A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Aikin rana nayi yau, kafin in tafi nayi miya na ajiye a dakina, don haka ina dawowa na dafa cous-cous muka ci a matsayin abincin dare. Yau ko hirar da ake yi ban tsaya ba, ina maida kayan kicin, dakina na wuce nayi shirin kwanciya barci, na musu sallama na fada dakin Yaya na kwanta.

Ina kwanciya barci ya dauke ni, yau wuni muka yi akan kafafunmu, saboda haka jin jikina nake kamar wadda aka wa dukan tsiya. Ban damu da jiran Yaya ba, kamar yadda nace, mun dan koma normal ne, amma ba duka ba. Duk da hakan yana damuna, amma ban bari ya dameni sosai ba.

A cikin barcin naji shigowar shi dakin, da alama yau hirar bata yi tsayi ba, tunda ko cikakken minti goma banyi da kwanciya ba. Ina jin motsin shi a cikin dakin, da alama shirin kwanciya barci yake yi, amma saboda tsabar gajiya na kasa bude idanuna.

A hankali naji an zauna a gefen gadon, tattausan hannu ya shafo gashin kaina zuwa gefen kumatuna. Wata siririyar murya, very husky and soothing, take kiran sunana, amma daga can nesa nake jiyo muryar kamar a cikin mafarki.
“Na’ilah… Baby…!”.

“uhm?”, na amsa. Amma na kasa daga idanuna.
“Baby!!”. Aka sake kirana, wannan karon desperately.

Don haka nayi kokari na bude idanuna da kyar, kuma a hankali.

Ban san me zan ce ba, saboda na kasa banbance tsakanin mafarki da farke. Shin wannan ma daya daga cikin mafarkan dana saba yi ne? Ko kuwa da gaske ne?!.

Ba kamar sauran mafarke-mafarken dana saba yi ba, kamar su dinne dai, amma ya banbanta. A maimakon silhouette din mutum dana saba gani, wannan karon sai nayi ido-da-ido da Yaya. Wanda ya saki wani irin tattausan murmushi lokacin da yaga na bude idanuna mun hada ido dashi.
Nayi scrunching eyebrows dina in confusion, mafarki nake yi?.

Ya kara shafa gefen fuskata, “I love you, baby na!”.

Scratch that! Be it mafarki ko rashin mafarki, it doesn’t matter. What matters is that, Yaya ne, mijina, nake gani zaune a gabana, yana furta min abinda na jima banji daga gareshi ba. Sanyin daya mamaye kirjina a wannan lokacin, Allah ne kadai yasan iyakarshi.

Sai dai barcin dake cikin idanuna ya rinjayeni, da kyar nake damben iya daga idanuna da suke komawa suna likewa kamar ana jona su da maganadisu.
Na dafa hannunshi dake kan kumatuna, “Yaya..!”. Na samu na furta hakan a hankali, kafin barci ya sake daukata. Hakan bai hana ni jin warmness din da lebbanshi suka haifar akan goshina ba. Ban kuma daure murmushin daya subuce min ba duk da barcin daya ci karfina.

Kiran sallar farko a cikin kunnena. Na bude idanuna a nutse, a hankali kuma abubuwan da suka faru a daren jiya suka fara dawo min. Tunanina daya a lokacin, shin mafarki ne nayi?.
Sai dai daga jin dumin jikin daya kamo ni ya rukunkunme ni ta baya kamar wanda yake tsoron a dauke mishi ni, ina tantamar idan mafarki ne.

Murmushi ya fara kokarin subuce min, wani irin sanyi, aminci da salama dana manta rabon da inji kwatan-kwacinsu suka dinga kwararawa suna shiga cikin zuciyata. Marata cike take tam da fitsari, dalilin daya tasheni daga barci ma kenan, amma na kasa zame jikina daga nashi. Sai ma kara lafewa da nayi a kirjinshi ina jin bugun zuciyarshi.
Mun jima a haka, har zuwa lokacin da ya farka. Sannan na daga kai, tare da kokarin zame jikina daga nashi wanda sai a lokacin ne ya sake ni.

Sauka nayi daga kan gadon na shiga bandakin. Bayan na gama abinda zan yi, alwala na dauro sannan na fito. Ina fita, shima ya shiga bandakin.
Na gyara jikina tare da fara nafila kafin lokacin sallah yayi. Ina jin lokacin da Yaya ya fito shima, ya shirya ya fita zuwa masallaci.

Ina cikin nade abin da nayi sallar naji ya dawo. Ina jin lokacin daya maida kofar ya rufe. Nayi shiru a tsaye ina jiran in ga abinda zai yi ba tare dana juya ba, saboda ban san abinda zai faru ba. Kawai sai ji nayi an rungumoni ta baya. Ya lalubi kunnena yace “good morning, baby”.

