Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Washegari ya gama shirya kanshi cikin suit as always ya nufi parlon Mummy don yin breakfast saidai ga mamakinshi Miemie kadai ya samu zaune a dinning tana pressing phone dinta…sanye take cikin uniform dinta complete da alama ta gama shirin tafiya school…tun kafin ya karasa dinning din data hangoshi cikin igbo tace”Uncle Bobby Iboola chi”(Uncle Bobby good morning)…yace”kedu ka odi”(how are you)..tace”adimm ma”(i am fine)…yana gyada kai yace”where is everyone?..”tace”Aunty dai ta shiga kitchen yanxu…Mummy da Uncle Sab kuma basu fito ba”..baice komai ba ya juya ya kama hanyan dakin Mummy…zaune ya sameta gefen gado waya kare kunnenta..karasawa ciki yayi ya zauna tareda kama hannunta har ta kammala wayan snn yace”Iboola chi Mummy”…Mummy ta dan kirkiri murmushi tana shafa uban gashin kanshi da yasha gyara tace”iboola chi..how was your night”…yace”fine Mummy”…tace”yau ka kusa makara”…yace”wlh Mummy bacci ne ya daukeni..kuma baki tasheni ba”…murmushi ta kara saki before tace”ai ba aikina bane tashinka a bacci Bobby…aure ya kamata kayi kawai”…ya bata rai yana turo lips dinshi yace”Mummy stop it plss”..ture kanshi tayi daga jikinta tace”i will not stop…haka nan kake tunanin zakayita min zaune a gida without getting married?..you better wake up cox you are dreaming”…sake bata rai yayi yana squeezing face dinshi kaman zaisa kuka yace” Mummy please!”…daria ya ba Mummy sosai ganin yanda yake bubbuga legs dinshi…gaskian Sumayya da take cewa ko Sabeer bai kai Bobby shagwaba ba…saida ta gama dariyan snn ta dan daidaita face dinta tace”da gaske so nake kayi aure Bobby…i want to see your kids running all around this house before i die..i really want to see that”…shiru Bobby yayi yana sauraronta bai san me ya kamata yace ba…sam baison promising nata abunda yasan bazai iya ba…ba wai aure ne baiso ba aah dalili guda daya ne yake ganin zai mishi katanga da yin aure har abada…wnn dalilin kuma shine dangin mahaifinshi…yasan definitely duk ya dauko aure dole familyn uba sune suke taka rawan gani…shi kuma a yanxu bashida makiya da suka wuce familyn dad dinsu..he hates them to the extent that duk wani bafulatani a duniya yakejin ya tsaneshi especially those from Gombe sbd munanan abubuwa da suka aikata musu shi da Mum dinshi da kuma siblings dinshi…wnn dalilin yasa ya yanke ma kanshi hukuncin indai saida dangin mahaifinshi zaa bashi aure to ya gwammaci bazaiyi aure ba har ya koma ga mahaliccinshi…wnn shine dalilinda duk yanmatan dake rushing dinshi baya kulasu cox he will never get married…Aunty Sumayya ce ta shigo dakin tana sanye cikin dogon riga na wani blue lace tayi daurin dankwalinta das da alama ta gama shirin office itama..kyakyawa ce sosai gata da wani irin haske mai daukan ido dukda ba kama sukeyi da Bobby sosai ba kana ganinta zaka gane thesame blood ke running a veins dinsu…a fuska idan ka kalleta bazaka ce ta haifi Miemie ba sbd kyawun jikinta sak na Mummyn su ne…itama a ido ba kowa ke yadda ta haifesu ba kuma har yanxun jikinta nada kyau kaman bata fara tsufa ba…ta karaso ciki tana dan hararanshi tace”Mummy Allah ki dena bari yana kwanta miki a jiki haka…qatoto dashi instead of yaje yayi aure shine zaizo yanama mutane shagwaba like a small baby”…da sauri ya dago da kanshi yana kallon Mummy jin again Aunty Sumy na mgnr aure..smiling yaga tanayi sai ya juya ga aunty sumy itama yaga haka kawai sai yace”hada baki kukayi koh?..”Mummy ta dan dungure mishi kai tace”ba wani hadin baki gaskia ne kawai..kuma idan bakayi wasa ba da kaina zan samo matar da zan aura maka”..Bobby ya wani kwabe fuska kaman zaisa kuka aunty sumy na daria…Mummy kuma mikewa tayi zata fita daga dakin tace”oya ku fito ayi breakfast”..duk cikinsu ba wanda yace komai har ta fita daga dakin…shima Bobby ya mike hannayenshi zube cikin pockets dinshi ya saki wani smile da kana gani zaka san na tsokana ne kafin yace”Aunty Sumy don’t worry dama da akwai wani doctor a Hospital dina da yaketa min nacin yana sonki..ina ganin i will just have to talk to him indai da gaske yakeyi kawai ya fito ni zan bashi aurenki”…tun kafin ya karasa mgnr Aunty Sumy ta kai masa rankwashi a kai tana daria…shima yana dariyan suka fita daga dakin.
