A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Yace “ba ina nufin ba zaki bimu bane, ina nufin babu inda zaki je, kina gida”.
Murya na nuna bacin rai tace “kana nufin ayi asarar kudin da aka biya ne ko me?”.
Yace “lokacin da aka biya kudin ai ba’a nemi shawarata ba, ko an nema? Kada ki manta kuma abinda ya dace ayi kenan tun daga farko. Ta inda ake hawa kuwa ta nan ake sauka”.

Tayi shiru, can kuma tace “amma kasan duk shekara muna zuwa Hajji da umara ko?”.
Yace “ba a taba tambayata ba, ko an taba? Nayi iyaka karar da zanyi, na kuma gaji. Saboda haka babu inda zaki je wannan karon, idan kuma zaki yi musu da nine, to mu zuba don Allah!”.
Sai ta kame bakinta ta kulle. Na girgiza kai ina yin dan murmushi. Dama masu iya magana sun ce idan tura ta kai bango…!

Har na gama ayyukana ban sake jin duriyarsu ba, sai sautin karar talabijin ko kuma muryar Yaya idan an kira shi a waya.
Zuwa can na fito daga dakin hannu rike da basket da na matse bed sheets da kananun kayan Yaya dana wanke na wuce su a falon a zaune sunyi jugum-jugum.
Baya na fita na shanya kayan, na koma gidan ta kofar waje.
A kofar shiga falon muka yi karo da wata mata, muka kalli juna ni da ita, kamar na santa amma kuma na rasa a ina na santa. Na dakata ta shigo gidan kafin na rufa mata baya, sai da muka shiga falo naga tayi hanyar dakin Raheemah. Ni kuma na koma falon Yaya.

Lokacin dora girkin rana yayi na fita kicin na hau dafe-dafe, yam porridge nayi, nayi dambun cous-cous, da lemun cocktail.
Ina gama shirya abincin akan dinning Raheemah ta fito ta kwashi abincin da yawa ta koma dakinta, ban mata magana ba saboda bakuwar da nasan tayi.

Dakina na koma, nayi wanka tare da sanya kananun kaya, rigar blouse da dogon wando, na dora hular beanie na sanya silifas mai taushi na fita zuwa falon Yaya.
Ranar haka muka yini, Yaya bai leka ko nan da can ba. Sai can bayan sallar la’asar sannan ya fita.
Sai da yammar ne na fahimci cewa wannan bakuwar ba kowa bace face Haleemo. Na bita da kallo cike da tsananin mamaki, ta rame, tayi baki, duk wannan kwalisar babu ita, baka taba cewa itace Halimon nan. Kayan jikinta ma daga ganinsu sun ga jiya sun ga yau.
Ganin babu wadda tayi min magana a cikinsu, yasa nima na juya musu baya, naci gaba da yanka kabeji da nake yi a kicin. Amma kuma zuciyata cike take da tunanin abinda ya faru da ita, a iyaka sanina da ita Umar ta aura, to me ya faru? Ko sun rabu ne?.

Bayan na gama girkin, kasancewar lokaci ya kure tunda har an gama sallar magriba lokacin, yasa kayan ma a kan dinning na barsu gabadaya, na wuce dakina.
Wanka na fara yi, sai da nayi sallah sannan na zauna zaman shafa mai da hoda. Ina cikin shafar ne naji hayaniya ta fara tashi, na dan dakata, jin abin ya ki ci ya ki cinyewa yasa na dauki doguwar hijabi na zura na fita falo domin in ga abinda yake faruwa.

Raheemah na jingine da bangon falon, Yaya da Ameerah kuma na tsaye a tsakiyar falon sunyi cirko-cirko suna raba idanu kamar wasu zakaru.

                         *☆⋆47⋆☆*

Kallo daya zaka yiwa yanayin da mutanen falon suke ciki, zaka fahimci cewa babu lafiya.

Ameerah na tsaye nesa kadan da Yaya, in banda rawa, babu abinda ilahirin jikinta yake yi. A tsorace take sosai.
Shikuwa Yaya ya tsaya jimke da hannu, sai dana kare mishi kallo sosai sannan na fahimci cewa wata yar karamar farar takarda ce jimke a hannun nashi, wadda ya kama ya rukunkume har knuckles dinshi sai da suka yi fari, a gefe guda kuma jikinshi yana rawa cikin bacin rai.
Raheemah kam ta coge daurin dankwalin nan nata a tsakiyar ka kamar yadda ta saba, da alama itama hayaniyar ce ta fiddota zuwa cikin falon.

