A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Yaya bai ce komi ba sai pacing daya hau yi kamar mai fareti, cikinmu babu wanda yayi gigin yin ko motsi, sai ni da lokaci zuwa lokaci zan ja majina ko in share hawayen fuskata.
Ya dawo ya tsaya a gabanta, “what were you thinking you silly woman?”, ya furta with venom a cikin muryarshi. Kafin ya juya ya cigaba da zagayen da yake.

Falon ya dauki shiru kamar babu wasu halittu da suke numfashi a ciki.

Yace “ban san ko daga ina matsalar nan take ba, amma wannan ba hujja bace. Me kike tunani, kin tsani ganinta ne har haka ko me? Hasbunallahu wa ni’imal wakil!”.
Da alamu ya. kasa iya wrapping kanshi akan wannan matsalar, nima hakan take a wajena.

Yace “kwanaki munyi ta cin karo da matsalar yawan gishiri yaji, tsami, da sauransu a duk ranakun da Na’ilah tayi girki, it was so suspicious I can’t help but wonder, kina da hannu a haka?”.

Ta dago rinannun idanunta da suka rine suka yi jawur saboda tsabar kuka, suka yi clashing da nashi rinannun da tsananin bacin rai, shock da tu’ajjibi suka haifar mishi. “Bab…”, ta daga baki zata fara magana yayi gaggawar katseta, “cut it! Tambayarki nayi don haka amsa zaki bani ehh ko a’ah?”.
Tayi kasa da kanta a sanyaye, “kayi hakuri”.

Ya rumtse idanunshi yana girgiza kanshi kamar yana shaking wani abu daga ciki, “cikin da kika yi b’ari fa kwanan nan?”.
Nan ma wani shirun ya ziyarce shi kafin bada hakuri ya biyo baya.

Shirun daya biyo bayan nan was deafening.
Magana daya Yaya ya iya yi a wannan lokacin, “kin cuce ni Ameerah!”. Wadda daga jin yadda muryarshi ta lullube da zallan bakin ciki da sararwa, daga gani babu tambaya abin data aikata ba karamin girgiza shi yayi ba. Sai dai ni kaina abin ya girgiza ni, sosai ba kadan ba, wa ma zai taba tsammanin haka daga gareta? Da iliminta, da wayonta da komi. Rashin dabara ce ko kuwa tsananin jarumta?.

Daga lokacin da Yaya ya yanke shawara, na fahimci abinda yake shirin aikatawa, niyyarshi a bayyane take, idanunshi sun rufe da takaicin abinda tayi.

“That’s it Ameerah… Kije na…”

Ban san lokaci ko dalilin daya sanya ni mikewa tsaye da sauri ba ina mai ambatar sunanshi, dalilin daya sanya shi dakatawa kenan, ya tsaya yana kallona cikin nuna alamun tambaya.
Nace “Yaya, kada ka aikata abu cikin fushi kazo daga baya kana dana sani, don Allah ka fara nutsuwa tukun”.

Ya kalleni, ya juya ya kara kallonta, ya daga baki kamar zai yi magana, ko kasa yin maganar ma yayi? Kawai juyawa yayi ya fita daga cikin falon da sauri.

Ameerah tayi tsaye a nan inda ya barta, kusan minti daya, kafin ta lallaba ta fada cikin dakinta. Na koma cikin kujerar dana tashi na sake zama. Ba ni na aikata abin ba, amma har yanzu ilahirin jikina rawa kawai yake yi. Ita Raheemah na tsaye a inda take, bata da niyar motsawa. Allah kadai yasan iya lokacin da muka dauka a haka, bayan rawar da jikina yake yi, wani irin sanyi jikin nawa ya dauka ta yadda ko yatsar hannuna kasa motsawa nayi.

Zuwa can sai muka ji karar bude kofa, muna daga kai sai muka ga Ameerah ta dora gyale a kafada, ta ratayo jaka a daya kafadar, makullin motarta a hannu. Babu wanda ta kalla a cikinmu bare muyi tunanin samun karin bayanin inda ta nufa, ta kara gaba. Muma babu wanda yayi gigin tararta bare ya mata magana. Tana fita Raheemah ta juya ta koma dakinta.
Na ci gaba da zama a falon ba ko motsi, ina kallon waje daya kawai; inda Ameerah take tsaye yan mintuna da suka wuce.

