A ZATO NA COMPLETE

A bakin kofar falon muka tsaya na karbi ledojin hannun Balarabe saboda nan ne iyakacinsu da gidan, na tura kai na shiga falo. Karfe hudu na rana ta gota da kadan. Allah-Allah nake in dangana da dakina in cire uniform din jikina, in watsa ruwa ko naji sanyi a jikina saboda wani azababben zafi da ake zubawa yau.
Zaune a falo, Yaya ne da Raheemah sunyi jigum-jigum, sai wata Hajara cousin din Ameerah da take yawan zuwa gidan. Nayi sallama, suka amsa min cikin sanyin jiki, sai naji jikina ya kara yin sanyi, nace musu “lafiya kuwa?”.
Hajara ce kawai ta iya amsa min, tace “Ameerah ce ta fadi a bandaki dazu, ana tunanin kamar ta samu miscarriage!”.
Sai naji jikina ya kara yin sanyi, nace “Subhanallahi, ya jikin nata? Sun tafi asibiti ne?”.
Tace “a’ah, ai family doctor dinmu tazo, yanzu haka tana ciki tana dubata”.
A raina naji abin banbarakwai. Nayi tunanin idan aka samu akasi irin haka, asibiti ake garzayawa? Amma sai na kame bakina nayi shiru. Na shiga daki na canza kayan jikina, na koma falo nabi layin jiran fitowar likita.
Banyi mintuna goma da zama ba, sai ga likitar ta fito. Duk muka tashi tsaye. A shekarance za’a iya cewa zata yi shekaru arba’in da wani abu, ta kalli yadda muka yi cirko-cirko cikin jimami, tace “sai dai hakuri, amma cikin ya zube saboda tsabar buguwar da tayi”.
Hajara ta hau sallallami da salati cikin kuka, shi kuwa Yaya shiru yayi kawai yana kallon likitar, sai dai daga ganin yadda idanunshi suka kada suka yi ja, kasan cewa zancen ya shige shi sosai. Ban san a wani shafi nake ba, na bakinciki, jimami ko tausayi?.
Raheemah ta kama kugu ta fada karkada jiki cikin tsiwa, “hmm! Allah sarkin baiwa! Wadda aka bullo da ita kuma kenan? Ku dai kuka sani, nan gaba ma zuwa za ayi ace ta haihu an sace mata dan!”.
Cikin nuna alamun gajiya Yaya yace “Raheemah…!”. Amma bai karasa fada ba, kamar wadda maganar ta kakarewa. Da mai hankali ce, ko kuma da masifa bata rufe mata idanu ba da ta fahimci warning din da yake tattare a cikin muryarshi.
Maimakon tayi shiru sai taci gaba, “ai wallahi kaima tabewar basira ce ta same ka. Wadda aka tabbatarwa da cewa ba zata taba haihuwa ba, ita ce zata zo rana daya tace wai tana da ciki? Yo cikin abin banza ne ko kuwa a ruwa ake shan shi? Aikin banza, an rasa karyar da za ayi sai ta ciki. Ai wallahi dama jiran ranar da za’a haife muke yi mu ga uban abinda za’a kawo ace an haifa, sai kuma aka kare da bari. An kira likitar bogi ana wani kukan karya saboda an maida mu sakarkaru, to mun san komi ai wallah kuma idanunmu ba a rufe suke ba!”.
Aikuwa sai Hajara ta shaka, nan da nan ta manta da kuka da salatin da take yi, tace “su waye kike cewa masu yin karyar ciki?”.
Tace “ba ga ku nan ba! Makaryatan banza dana wofi!!”.
Hajara kuwa tace “ke in ana zancen ciki ma har kin isa kiyi magana? Ke da ko batan wata ma baki taba yi ba? Idan fitsari kayan banza ne kaza ma tayi mana mu gani?!”.
Wai! Ai sai Raheemah ta hau ihu, tana yi har tana hadawa da buga kafa a kasa, “ai wallahi na godewa Allah tunda abin bai kaini ga yin karyar ciki ba, kuma lafiyata lau, ina kuma da amfani ba ci nake ina kasayarwa ba!!”.
Hajara tace “idan abin haka ne, me yasa ke baki taba yin cikin ba?”.
Nan da nan falo ya rikice da hayaniya kamar zasu ba hammata iska, sai da Yaya ya tsawatar musu sannan da kyar. Raheemah ta wuce dakinta tana cigaba da zage-zagen.
Ya juya ya ba likitar hakuri, tayi murmushi tace babu komi ai. Ya tambayeta ko nawa ne kudin aikin da tayi? Tace ai kudinta suna cikin albashinta, Hajara ta taka mata ta mana sallama ta tafi.