Hankalin Yaya gabadaya yana kan Ameerah, kallon da yake watsa mata kadai ya isa yasa duk girman kai da ji da kai na mutum ya saddakar masa ko da bai yi niyya ba kuwa. Ni kaina da nake gefe sai dana ji gabobin jikina sunyi sanyi. Ban taba ganin wannan side din na Yaya ba. Da alamu ma sam bai san da wanzuwarmu a falon ba, idan ma ya sani to yayi kokari wajen nuna cewa wanzuwar tamu anan bata shalle shi ba.

Ya nuna mata hannunshi da yake rike da farar takardar nan yana nuna mata, cikin wata irin murya da ta sanya ni na kara kallonshi da kyau domin in tabbatar da cewa da gaske shi dinne dai, he sounds deadly. Calm, but deadly. Kamar wani sabon mutum da ban taba gani ba, haka ya juye ya koma a lokacin.
Yace “care to explain, ko menene wannan kike kokarin zuba min a cikin abincina?”. Jin abinda yace yasa na zare ido ina kallonsu, a lokaci daya kuma ina kara matsawa kusa dasu.

Ameerah ta dan ja baya da sauri, tsoron dake shimfide akan fuskarta da baka taba rabata da kwalliya, ya bayyana zane baro-baro, instead, shi ya zame mata kwalliyar yau.
Tace “don Allah kayi hakuri. Wallah na tuba, don Allah!”.

Sai dai bai jira ta gama magiyar da take yi ba, ya daka wata irin gigitacciyar tsawa, “Don’t you dare Ameerah! Tambayarki nayi, damn your sorrys don ba ita nake bida ba. Ki fada min, meye hadinki da shinkafar bera na tsinceta a hannunki kina kokarin sakata cikin abincin da zan ci?!”.

Naji ana min wata irin kururuwa a cikin kunne, kaina yana juyawa kamar ana katantanwa dani, kafin wani irin duka a tsakiyar ka ya ziyarce ni kamar ana buga min guduma a ka. Ala dole na lalubi kujerar dake kusa dani na zauna babu shiri saboda rawar da kafafuna suka dauki yi.

Yanzu kam hawaye ne suke ta zarya akan kumatunta, daya bayan daya suna sintiri babu kakkautawa.

Yaya ya kura mata ido, “shikenan? Kaunar da kike ikirarin kina yi min kenan? Soyayyar kenan? At the end of the day kiyi sanadin raina?”.

Kai ta hau girgizawa, “ba haka bane, wallah banyi da niyar cutar da kai ba, ka yarda dani. Sharrin shaidan ne!”.

Yace “kada ki maida ni sakarai mana! Da idanuna na ganki kina zuba abinnan fa. Ko kuwa kina nufin ki ce sharri na miki, ko kuma idanuna ne basu gani daidai ba?”
Tayi shiru kanta a kasa, sai kai data girgiza kawai.

Yace “kina fa bata mana lokaci, ki fada min dalilin ki, ko kuwa kina so ne kice min gishiri ne wannan a hannuna?”.

Ta daga baki da kyar tace “akwai antidote dinta, da kaci zan baka yadda zaka amayar da gubar da kaci. Wallahi ba zan taba yin abinda zai cutar da kai ba, na rantse da Allah!”.

Sai dai ko kadan rantsuwar da take ja bata dada shi da kasa ba. Instead, sai kallonta daya tsaya yana yi. Babu mamaki tunani da lissafin gidan kula da masu tabin kwalwa mafi kusa yake so ya lalubo.
Da kyar ya iya kakaro sautin, “me yasa?”, daga can kasan makoshinshi.
Bata amsa ba sai daya kara jefa mata tambayar cikin daka tsawar da tafi ta dazu gigitarwa.

Ta ja baya da sauri, “munyi zaton idan ka ci abincin zaka zargi ita ta zuba maka, sai ka sallameta!”.

Na tsayin lokaci, duniyata sai ta tsaya cak. Bansan lokacin da hawaye suka fara zarya suna gangarowa kan kumatuna ba.
Wannan shine karshen kiyayya da wani mahaluki zai taba nuna maka a cikin rayuwa, shin ta tsani ganina har haka ne da abin zai kai ga laka min sharrin kisa? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!!.
Yanzu da Yaya bai shigo ba akan lokaci ya sameta cikin aikata wannan aika-aika ba, mai zai faru? Da haka zan kare rayuwata da laifin attempted kisa, haka kawai ban san hawa ba ban san sauka ba. Da haka rayuwata zata kare, ina tsanar kaina da tuhumar ta yaya hakan ta faru? Yaya da yan’uwanshi da suka zama nawa yan uwan nima suna tsanata?
Me na yiwa wannan matar ne da zan cancanci haka daga gareta?.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button