Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

inaso inyi muku wani dan sanarwa plss…wata tamin dm jiya waita biya kudi bansata a group ba kuma nidai baki ta turawa kudinta ba…you people should take note plss…Vip groups dina guda biyu ne kawai daga Dr.Bobby VIPs(a) sai (b) duk wani group apart from wnn ba nawa bane…and ku dinga kula ta wnn number dake kasa kadai zaku sameni kuma dashi zanyi adding dinku a group so dan Allah a kiyaye????????

Masu bukatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank.. Sai a tura evidence of payment through 07063800556.

Rano✨

????Dr.BOBBY????

By Aysha Rano✨

Wattpad@aysharano22

06

Suna zaune Bobby ya shigo rikeda waya a hannunshi kai tsaye ya karaso ciki tareda mikama Aunty Sumy wayan yace”Its your call”…ba musu tasa hannu ta amsa wayan tareda karawa kunnenta tayi sallama…a daya bangaren Hafsa tace”wa’alaiki salam Maman Miemie..inata kiran wayanki no answer shine nace bari inyi trying na Bobby in gani sai gashi kuma ya shiga..Ilham ce ta dameni wai tanason mgn daku”..Aunty Sumy ta dan saki murmushi tace”oh Hafsa wai kece?..dama kinada Number Bobby knn?..”Hafsa tace”bani dashi wlh Ilham din ce ta bani wai tunda naki baki dauka shi a kirashi..gata kuyi mgn”..daga haka ta mikama ilham dake zaune kusada ita wayan…yarinyan da bazata haura 8 to 9 years ba ta amsa wayan full of happines tace”Auntyyy”..aunty sumy ta saki daria jin yanda taja sunan nata tace”na’am ‘yar gidan aunty ya kike?..”tace”am fine aunty just missing you..i want to come back home”..aunty sumy tace”hope dai ba rigima kikema aunty hafsa ba koh?..”tace”bana rigima aunty kullum sai mun fita yawo..yau ma saida aka kaimu shopping dasu fadeel”..aunty sumy tace”inyee ‘yan gidan aunty hafsa..ilham banda fitina kinji?..kuma banda kiriniya banda sa aunty hafsa magana”…daria ta saki sosai kaman wata babba tace”aunty i want to speak to everyone please..where is my Uncle Bobby?..”Aunty sumy tayi putting nata on speaker snn tace”your uncle bobby is here”..cikin excitement ilham tace”my uncle bobby”..yace”yes my mummy how are you?..”tace”am fine uncle bobby ya aiki?..”yace”aiki fine ilham gobe zaki dawo ba?..”tace”yes..kasan me na siyo muku daxu da mukaje shopping?..”yace”sai kin fada mummy”..suna jin yanda ta danyi kasa da murya snn tace”na siyo maka cheesy na siyoma uncle sab sweet na siyoma yaya chocolate snn na siyoma Mummy da aunty biscuits”..dan bata rai Bobby yayi yace” seriously ilham?..of all abubuwan dake wajen ki rasa abunda zaki siyomin sai cheesy?..”daria ta saki sosai tace”to ba kace min kana son cheesy ba..shknn zan sake maka wani yanxu ka bama Mummy da uncle sab muyi mgn”..bai sake mgn ba ya mikama Mummy wayan..nan ma hira suka sha sosai sai kace wata babba snn sab ya karba shima aka sha hiran dashi…miemie ce karshe aka kai mata wayan har