban ga yayi wani abu ba, anya kuwa ba asarar kudi kawai muka sake yi ba?”.
Tace “ina, shi mai nema ai baya gajiya. Ba zamu gajiya ba, balle ina da tabbacin wannan din zai yi. Kin san fa aikin malamin nan kamar yankan wuka, kin dai ga irin aikin da yawa Halima. Ke kanki ba da taimakonshi bane kika shigo gidan ba?”.
Tace “haka ne, kawai naga kwata-kwata aikin baya yi ne yan kwanakin nan. Duk inda muka je sai dai suyi ta cinye mana kudi. Shima wanda nake zuba mishi a abinci fa har ya kare, amma kinga har yanzu shiru kamar an shuka dusa. Bai sallameta ba, bai juya mata baya ba kamar yadda suka ce. Ranar nan ma fa har tambayata yayi me yasa abincin yake wani warin magunguna? Nace mishi maggi ne. Kada fa mu je ya cafko mu Momcy”.
Tace “ke ja can matsoraciyar banza da ta wofi!! Dan ubanki ke har kin fara sarewa tun kafin aje ko’ina? To arr dinki, ni cikin yayana babu matsorata wallahi, ki kiyaye ni. Kina ganin idan kika zauna a gidan wannan tsakanin wadannan matan nashi, zaki ganu? Shi komi ba dan hakuri bane? Da sannu, su duka zamu yi waje dasu. Yanzu abinda zamu kokarta muyi shine mu ga cewa mun karkato da hankalinshi kanki tukun. Yanzu kije ki zuba maganin a cikin danyen nama, ya kwana, gobe ki soya shi ki mishi girki yaci, zaki ga abin mamaki. Amma kada ki kuskura ki kara bari inji kalmar karaya ta fita daga bakinki, kina jina?”.
Cikin sanyin jiki tace “ehh Momcy”.
Tace “to madallah, maza je kiyi aikin gabanki”. Ta kashe wayar.
Na dafe kai da baki a lokaci guda. Kaji fa wata irin tabewar basira. Kai Allah dai ya kara rufa mana asiri, ya kuma sa mu dace.
Ban damu da cewa har yanzu tana cikin kicin din ba, na tashi nima na shiga kicin din. Wutar kicin din na kunna haske ya bayyana, daidai lokacin tana maida danyen nama cikin firjin. Da sauri, kuma a tsorace ta maida firjin din ta rufe, ta juyo tana kallona cikin zare idanu. Ban ce mata komi ba, na bude microwave na ciro abincin ciki, na koma kan dinning na zauna na fara ci.
Ta zo ta wuce ni cikin sanyin jiki kamar kazar da kwai ya fashewa a jiki, tana yi tana satar kallona.
Nima a sanyaye na fara cin abincin hankalina ya kasu gida-gida, har na rasa da wanne zan ji. Da alama sai na kara zagewa da addu’a ba akan kaina kadai ba, har shi Yayan.
Ina gama cin abincin, na je na dauke gabadaya naman dake cikin fridge na zubar. Na koma dakin Yaya. Bandaki na shiga na dauro alwala na fito na fuskanci alkibla ina jero nafilfili.
Washegari da safe ba sai aka maimaita yar gidan jiya ba? Na hadawa Yaya abincinshi na kari ya fara ci cikin nutsuwa, ya kai shayin dana hada mishi, kawai naji ya furzar dashi, a dan zafafe yace “meye haka Na’ilah?”.
Daga farko tsananin mamakin ya kirani da Na’ilah ne ya kama ni, kafin mamakin abinda ya faru da shayin ya biyo baya. Bai ma tsaya yi min karin bayani ba, ya tashi ya bar wajen. Ina nan zaune cikin rashin sanin abin yi, sai gashi ya fito dauke da brief case dinshi, da kyar ya iya cewa “sai na dawo”. A Karo na farko, ranar ya fita ba cikin rakiyata ba, kuma cikin rashin dadin rai.
Sai daga baya na fahimci cewa, robar sugar aka juye gabadaya aka zuba gishiri. Wannan karon ma kadan ya hana ni inyi kuka.
