Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

A hankali ya shigo parlon yana tafiya a hankali kaman mara lafia hannunshi rikeda briefcase dinshi sai dayan kuma rikeda suit dinshi…kallo daya zakayi mashi ka gane bashida lafia sbd dan karen raman da yayi kaman wanda yayi wata a kwance…ya kara wani irin haske da idan ba saninshi kayi ha u will think ko bleaching ya fara…Miemie da Sab ne kadai zaune a parlon suna labari kaman basune ke fada kaman suna ganin hanjin juna ba…he is so lost in thought that har ya kama hanyan Flat dinshi bai lira dasu a parlon ba…Sabeer da bai dade da dawowa ba ya dan daga muryanshi da igbo yace”uncle Bobby sannu da zuwa”..dakatawa yayi tareda juyawa a hankali yana kallonshi yace”yaushe ka dawo?..”Sab yace”ban dade da shigowa ba..ya aiki?..”a takaice yace dashi”fine”..snn ya juya yacigaba da tafiyarshi walking slowly..dagashi har Miemie dankallo suka bishi sbd yanda yake tafia da yanda sukaga damuwa karara kan face dinshi shows kodai wani ya 6ata mashi rai ko kuma yana cikin serious rashin lafia idan akayi laakari da raman da yayi…yana shiga Mummy ta fito daga parlonta tana dubansu tace”kaman muryan Bobby naji yanxu”…Sab ne yace”shine..amma Mummy kinganshi kuwa?..bashida lafia ne?..”Mummy bata iya cewa komaiba ta bishi zuwa part din nashi…yana zaune gefen gado yana kokarin cire takalman kafanshi ta shigo dakin…saida ta isa har ciki ta zauna nan kusada shi snn ta dubeshi da kyau kafin tace”yanxu Bobby bakaji duk fadan da nayi maka ba daxun koh?..”rausayar da kai yayi yana kallonta kaman zaisa mata kuka yace”Mummy to yanxu me nayi?..”tace”kaki ka kwantar da hankalinka ka dena sama kanka damuwa mana…yanxu kana tunanin wnn damuwar da kake zaiyi sorting things out ne?..”rai a 6ace yace”Mummy yarinyar ce ta rainamin hankali…har wace ita da zan dinga kira tana ignoring min call?..har rejecting calls dina fa ta farayi sbd taga ban hadata da babanta ba”…murmushi Mummy ta saki tana kallonshi tace”kenan dai idan na fahimceka ignoring calls dinka da take bai maka dadi ba..u want her to be answering ur calls koba haka ba?..”da sauri ya shiga girgiza kanshi yace”Mummy don’t misinterpret me plss..that’s not what i mean”…tace”then why all this damuwa idan abun bai dameka ba?..why ka kasa cire abun a ranka har yake saka rama haka?..”shiru kawai yayi baice komai ba as basan mezai fada mata ba..sam bashida abun fada..shi kanshi yana mamakin kanshi wai the whole him ne yake damuwa sbd wata can tana ignoring calls dinshi…abun ya dameshi sosai bai abunda bai ta6a tunanin faruwa dashi ba har abada…ganin yanda yayi kicin kicin da fuska Mummy ta kara sakin smile tana cewa”nidai i want u to take it easy on urself plss..i told u kana bata hakuri komai wucewa zaiyi amma baka yadda ba”…tun kafin Mummy ta rufe baki yayi spitting yana fadin”over my dead body”..murmushi har yanxu takeyi tana girgiza kai…wnn hakilon nashi karamin daria yake bata ba wlh..kiri kiri ga abu yana feeling amma dan banzan ego dinshi bazai bari yayi admitting ba…mikewa tayi ta fita daga dakin don kawo mishi abincinshi tunda da dadewa ya yayema kanshi cin abinci tare dasu.

Ranan Tuesday karfe biyu ya bar Hospital zuwa College sbd yanason mgn da Nur…tunda incident din nan ya faru basu sake haduwa ba…yasan tunda yaji shiru Nur ko a waya bai nemeshi ba fushi yakeyi dashi…da kanshi ma yayi driving sbd driver dinshi baida lafia…yana shiga cikin premises din bayan yayi parking ya nufi Office din Nur yanata baza ido wai ko zai ganta a nan waje amma ko mai kamada ita bai ganiba.