Jennifer cook dinsu na gama jere abinci kan dinning Miemie ta mike tareda fara serving…saida ta zubama kowa sai ga Sab ya shigo yana ta yatsine fuska…kai tsaye kujeran dake kusada Mummy ya zauna bayan ya matsar da kujeran kusada nata sosai kawai ya dora kanshi shoulder dinta yana dan yatsine fuska yace”Mummy am sick”…a hankali Mummy ke shafa kanshi tace”meke damun dan autana?..”fuska a kwabe kaman zaisa kuka yace”headache ne Mummy..jiya ko bacci ban samu nayi ba sosai”..dago kanshi Mummy tayi tareda kai hannu tana feeling temperature dinshi tace”eyya sorry love.. yanxu ka samu kaci wani abu sai Bobby ya dubamin kai kafin ya fita”..ba musu Sab ya gyada mata kai ita kuma ta janyo plate ta fara serving nashi…Bobby da tun dazun yake kallonshi yana hararanshi yace”yanxu headache din kakema wnn abun ko Sab?..only headache kakema wnn kwararaton”…langabar da kai Sabeer yayi without saying anything… Aunty Sumy na smiling tace”kai da kake fake auta ma kayi shagwa6a bare shi da yake authentic auta”…harara kawai Bobby ya watsa mata bai sake cewa komai ba…kowa ya maida hankali kan abincin da yakeci…suna dab da gamawa Aunty Sumy tace”umhum Bobby mgnr interview da na fada maka this coming monday zaayi inshaAllah..hope you’ll come over?..”girgiza kai yayi yace”nima i have alot on my table so kuje kuyi interview dinku Allah ya bada sa’a”..tun kafin ya rufe baki ta sake cewa”hope bada gaske kake ba?..why zakace baka zuwa a matsayinka na proprietor?..”shima tana rufe baki yace”Aunty you are the MD zaa iyayin komai a gabanki ba sai dole naje ba..a kyaleni ma inji da aiyukan Hospital dana sauran colleges din”…Mummy dake sauraronsu tace”wich interview are you talking about?..”da sauri Aunty Sumy tace”Mummy interview da nace maki zamuyi na new teachers da zamu dauka…primary section muna buqatan Islamic and Basic Science teachers…secondary section kuma English and Geography..dan Allah Mummy talk to him kada yace bazaiyi attending ba please..zuwan nashi is very important besides ba dadewa zaayi anayi ba”…juyawa Mummy tayi tana dubanshi tace”ya kamata kaje Bobby..i see nothing wrong with that”…kasa cewa komai yayi sai kai kawai daya daga mata…tunda Mummy tasa baki kuma ai mgn ya kare..itama Aunty Sumy sanin hakan ne yasa tayi involving Mummyn a mgnr sbd tasan bazai taba tsallake umarninta ba…a iya saninta da Bobby abu daya ne yake jayayya da Mummy shine idan tayi mgnr familyn dad dinsu wnn kam ko mgnr baya bari yayi nisa yake stopping nashi sbd bayason yakai limit dinda zata umarceshi da yaje garesu shi kuma ya watsa mata kasa a ido…yau shekara biyar knn da rasuwar mahaifinsu kuma tun daga ranar babu wani cikinsu daya sake yin koda hanyan Gombe idan ka cire Sabeer dake Police Academy Wudil…alqawari ne ya daukan ma kanshi babushi babu zuwa Gombe har abada..haka ma Mummy da siblings dinshi duk babu mai zuwa…ko Wudil din ma da Sab keyi watarana sai yaji kaman ya cireshi sbd bai son yin hanyan Gombe at all…ba don bai son katse mishi karatunshi da yayi nisa ba da babu abinda zai hanashi cireshi daga makarantan.
Suna gama breakfast kowa ya tashi Miemie da Aunty Sumy mota daya suka shigo zuwa school shi kuma Bobby saida ya fara duba Sab kmr yanda Mummy tace snn ya shiga nashi motan shima suka wuce College. Mummy da Sab kuma suna gida kasancewar shi Sab din yana hutun makaranta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button