daki nan ma suka dora daga inda suka tsaya…Bobby na duban Mummy in a serious tone yace”Mummy nidai kada a sake bari wani daga cikin mutanen nan yazo yace zai dauki yaran nan bana so wlh..after duk abubuwan da suka yi mana yanxub zasu ringa wani zagayowa suna daukan yara sbd mu yadda dasu?..”girgiza kai Mummy tace”kaidai ka fiya riko wlh Bobby..baka manta abu komai qanqantarshi…abun daya faru ya riga ya faru saidai a kiyaye gaba”..aunty sumy tace”kuma Mummy duk abubuwan da suka faru babu ruwan hafsa a ciki..lokacin ma tana england komai ya faru so bazan iya hanata ba muddin ta nuna tanason daukansu koba komai qanwar mahaifinsu ce”..wani kallo Bobby yayi mata yace”sbd tana qanwar mahaifinsu bashi zai daman zuwa koda yaushe tace zata daukesu ba..idan abun da gaske ne meyasa shi baban nasu ya kasa nemansu duk tsayin wadan nan shekarun sai ita?..”dafe goshi kawai Mummy tayi dan tasan kome zaa fada bazai yadda ba tunda ya riga ya dauki zafi haka…itama aunty sumy sanin halinshi yasa taja bakinta ta tsuke tunda it’s of no use trying to explain things to him bazai taba fahimta ba..ya mike zai koma flat dinshi Mummy ta kira sunanshi…ba musu ya dawo ya zauna yana fuskantarta…itama tana dubanshi tace”wane magana kukayi da Nuru dazu kace bazaka iyaba?..”da sauri ya kalli Nur da yayi wani kasa da kai sai kace mutumin kirki…wato ma karanshi yazo ya kawowa Mummy sbd yasan ita kadai zata iya mishi dole koh…rai a dan bace Mummy tace”bada Bobby nake mgn bane?..”a hankali yace”Mummy lecturing fa yakeso inje inyi..sbd Allah Mummy ta ina zan wani fara shiga class ince zanyi lecture bayan ba tabayi nayi ba..idan tsakani da Allah ne shi meya hana bazai je ya koya musu da kanshi ba”..yana rufe baki Nur yace”amma kasan da field dina ne ba abunda zaisa ma in tambayeka sbd nasan 6atamun lokaci zakayi..kaine gynaecologist dan haka kai ya kamata ka koya musu ba ni ba”…wani irin daci yaji yana taso mishi tun daga throat dinshi zuwa bakinshi..gaba daya sai ya zama speechless a wurin..nan take Mummy tace yaje ya taimaka musu koda na one or two days ne…as usual ya amsa mata da toh snn ya mike zuwa flat dinshi…Nur ya bishi da kallo yana kunshe daria…sallama yayi dasu Mummy snn ya mike zuwa flat din Bobby ya sameshi kwance kan three seater a parlor idanunshi lumshe yayi pillow da hannayenshi…murmushi ya saki tareda sunkuyawa saitin kunnenshi yace”this is your punishment for making Lamido cry”…Bobby da yaji mgnr kaman daga sama baisan lokacinda ya mike zaune da sauri yana kallonshi ba…mamaki ne karara a fuskanshi jin abunda yace…shi kuwa Nur juyawa yayi ya fita daga parlon yana daria kasa kasa yasan yanxu komai taurin kanshi dole yayi abunda yakeso tunda Mummy tasa baki…Bobby kam sbd tsabar takaici baisan time daya dunkule hannunshi tareda naushin kujeran da yake kai ba yana fadin”Fuck you Nur”.