Suna fita Yaya yayi dakin Ameerah, na bi bayanshi. Tana kwance akan gado tana barci. Idan ba fada maka aka yi ba, ba zaka taba cewa mai jinya ce ba wadda tayi bari. Babu paleness alamun rashin jini, babu alamar cuta ko kadan a tattare da ita. Ni dai na tabe baki a cikin raina, sai me idan tayi karyar ciki? Wannan ai matsalarta ce ba tawa ba. Matsalata ita ce matsalar dake tsakanina da mijina a yanzu.
Na samu kujera na zauna anan, babu mai uhm ko uhm uhm a cikinmu. Na kalli yadda ya dafe kai a zaune, har yanzu kayan aikine a jikinshi, bana tunanin ko sallar la’asar ma yayi. Na danyi gyaran murya nace “Yaya ko zaka je ka canza kayan jikinka ne? Zan kula da ita kafin ka dawo. Kayi sallah ma kuwa?”.
Ya daga kai a hankali ya kalleni kafin ya girgiza kai. Tausayinshi ya cika min zuciya. Nayi takaicin cewa yau ba ranar girkina bace, da na faranta mishi rai, ta yadda zai manta da kowa da komi.
Nace “kaje kayi to, sai ka dawo”.
Babu musu ya tashi ya bar dakin. Ni kuma naci gaba da zama anan har Hajara ta shigo itama.
Zuwa can Ameerah din ta tashi daga barci. Muka matsa muna mata sannu, Hajara ta taimaka mata ta tashi zaune. Na mata ya jiki, ta amsa tana wani yamutsa fuska. Ban kara ce mata komi ba, sai wani kallon dana jefa mata wanda ya sanya ta shiga taitayinta a take, ita tasan ni ba sakara bace, kamar yadda nasan itama ba sakarar bace, ta fahimci ma’anar kallon da nake wurga mata sarai. Nan na barsu na wuce dakina.
Washegari kuwa haka aka yi ta zuwa dubiya da jaje. Janan da Yaya ma sun zo. Bayan sun dubata, muka nutse daki ni da Janan. Tunda tazo take bi na da kallo cikin alamun tambaya, nasan hakan baya rasa nasaba da yadda nayi wuri-wuri ne, na canza kama. Muna shiga daki kuwa ta fara watso min tambayar lafiya? Nayi rashin lafiya ne?.
Na zauna a gefen gado ina kallonta, “lafiyata lau mana, me kika gani ne?”.
Tace “ban gane ba? Baki ga irin ramar da kika yi bane? Kin kuma kara baki”.
Na daga kafadata sama kawai, “halin rayuwa kenan dama, yau dadi gobe madaci”.
Itama ta zauna a gefen gadon tare da dafa kafadata, tace “to Allah ya kyauta. Amma don Allah ki kwantar da hankalinki. Kada ki saka wata damuwa da bata kai ta kawo ba a cikin ranki ki janyowa kanki wata cutar. Komi zai zo ya wuce”. Na gyada mata kai a hankali.
Sanin ba zata ji komi daga bakina ba, yasa ta kawo min hirar wajen da take yin internship. Duk mun kusa gamawa, nan da watannin da basu fi uku ba zamu gama, mu zama cikakkun nurses.
Daga karshe ma dai muka fita ni da ita. A motarta wata madaidaiciyar SUV Lexus UX ruwan toka, da mijinta ya sai mata. Da yake ta riga ta iya motarta tun kafin tayi aure, ita take kai kanta ko’ina, yanzu ma ita ta kawo su da Yaya.
Gidan Yaya Hafiz muka je, matarshi Hauwa, ta karbemu da far’arta. ‘Ya’yansu maza biyu, mace daya suka zagaye mu suna mana sannu da zuwa. Da yake lokuta da dama suna leko mu, amma zumuncinsu yafi karfi da Ameerah, amma muna gaisuwar mutunci da ita.
Bayan mun dan yi kamar mintuna ashirin haka, muka musu sallama muka tafi. Muka nutsa cikin garin Abuja, shiga gidan wannan, fita daga wancan, yawancinsu duk gidajen kawayen Janan ne, wasu kuma gidajen yan’uwansu ne. Sai da Yaya ta kirata akan tana jiranta, sannan fa muka juya.
Bayan sun tafi na koma daki na zauna ina jiran a kira sallar magriba Nasan yau idan na kwanta sai nayi ciwon jiki saboda yawace-yawacen da muka sha.
⋆⋆
Kwana biyu, komi ya natsa, komi ya koma yadda yake, mun ci gaba da gudanar da rayuwarmu kamar da. Ameerah ma ta warware har ta karbi girki abinta.
Ranar Alhamis, ranar satina daya da zuwa Suleja. Abubuwa da dama sun ragu, ina kuma ganin canji sosai a tattare da Yaya, ya sauko sosai. Tunda yanzu mu kan zauna muyi hira cikin raha, muci abinci tare, duk da lokaci zuwa lokaci ya kan dan janye jikinshi, but am not complaining.