Naji kunya ta rufe ni, nace “ina kwana Yaya?”.
Ya nutsa kanshi gefen wuyana yana humming, “lafiya lau baby na, kinyi barci lafiya?”.

Na gyada mishi kai tare da juyawa ina kallonshi cikin murmushi, “sosai ma!”.

Bai ce komi ba, sai kara ja na cikin jikinshi da yayi, ya kara saka kanshi a wuyana yana shakar numfashi. Abinda yake matukar kauna kenan. Mun jima a hakan, kafin ya dago ni yana kallona, “God, how I miss you!!”.

Na daga hannu na shafo gefen fuskarshi, “I miss you too, Yaya na!”.

Daga nan kuma abinda ya faru sirrinmu ne. Sai can, rana ta fito sosai sannan na raka shi ya tafi bayan na soya mishi kwai ya ci da shayi da biredi.

Ina dawowa daga raka shi din da nayi, naci karo da Raheemah a kofar kicin ta baya ta coge tana watsa min kallon tara saura. Na gaida ta fuska babu yabo babu fallasa. Ta kare min kallo tun daga sama har kasa, taja tsaki, “jarababbun banza da wofi!”. Ta fadi hakan cike da tsana da dacin rai.

Ban ce mata komi ba, ban ma ji komi a cikin raina ba, farincikin da zuciyata take ciki a lokacin ya wuce tunanin mai tunani, babu abinda zan fari ya wargaza min wannan jindadin. Don haka na hasketa da murmushin tura haushi kawai na kara gaba.

Ina shiga kicin ta sake biyoni, “kina nufin yau da abinda zamu karya kenan?”. Ta fada tana nuna flask din shayi da biredin da na ajiye akan dinning table, shekeke kamar wasu kayan kashi.
Nace “ehh mana, me suka yi ne?”.
Kafin tace wani abu, Ameerah ta fado kicin din sanye da rigar barci ta leshi wadda ta tsaya mata a gwiwa. Ta kalli yadda muka yi cirko-cirko damu kamar wasu zakaru, ta dauke kanta ta hau dage-dagen drawers. Ni ce na fara gaida ta, sai data dauki gwangwanin white oats, sannan ta amsa.
Nima na dauki yoghurt daga cikin fridge na koma dakina. Bashin barcin da na ci na biya kafin lokacin tafiya aiki yayi.


Shikenan, muka shirya abinmu. Rayuwa taci gaba da tafiya, akwai lokuta da dama da sabani zai shiga tsakaninmu, hakan bai taba affecting rayuwar aurenmu ba. Bamu fari sabani ya kaimu ga bacin ran da zai hana mu jindadin rayuwar aurenmu ba.

A hankali azumi yana ta matsowa. Ranar nan kwatsam sai ga Yaya da albishirin zamu je umra dashi. Wayyo, murna har sai da nayi hawayen dadi. Na fara kiraye-kirayen wayar yan’uwa da abokanan arziki ina albishir.

Washegari sai rigima ta balle, a cewar Raheemah Yaya yayi rashin adalci. Saboda wancan karon ma da zai tafi tare da Ameerah suka tafi wanda hakan yake nufin wannan turn dinta ne kenan.
Yaya yace “wannan nima haka naji shi daga sama yadda kika ji shi kema, bani da alhakin kudin jirginta. Illa iyaka mun tafi tare, mun kuma dawo tare”.

Da taji haka kuma sai tayi shiru ta fara kokarin nade tabarmar kunya da hauka. Wai “ai duk da hakan dai, ai..”, Ta hau kame-kame. Yaya kuwa yayi banza da ita, ya juya yana kallon Ameerah yana gaya mata tayi list din abubuwan da zasu bukata kafin tafiyarmu, tace to.

*

Anyi haka da kwana biyu, sai ga Ameerah da nata biridin itama. Ranar assabar ce, lokacin saura sati biyu mu tafi.
Na tura Yaya falonshi yana karatun jarida, ni kuma na hau gyara mishi daki. Daga bandaki na fara, bayan na wanke shi tas na kyalkyale shi yana ta sheki da tashin kamshi, sai na koma bedroom.
Ban san lokacin da Ameerah ta shigo ba watakila lokacin ina bandaki. Ina jiyo sautin muryoyinsu daga nan.

Wai itama Daddynta ya biya mata umrah, da alamu kenan tare zamu tafi da ita. Tana fadar hakan tana yar dariya. Sai dai daga jin yadda muryar Yaya tayi a lokacin, abin bai bashi dariya ba.
Kai tsaye yace babu inda zata je.
Da taga tayi roko da magiya ya kafe, sai tace to zata bi yan gidansu kawai su tafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button