A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Ban tashi ba sai washegari da safe. Ina bude ido, naga Janan zaune a gefena. Ban san lokacin da tazo ba, nan na sake bude wani shafin kukan tana aikin lallashi. Daga karshe nayi shiru, ta taimaka min na shiga bandaki nayi wanka. Na fito ta bani abinci na karya, na sha magunguna.
Tace Yaya ya zo da safe, yace zai kirani a waya saboda ana nemanshi a office ne, kai kawai na iya gyada mata.

Wajen karfe goma kuwa ya kira ni, na dauka muka gaisa. Dole na ware muryata sosai saboda kada ya karanci damuwar dake nake ciki. Nasan na kwallafa raina akan cikin jikina, amma Yaya ya fi ni. Tafiyar da yayi zuwa Niamey, haka ya dawo da kayan wasan yara kala-kala. Daki guda ya ware, yanzu ya kusa cika da kayan wasan yara dana sanyawa.
Ya tambayeni saukin jikina, nace mishi naji sauki. Nan muka dan sha hira dashi kafin muka kashe wayoyin da alkawarin zai sake kirana idan aka jima.

Yinin ranar cikin amsar waya da mutane yan dubiya muke, har yanzu na kasa yarda da cewa babu cikin jikina, amma idan na tuno hakan yana daga cikin kaddarar Allah, sai in kwantar da hankalina.
Matan Yaya ma sun leko zuwa rana, da dai-daya ma suka zo. Sai da Ameerah tazo ta tafi sannan Raheemah ta zo.

Zuwa can yamma, na dan warware daga jiki har zuci. Likitar data duba ni jiya, ta shigo ta sake duba jikina. Bayan yan tambayoyi data min na amsa, ta tabbatar min da cewa zuwa nan da kwana biyu ma zasu iya sallamata. Nace mata nagode.

Tace “amma barinki ya bani mamaki Nailah (haka yawancin mutanen asibitin suke furta sunana saboda basu iyawa), last time da kika zo muka duba ki, komi lafiya lau daga ke har dan cikinki, ba kwa fuskantar wata barazana. Kin tabbatar baki ci, ko sha wani abu da zai fitar da cikinki ta karfi ba? Saboda daga yanayin abin kamar da karfi cikin ya fita”.

Na girgiza mata kai a hankali, nace “kawai dai kaddara ce Allah ya aiko”.

Ta girgiza kai cikin nuna fahimta, “haka ne, Allah ya mayar miki da mafi alkhairi. Ki kwantar da hankalinki fa kinji? Kada ki sanyawa kanki damuwa”.
Na sake mata godiya, ta mana sallama ta fita.

Tana fita Janan tayo kaina da tambayoyi, nace “ni fa bana son wani tada rigima da maganganu. Idan ma wani abin ne, Janan ina da shaida ne? Koma menene, mutum ai kanshi ya yiwa. Don Allah kada ki bari ma Yaya yaji wannan maganar, Allah kadai yasan abinda zai yi akai. Ni na barwa Allah komi, na kuma yarda babu abinda yake faruwa face cikin yarda da izininsa. Don haka ki manta da maganar kawai”.

Ta rausayar da kanta gefe guda, “to shikenan ai tunda haka kika ce. Zaki ci abinci?”.
Ta watso min tambayar tana nufar kulolin dake ajiye a wajen wadanda yawanci abokan aikina ne na nan suka kawo min su, nasan duk don ta dauke hankalina daga kan zancen ne. Murmushi kawai nayi na gyada mata kai.

[Hello there! ????].

                         *☆⋆45⋆☆*

Kwana na biyu ina hutawa a gadon asibiti. Bayan an tabbatar da lafiyata da komi, aka sallamomu muka koma gida. A ranar Janan ta koma Kaduna ina ta mata godiya.
Sai dana kara kwanaki uku ina kara hutawa, sannan na koma bakin aikina na kuma karbi girki. Rayuwa ta koma normal, mun maida komai bayanmu mun fuskanci gabanmu.

Zaune muke gabadayanmu a falon Yaya da misalin karfe tara na dare. Yanzu har Raheemah ta kan fito ayi hira da ita, kafin dare yayi kowa ya nemi makwancinsa kuma.
Na fahimci Yaya a mutum mai son karfafa zumunci da son kusanci ga iyalinshi, hakan yana kara min girmanshi da kimarshi da nake gani a cikin idanuna. Duk da cewa ta fanninsu, ba hakan suke so ba.