Saboda haka da girki ya sake dawowa kaina, na dinga bin kwakkwafi. Idan na shiga kicin, bana lekawa ko nan da can har sai na gama girkina, idan kuma na gama, tunda nasan na Yaya ne ake hari, sai in shige daki dashi in kulle har sai ya dawo. Duk da nasan cewa da gangan ake min haka, amma ban shirya neman kowacece ba, bani kuma da zuciyar ramawa. Nasan cewa dai, rana dubu ta barawo ce, daya kuma ta mai kaya.
*
Yau da yake ba ranar girkina bace, kuma ina off saboda evening duty dana gama, ban fito daga daki ba sai karfe biyu na rana. Yau da su kayan marmari ma na karya. Kwana biyu yanzu mangawaro kawai nake sha kamar babu gobe, kullum sai in sha fiye da guda biyar.
Yanzu ma abinda ya fiddo ni waje kenan, saboda mangwaron dakina ya kare ne. Yaya da zai fita yace za’a kawo wani.
Ina shiga kicin kuwa, na ganshi an kawo shi har kwali guda. Wani irin dadi ya ziyarceni. Na dauki guda biyu manya masu kyau, na wanke su na yanka. Ina cikin yi, Raheemah da take yin girki ranar ta shigo. Tunda abin nan ya faru, kusan sati daya kenan, bata ko yarda mu hada idanu da ita. Ko hira suke yi, idan taga na shigo waje, haka zaka ji tayi shiru ko ta ma tashi ta bar wajen.
Sannu kawai na mata ciki-ciki, na dauki mangwarona na koma daki.
Na zauna na tada mangwaron nan tas, na bi da ruwa mai sanyi.
Komawa nayi na kwanta naci gaba da barcina.
Wajen karfe hudu, wani irin masifaffen ciwon ciki ya tado ni daga barcin da nake yi.
Na tashi na fara murkususu. Tun ina yi akan gado, har na fado kasan carpet. Gabadaya ciwon ya gigitani, ban taba jin azababben ciwo irin wannan ba.
Da kyar na iya lalubo wayata na kira Yaya, yana dauka ya fara tambayar lafiya? Saboda yasan ban cika kiranshi idan ya tafi wajen aiki ba, musamman ma ranar da ba girkina ba. Ban iya mishi magana ba, sai gurnanin ciwo kawai daya dinga fita daga bakina. Nan da nan ya rikice, yace gashi nan zuwa.
Ina jin lema tana fita daga jikina, amma bani da kuzarin daga kai in ga ko menene. Ban ma san lokacin da Yaya ya dawo ba saboda hankalina ya gushe daga jikina.
Lokacin dana dawo cikin hayyacina, tuni cikin jikina ya zube.
Lokacin da wata likita daga cikin likitocin asibitinmu ta isar min da wannan sako, dauka nayi mafarki nake yi.
Sai da naga Yaya ya shigo, jiki babu kuzari, fuska very defeated, kawai na saki kuka ina jan Innalillahi…
Dr. Anita ta matso ta dafa kafadata tana lallashina har na dan nutsu nayi shiru, nasiha ta dinga yi min mai shiga cikin jiki da nuna min hakan ikon Allah ne, shi ya bamu shi dama tun farko, tunda kuma ya dauke kayanshi ba sai muyi hakuri ba. Sai da taga na daina kukan, sannan ta juya wajen Yaya shima ta mishi jaje, sannan ta barmu ni dashi.
Muna hada ido da Yaya, na sake barkewa da wani kukan. Ja na yayi cikin jikinshi kawai yayi yana shafa gadon bayana har sai da nayi mai isata, sannan ya dago kaina. Shi kanshi idanunshi sun kada sunyi jawur kamar wanda zai fashe da kukan. Nasan karfin hali kawai da jarumta irin ta namiji ce yake yi.
Ya taimaka min na tashi zaune saboda jikina babu karfi, likita tace ya bani abu mai ruwa in sha, a bani magani, amma sam na kasa cin komi. Sai da yayi kamar zai min kuka sannan na samu na dan kurbi yoghurt din daya kawo min. Ya bani maganin na sha.
Komawa nayi na kwanta, shi kuma ya zauna a gefena ya kamo hannuwana cikin nashi ya damke, wasu zafafan hawaye suke ta zirya akan kumatuna. Ya sanya hannu yana dauke min hawayen, cikin sanyin da muryarshi tayi, yake bani hakuri, yana kara yi min tuni akan yarda da kaddara.
Da alama maganin da aka bani har da na barci. Saboda ba’a jima ba barci mai nauyi ya daukeni.