Har washegari Saturday ranshi bai dena 6aci kan abunda Nur yayi mishi ba..neman hanyan da zai rama kawai yake amma ya rasa…mikewa yayi daga karshe ya bude wata kofa ta cikin parlonshi sai gashi wajen wani tafkeken swimming pool daga gefenshi kuma gymnasium dinshi ne daya cikashi taf da kayan motsa jiki…kai tsaye gym din ya nufa dan a al’adanshi every Saturday and Sunday sai yayi training kafin yayi komai dan haka yana shiga ya fara training dinshi…ya 6ata lokaci sosai yanayi dan bai baro gym din ba sai da ya hada gumi sharkaf snn ya bude fridge dake ciki ya dauki chilled water ya bude yasha snn ya fito daga gym din yana cigaba da sipping a hankali…direct bedroom dinshi ya wuce bai kobi takan wayanshi da yaga yana haske ba ya fada bathroom…wanka yayi a tsanake snn ya fito yana goge jiki da towel..ya isa gaban mirror yayo shafe shafenshi snn ya shiga closet dinshi ya sako kaya ya fito snn ya isa ga wayanshi da har yanxu bai dene haske ba alamun ana kira knn…missed calls ya gani har 8 biyu na wata Nurse dake Hospital dinshi,biyu na Nuru sai ragowan hudun kuma gaba daya na Rayhan ne…baibi ta kan natan ba ya fara kiran Nurse din..bayan sun gaisa tace”Sir dama da akwai emergency ne kuma Dr Isaac baya nan”..yace”doc Vivian fa?..”tace “itama bata nan Sir”.. kmr bazaiyi mgn sai daga baya kuma yace”alright i will be coming”.. ta amsa da” ohk sir”..snn ta kashe wayan…suna gamawa ya shiga kiran Nur shima bai dade yana ringing ba yayi picking yana fadin”Bob ina ka shiga naketa kira baka picking?..”ba tareda ya bashi amsan tambayan ba yace”what’s the call for?..”da sauri Nur yace”wlh yanxun ake kirana daga Hostel wai wuta tayi spark a wani apartment kuma baa san me yayi causing ba shine naga ya kamata muje mu duba to make sure ba wani babban matsala bane”..shiru Bobby yayi yana sararonshi har ya gama snn yace”yanxun Hospital zanje munada emergency sadai in na gama da can in shigo”..da sauri Nur yace”No problem kana gamawan ka shigo i’ll wait for you”..bai sake cewa komai ba ya kashe wayan…karasawa gaban mirror yayi ya sake feshe jikinshi da turaruka snn ya dauki dayan phone dinshi ya fita daga dakin…kai tsaye parlon Mummy ya shiga bai sameta ciki ba dan haka ya wuce bedroom…tana zaune kan sallaya sanye da hijab a jikinta tana azhkar ya shigo…ya nemi wuri ya zauna saida ta gama azhkar din ta juyo tana kallonshi tace”Bobby”..yace”Mummy ina kwana”..tace”lafia lau..in zakaje haka da sassafe?..”yace”Hospital zanje wa there is emergency..daga can kuma zan shiga college amma ba jimawa zanyi ba”..Mummy ta mike daga inda tace”to muje kayi breakfast “..tana rufe baki yace” Mummy am ok plss..bana jin yunwa”..zaunawa tayi kusa dashi tareda kamo hannunshi a hankali tace”wai sbd maganan jiya ne kaketa 6acin rai haka?..”ya dan turo bakinshi yace”Mummy nifa ba ta6a lecturing nayi ba kin sani..kawai sa inje in wani ce su zauna zanyi musu lectures “..murmushi Mummy ta saki tareda gyara zama tace” ko da baka ta6ayi ba am ???? sure you can do it..besides taimakawa zakayi Bobby dududu baifi kuyi na two or three days ba zaa samu wani..ko kana ganin as the proprietor bazaka iya shiga class ka koyar dasu ba?..”da sauri ya girgiza mata kai yace”that’s not what i mean”..tace”to ka kwantar da hankalinka nasan you can do it..and believe me zaka kara qima a idonsu idan sukaga har ka shiga class dinsu da kanka ka koyar dasu so relax”kasa ce mata komai yayi sai dan murmushi daya saki…murmushin itama tayi masa tareda mikewa ta kama hannunshi suka fita zuwa dinning…da kanta tayi serving dinshi baiyi musu ba ya shiga cin abincin…jin shiru da yayi gidan yace”wai duk ba wanda ya tashi?..”Mummy tace”kasan weekend ai dama ba tashi da wuri suke ba..kowa yana ramuwar bacci”…gyada kanshi yayi yace”amma shi Sab ramuwar baccin uban me yake shida ba fita ko ina yake ba?..wai yaushe ne ma zasuyi resuming school?..”tace”nan da two weeks ina tunanin”..yace”Allh ya kaimu..gara ya koma ko don sbd mu huta da rigimarsu da Miemie..kullum cikin cin zalinta yake”harara Mummy ta maka mashi kafin tace”bayanta kake goyo sbd ita ‘yarka ce koh?.”ya dan saki murmushi yace”aah Mummy gaskia dai nake fada”..tace”to rike gaskiyan naka baa son ji dan bazan bari ka dorama d’ana laifi ba”…murmushi kawai ya sakeyi baice komai ba…saida ya gama cin abincin ya mike Mummy ta rakashi har centarl parlor tana