Shiru Yaya zai dawo yanzu, amma babu alamun shi. Ba karamin mamaki nayi ba lokacin dana daga kai na kalli agogo naga goma saura. Sai a lokacin ne nayi kokari na koma dakina ina hada hanya. Sallar isha’i na fara yi. Ko bayan na gama sallar, zama nayi akan abin sallar ina kara neman tsarin Allah daga sharrin zafin kishi, kishi wanda zai iya sanya ni aikata mummunan abu ko kwatankwacin wanda Ameerah ta kwatanta yi yau.
Wani irin kishi ne wannan? Wane irin so ne da zai sanyaka aikata abu kamar sanya guba, da sunan son yin framing din wani, kawai don ya bar maka gida? Anya mata zamu so ganin haske a cikin rayuwarmu kuwa?.

Abin bai taba zuwa kaina ba a cikin rayuwata sai yanzu. Nasan nayi kishi, na kuma san na tsani kishiya, sai dai ko da wasa, ko a cikin mafarki ban taba tunanin zan iya aikata abu irin wannan ba. Sai dai dana zauna na kara yin tunani, sai naga ai tun daga farkon fari, abinda ya sanya ni kin kishiyar kenan. Tsoron juyewa in zama abinda ba ni bace yasa, tsoron kishi ya sanya ni aikata abinda zai zo ya zame min abin nadama nake yi, ina tsoron aikata ire-iren wadannan abubuwan ne.
Na kara rokon Allah akan ya kiyaye zuciyoyinmu daga sharrin sake-saken shaidan, da bin shawarar mugayen kawaye, har ma da yan’uwa.

Sai wajen karfe sha daya sannan Yaya ya dawo gidan, lokacin gidan yayi shiru, ko karar tv baka ji a lokacin balle na mutane, har lokacin kuma ina zaune anan inda nake.
Kirana yayi a waya yace in same shi a falonshi. Na tashi na fita, yana zaune akan kujera da ledoji a gabanshi. Sai lokacin na tuna ban dauke kayan abincin ba ma. Ya miko min nawa, buyin kuma yace in mika musu, da alamu bai san Ameerah ta bar gidan ba.
Dana fada mishi Ameerah bata gidan, bai ce komi ba, kai kawai ya gyada tare da tashi ya fada dakinshi.

Na kwashi ledojin na tsaya ta kofar dakin Raheemah na buga mata kofa, ta leko na bata. Bata ce komi ba ta amsa ta maida kofar ta rufe. Sauran kuwa sai kicin na kaisu na ajiye don babu abinda zai iya shiga cikina a lokacin. Na kwashe kayan nan gabadaya na zubar da komi, har lokacin ganin komi nake yi kamar a mafarki, na kasa yarda ya faru.

Sai wajen karfe goma sha biyu nayi sallama dakin Yaya. Yana kwance akan gado, amma ba barci yake yi ba. Na zauna a gefen gadon ina kallonshi, bai yi ko motsi ba.
Zuwa can nace mishi “ba zaka ci abincin bane? Ko zan sama maka wani abu ne?”.
Ya girgiza kai. Sai ban takura shi ba, na tashi na kashe wutar dakin na koma na kwanta.

Nasan yana bukatar lokaci kafin ya samu komi ya zauna mishi a kai. Ko ni kaina abin ya kasa zaunar min, balle shi, da suka kwashe lokuta masu tsayi da ita, to think that zata iya betraying dinshi ta haka, abu ne mai wahala. It must be a big blow. Daga ni har shi babu wanda ya tankawa wani, muna ta sake-sake. Ranar kam barci sai barawo.

*

Washegari karan wayar Yaya ne ya tashemu daga barcin da muka koma bayan sallar asuba. Kaina har juyawa yake yi saboda tsabar ciwo da rashin barci.
Sai da tayi kara sau kusan uku babu kakkautawa, a raina har ina mitar wane mai gajen hakuri ne wannan da bai san ya kira sau daya ya hakura ba? Karfe bakwai da rabi ma bata karasa yi ba lokacin.
Sai da kira na uku na katse, yana katsewa kuwa na hudu ya sake shigowa. Sannan Yaya ya kai hannu ya dauka.

Murya shake da barci ya fara da yin sallama, sai dai da alama mai kiran wayar bai damu da sallamar tashi ba, ya tare shi da “Me Ameerah ta maka ka turota gida tun da sassafe?”. Da alama Babanta ne.
Kasancewar a kusa dani yake, ina jin maganar da ake yi a daya bangaren.

Tashi zaune yayi yana gaida shi, wannan karon ma bai amsa ba, ya kara maimaita mishi tambayar daya mishi. Tashi yayi cimak ya fita daga dakin, na bishi da kallo.
Sai can kusan bayan minti sha biyar, sannan ya dawo dakin. Ya zauna a kan sofa tare da dafe kanshi cikin hannuwanshi. Ganin haka yasa na tashi zaune a tsakiyar gadon.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button