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
27
Yana shiga ya iske Nur zaune kan office chair dinshi yana aiki da laptop yana ganinshi ya wani hade rai yanacigaba da aikin gabanshi ko kallon inda yake baiyi ba…Bobby ya karasa ciki ya zauna yana kallon yanda yake wani ciccin magani kawai saiya saki murmushi yana girgiza kai yace”Man how far?..”banza Nur yayi dashi yacigaba da aikinshi…Bobby ya sake cewa”Man meye haka ne plss?..stop acting like a kid”..tun bai rufe baki ba Nur ya dago yana kallonshi rai a 6ace yace”oh really?..wato I should stop acting like a kid sai kace kai ka manta wulakancin da kayimin harda korana office dinka ba”…saida ya barshi ya gama snn a nutse yace”I wasn’t on my sense..I was furious kai kuma kazo kana so kayi adding to what i was going through shiyasa nayi reacting that way amma am sorry”…wani harara Nur ya dago ya watsa mashi snn yacigaba da aikinshi…Bobby ya dan dafe goshi yanajin kanshi na wani sarawa sbd wnn abunda Nur yake..baisan meya sameshi ba amma shi yanxu sam bayason hayaniya..sam baison matsala idan ba hakaba head dinshi yayita mishi ciwo knn kaman me hypertension…after like 3 mins ya sake dagowa yana dubanshi yace”yanxu bazaka hakura ba dai knn?..”ba tareda ya dago ya kalleshi ba yace”ba haka ake bada hakuri ba ai..kai kanka kasan abunda kayi is uncalled for amma ya zanyi dakai?..”dan murmushi Bobby ya saki yana shafa lallausan gashin kanshi yace”to nace am soryy shikenan?..”sai yanxu Nur ya dago yana dubanshi yace”to yanxu kam na hakura..amma on one condition”…kallonshi Bobby yayi sai kuma ya dauke kai alaman baison wani mgn again..yasan tambayan da zaiyi mishi shi kuma sam bashida amsan bashi…tunanin nashi bai dire ba Nur yace”tsakaninka da Allah meya 6ata maka rai ranan?..”shiru kawai Bobby yayi as bayason fada mishi abunda ya faru…shi kuma Nur dage shoulder dinshi yayi yacigaba da aikin gabanshi yace”idan tayi naji”..qala dai baice mishi ba ya mike hands dinshi a aljihu…Kallonshi Nur yayi yace”so wucewa zakayi?..”yace”yes dama abunda ya kawoni knn?..”Nur ya sake daga shoulder dinshi yace”alright sai Thursday..my regards to Mummy dasu pretty”…Bobby ya amsa da”zasuji”..snn ya fita a office din..Nur ya bishi da kallo yana murmushi yace”dan rainin hankali zama ka gama guje gujenka ka dawo kan hanya ne…waya fada maka Borno gabas take?..”yana gama fadan haka sai ya kwashe da daria hadda su buga table ya sake cewa”su Dr Bobby in love har na matsu naga karshen love story din nan..da yake novice ne shi har dan ramewa naga yayi sbd damuwa..kai amma Lamido ta hadu wlh..kin gama min komai tunda kika fara daidaita wnn dan iskan”..ya karasa yana ske rushewa da daria…shikam ko baa fada mishi ba yasan definitely son Lamido yake sbd abubuwan da yaga yanayi dama wanda ita kanta Lamidon ta fada mashi.

Yana fitowa yaci karo da ita ta fito daa office din Sir Abdool aikam tana ganinshi ta wani hade rai tayi wucewarta abunta ko kallon inda yake batayi ba…saida takai bakin kofa sai kuma ta juyo idonta a kasa tana sake daure fuska murya a ciki ciki tace”ina yini”..kallonta kawai Bobby keyi without blinking…wasu irin ramuka da baisan dasuba a cikin heart dinshi yaji suna ciccikowa just by seeing her…haka nan yaji ganin nata gladen his heart sai a wani 6angaren kuma yaji ciwon zuwa office din Abdool da tayi…idan bai manta ba da bakinta ta ta6a furta mashi Abdool din sonta yake kuma shine zata biyoshi har office dinshi sbd batada hankali…ganin ta gaisheshi bai amsa ba ta juya zata wuce yayi saurin dawowa hayyacinshi snn ya dan daa murya ya kira sunanta”Aysher”…juyowa tayi tana dubanshi da mamaki…this is the very first time da taji sunanta a bakinshi..ko Lamido bata ta6ajin ya kirata dashi ba balle kuma Aysha da dama ba kowa ke kira a college din ba…takawa ya shigayi a hankali zuwa inda take..ya juya tabbatar ba kowa inda suke kafin ya sake juyowa yana kallonta ba yabo ba fallasa ya nuna mata hanyar office dinshi yace”muje”…turo baki tayi tana sake cin kunu tace”sir nifa class nakeso in koma”…bai sake ce mata komai ba kawai ya zuba mata idanunshi da yasan bata isa ta sake mishi gardama idan har ta kallesu…lokaci daya ta wani hade rai ganin yana kokarin yasata yin abunda batayi niyya ba