Na tashi na shiga kicin, fruit salad din dana hada yayi sanyi karara, na dauko forks guda hudu, na koma falon. A tsakiyarmu na ajiyeshi tare da ajiye cokulan masu yatsu, muka fara shan fruits din aka kuma cigaba da hira. Sai dai hirar kamar kowacce tata kawai take yi, idan Yaya yana hira da daya, baka ji biyun sun sanya baki sai dai su kalli TV ko kuma suyi shiru da bakinsu. Duk yadda yaso ya saka mu cikin hirar gabadaya abin gagara yayi, idan ma ya sanya bakin wata a cikin hirar ta danyi magana, sai ita dayar kuma tayi kim da baki, sai ta jira sun gama hirar sannan ta sako wata. Abin gwanin ban dariya, na dai yi ta kokarin makale tawa a ciki.

Duk da cewa a hakan ma ba karamin kokari yayi ba, tun da yanzu har mu kan zauna mu duka a waje daya ba tare da kaji kananan maganganu suna tashi ba. A ganina hakan kamar an fara daukar matakin farko kenan wajen hade kai.
Sai dai, tunda na dawo daga asibiti, wani shiru da matan suka yi su duka, yanzu babu bataccen girki idan nayi, Ameerah ta daina shiga dakin Yaya tunda safe, haka ita kanta Raheemah ta daina wannan yawan mitar tata. Jikina kawai yana bani ba daidai ba. Sai inji kamar shirun nan nasu, ‘silence before the storm’ ne.
Ko kuwa sun fara shiryuwa ne??.

Kadan-kadan Ameerah ta fara yatsina fuska, tun ana yi babu wanda ya kula har Yaya ya lura, ya kalleta cike da alamar tambaya, “lafiya, baki jin dadi ne?”.
Duk sai muka juya hankulanmu kansu.

Ta girgiza kai a hankali, “cikina nake ji yana juyawa… Kamar zanyi amai…”.
Tana rufe baki, ta tashi a sukwane tayi dakin Yaya, mu duka ukun muka tsaya muna kallon-kallo, kafin muka tashi da sauri muka bi bayanta.
Tana cikin bandaki tana ta kakarin amai, Yaya ya matsa da sauri ya tattagota suka dawo dakin, daga shi har mu sannu muke jera mata wanda take amsawa cikin jan numfashi. Muka rankaya muka koma falo muka zauna.

Muna zama ta fara wani kakarin da yatsina fuska, Yaya yace “wai wani abu yana damunki ne?”.
Tana daga baki, sai cewa tayi, “ai ita warin kankana ne yake tada mata hankali”.

Na daga girata sama cikin tsananin mamaki, Raheemah kam sai ta kama baki. Yaya yace in dauke farantin in maida kicin tunda mun gama shan fruits din. Ban ce komi ba na dauke kayan, a raina ina nanata ikon Allah kenan mai rike zariyar wando.

Na koma muka cigaba da hirarmu, har lokacin kwanciya barci yayi duk muka tashi. Na koma dakina nayi shirin barci, na koma dakin Yaya.

Cikin dare kawai sai karan waya muka ji, Ameerah ce wai cikinta ya dameta da ciwo. Nan muka nufi dakinta muka sameta tana ta birgima akan gado. Yaya yace min “ko kina da maganin ciwon ciki ne ki bata ta sha?”.

Nan na koma daki na lalubo maganin boskafone na koma dakin bayan na biya ta kicin na dauko ruwa mara sanyi.
Nan na sameta kwance shame-shame a jikin Yaya. Ban ce musu komi ba, na mika mishi maganin, ya tallafo kanta zai bata maganin, nan tayi fir tace ba zata sha ba.
Yaya ya fara aikin lallashi, amma ta kafe.
Cikin nuna alamun gajiya da halinta yace “kinsan ba neman magani kike yi ba, zaki tado ni da tsakiyar wannan daren, idan ba zaki sha maganin ba zan tafi in kyaleki yanzu wallahi”.
Sannan fa ta karba ta sha. Har wajen karfe hudu na dare muna kanta. Ni naki tafiya daki duk da sai da Yaya yace in tafi, ban san ko ciwon gaske take yi ko na karya ba. Sai da aka fara kiran assalatu sannan barci ya dauketa. Sai lokacin muka koma daki.

Bayan kwana biyu da yin haka, sai gata wai taje likita ya aunata ance tana da ciki. Nan suka hau murnarsu ita da Yaya, na bisu da addu’ar Allah ya raba lafiya. Wani abin mamakin shine, yanayinta sam bai yi kama dana masu ciki ba. Yadda take da, haka take yanzu, babu canjin komi a tattare da ita. Hakan yasa na fara tunanin anya ba cikin karya bane ba kuwa? Sai dai a yadda Yaya yake ta doki da rawar jiki akan cikin wannan, nasan ko giyar wake na sha ba zan fito in ce mishi ga abinda ake ciki ba. Don haka na kawo idanu na zuba musu, koma dai menene, nasan it’s only a matter of time, zamu ga ciki dai ya bayyana ai ko?.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button