mishi addu’a..yayi mata side hug tareda fadin”Ameen Mummyna..bari inga aunty Sumy kafin na fita”…gyada mishi kai kawai tayi snn ta juya ta koma ciki shi kuma ya nufi flat din yayar tashi…Miemie ce kadai kwance a palor tana kallon wani Series ya shigo..ta mike zaune da sauri tana gaisheshi yace”lafia..bata tashi bane?..”tace”ta tashi tun dazu tana daki”..bai sake mgn ba ya nufi bedroom dinta..zaune ya sameta a kan gado tayi tagumi tareda zubama wayanta dake rike a hannunta ido sai kace zata gano wani abu a jiki…ya karasa ya zauna kusada ita yana kallon wayan nata snn ya kalleta yace”Aunty Sumy lafia kuwa?..”firgigit ta dago tana kallonshi dan batasan ya shigo ba…ta boye wayan hannunta da sauri tana kakalo murmushi tace”yaushe ka shigo?..”maimakon ya amsa sai cewa yayi”lafia wai?..meya faru naga kin zubama waya ido haka?..did somebody called?..” girgiza kai ta shiga yi da sauri tace”b..ba wanda ya kirani”…bai sake cewa komai ba yakai hannu ya amsa wayan daga hannunta..direct call log ya shiga aikuwa yaci karo da wata international number..yayi tsai yana karema number kallo nan take kuma ya gane number England ce…ya dago yana kallonta fuskanshi har ya sauya sbd 6acin rai yace”why did he called?..”murya a sanyaye tace”don’t know..maybe sbd kids dinshi”..bata rufe baki ba cikin tsananin 6acin rai yace”but how dare he called you?..a ina ma ya samu numberki koda yake nasan qanwarshi ce zata bashi..wnn shine dalilinda yasa nace maku bana son mu’amala da mutanen nn..idan ba munafurci ba all these years meyasa bai ta6a kira ya tambayi kids din nashi ba sai yanxu?..after all what he’s done to us har yanada guts din dazai daga waya ya kiraki?..is he Maddd?..”shiru kawai Aunty Sumy tayi tana kallon yanda ya rufeta da masifa as if shine yayanta..tasan duk wnn abun da yake yanayi ne akan gaskiyarshi and bazata ta6a ganin laifinshi ba..ita kanta kusan mutuwar tsaye tayi da taji voice dinshi ta kuma tabbatar da cewa Ismail nefa da gaske ya kirata after 5 long years…to me zai fada mata?..me xai fada wanda bai fada mata shi a lokacinda zasu rabu ba?…a hankali tace”ka kwantar da hankalinka plss”..bai bari ta karasa ba yace”i will have to deal with him myself”..bata ce komai ba tana gani yayi blocking number snn ya mika mata yace”he might use another number to call..yana kira ki fadamin”..a hankali ta gyada mishi kai shi kuma ya mike ya fita sbd 6acin rai ko mgnr daya kawoshi bai fada mata ba…sauke ajiyar zuicya tayi bayan ya fita ta koma ta kwanta kan gado tana sake sake..ita kanta tasan idan yaji anyi blocking dinshi zaiyi using wani number ya kira..idan ya kira din kuma batasan me zata fada masa ba as gabaki daya kanta a daure yake yanxun..ga kuma Bobby da tasan muddin ya samu labarin ya sake kira din shima ba karamin rikici zaayi dashi ba..she knows how stubborn he can be and ko kadan bata blaming dinshi because duk abunda yakeyi yanayi ne sbd su..tasan yanda yakejin ciwon abubuwan da suka faru a baya shiyasa har yanxun ya kasa mancewa…yanada son ‘yan uwanshi sosai shiyasa duk wani abu daya shafesu yake bashi muhimmanci…ta lumshe idonta ta bude data tuna yanda yake dawainiya dasu Miemie tamkar shi ya haifesu..bama su kadai ba hatta ita kanta Bobby shine komai nata a yanxu..tun daga kan Mummy,Sab,Miemie da Ilham zuwa ita kanta shine ya zama tamkar mahaifi a garesu…duk tsawon shekarun nan bai ta6a bari sunyi missing wani abu ba ya zama gatansu sosai…kusan duk neman kudin da yakeyi a kansu yake karewa tunda shine komai nasu…kuma da yake Allah ba azzalumin sarki bane sai yake buda mishi a harkokinshi sosai kuma mishi albarka business dinshi har ya kawo level din da yake a yanxu…tayi nisa cikin tunani har batasan time din da ta fara hawaye ba..tausaya ma kansu takeyi yanda basu da kowa sai junansu a yanxu sai few daga familyn Mummy da suka rage..yanda familyn dad dinsu dana baban yaranta sukayi abandoning dinsu kawai sbd kasancewar Mummy ba bahaushiya ba…yanda sukayita truggling su kadai har Allah yasa suka yanxu…zuwa yanxu kuka takeyi sosai shiyasa bata cika son tana tunawa da past dinsu ba domin yin hakan yana dawo mata da baya gaba ne..gashi duk yanda takai da kokarin dakatar da kanta abun ya gagareta haka taci kukanta sosai ta godema Allah har 6arawon bacci ya lalla6o yayi gaba da ita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button