bayan duk wulakancin da yayi mata hadda kiranta karuwa shine yau zai wani zo yace mata muje kaman shi ya haifeta…kallon da taga bazata iya jurewa ba ta wuce zuwa office din nashi yana binta a baya…da kanshi ya bude office din ya shiga snn itama ta shigo ya maida kofan ya rufe..ya karasa kan sofa ya zauna itama ya nuna mata wanda ke opposite dinshi yace”seat”..rungume hannunta tayi tana sake hade ranta tace”am comfortable here”..baice qala ba ya mike daga nan inda yake ya karasa ya tsaya dab da ita har suna jin kamshin perfumes din juna ya rungume hannu idonshi na kanta yace”fushi kikeyi dani?..”da mamaki sosai ta dago tana kallonshi don batayi excepting such mgn daga bakinshi ba..shima kanshi Bobbyn baisan lokacin da mgnr yayi escaping lips dinshi ba..it’s like mgnr ya fito direct from his heart bawai a baki kadai ya tsaya ba…ganin yanda suka hada ido kuma sai taji kunya ta sake yin kasa da kanta tana turo baki…shikam bai iya dauke idanunshi kanta ba ya sake cewa”say something mana..are u mad at me?..”sake kautar da kanta tayi tana cigaba da turo bakinta tace”cewa fa kayi ina karuwanchi”…wara idanu yayi cikeda mamaki yana kallonta yace”Nii?..when did i say that?..”wani irin bacin rai taji ya rufeta na ba gaira babu dalili kawai sai tayi kasa da idonta…Bobby da duk yaji hankalinshi na neman tashi cikin wani irin murya dashi kanshi baisan yana dashi ba yace mata”Aysher speak manaaa”…runste idanu Lamido tayi nan take taji hawaye na neman ciko idanunta…a take hankalin nashi kuwa ya karasa tashi cikin wani irin rauni da baisan daga ina yake fitowa ba yaji yana ce mata”dont cry plss..ki fadamin yaushe nace maki kina karuwanchi?..”hannu takai tana goge hawayen nata baki a tunzure tace”ba haka kace ina biye biyen maza ba..kuma ni ba biye biyen mazan da nakeyi ko Sir Abdool da ka ganni dashi shi yake sona bani nake sonshi ba”..baisan lokacinda bakinshi ya furta”shi kuma wnn dayan fa?..”dagowa tayi tana kallonshi dan bata gane wa yake nufi ba..ya wani hade ranshi kafin yace”that boy..wanda kikayi acting as his wife ranan da kukayi drama”…dan murmushi ta saki da wet face dinta jin wanda yake nufi tace”bestie na nefa”…kallonta kawai yake rai a 6ace ya rasa ma abunda zaice mata…ganin ta sake maida fuskanta ta dinkeshi tsaf kmr ba ita ta gama murmushi yanxu ba yace”is that why u are not picking my calls?..”tana turo bakinda ya zame mata sabo ta daga alaman eh..yace”then i am sorry…da nace kina biye biyen maza i never meant that kawai raina ne a 6ace..are we good now?..”shi kanshi yana mamakin kanshi yanda ya kwantar da murya yana mgn da ita…kai ta sake daga mishi alaman eh snn kuma tace”amma sir dan Allah ka denamin masif..”bata karasaba sai tayi saurin rufe bakinta tana kallonshi tace”sorry ina nufin fada..kuma ka dena kallona da idanunka yana bani tsoro”..murmushi kawai ya saki abunda ya mance yaushe rabonshi da yayi kawai ya koma kan sofa ya zauna yana cigaba da binta da ido..har wani ajiyan zuciya ya saki a 6oye sbd wani irin relieve da yaji just by patching things up with her..zuwa yanxu duk taurin kanshi yasan tabbas bazai iya daukan tana fushi dashi ba sbd ya fuskanci zuciyarshi bata san wnn karatun ba…ganin ya koma seat dinshi ya zauna itama ta dan kalleshi gamida kauda kai tace”sir zan tafi”…kallonta still yake yanajin kaman kar ya barta ta tafi…sam bai gaji da ganinta ba amma ko kusa yaki yin addmitting hakan..sbd ya karyata zuciyarshi da take ta mishi ihun cewa Lamido wani 6angare ce mai girma na cikinta kawai sai ya nuna mata kofa tareda fadin”u can leave”…yana rufe baki ta juya ta fita tana mamakin wai yau proprietor ne yayi mgn da ita haka ba wnn masifan nashi har yana bata hakuri..lallai kuwa za’ayi ruwa da qanqara…shi kuma Bobby sai yaji kaman an sauke mashi wani abu mai nauyi cikin zuciyarshi just by patching things up with her…baisan meyasa ba amma sai yajishi garau duk wnn damuwowi daya sanyama kanshi na kusan sati guda babu su…ranan har ‘yan gidansu sun fahimci yana cikin nishadi don yanda yake murna da farin ciki says it all…Mummy dai sai binshi da kallo take cikin ranta tana”Allah dai ya tabbatar min da alkhairi”…nikuwa nace mata”Ameen Ameen Mummy”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button