Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 3208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
20
Ranan monday kiri kiri tayi kwanciyarta a hostel taki shirin shiga school din wai ita batada lafia bazata je ba…ba yanda Billy batayi da ita kan ta shirya su fita ba amma sam tace ita bata zuwa sbd tasan idonta idon proprietor ci mata mutunchi zaiyi…haka Billy ta hakura ta rabu da ita sauran da ya kamasu suna rawa tare ranan suka tambayi Billy why bata shigo school ba Billy ta amsa da batada lafia…sam basuyi tunanin da gayya tayi hakan ba so ba wanda ya sake daga maganan saidai kaf cikinsu ba wadda ba a tsorace take da kiransu da proprietor keyi musu ba..duk tsoronshi sukeji sbd bai daya daga cikin masu sakin ma yara fuska balle har suga damanshi…gashi kuma yanada wani irin kwarjini da kowane yake iya resisting idan yana tare dashi ba..yanada wani irin huge spirit dake sanya ma mutane shiga taitayinsu idan suna tare dashi…sai kuma uwa uba eyes dinshi da kowa ke fadarsu wajen nutsar da fitinanne.

Karfe biyar da wani abu ya shigo college din dan saida ya gama da Hospital snn ya taho…don ma zuwan ya kamashi dole ne amma da baiga dalilinda zaisa yashigo college monday ba tunda ba ranan shigowanshi bane…kawai ji yake idan baiga yarinyar nan yaci mata mutunchi ba bazai samu nutsuwa ba..sam bazai samu ya huce takaicin data kunsa mashi na ganinta da yayi tana rawa ba…ba ita kadai ya gani tana rawan ba amma ba na wanda ya tsaya mishi a rai kaman ita baisan meyasa hakan ba…ko don sbd tafi kowa zakewa ne oho…har yanxun ya kasa mance scene din…ya tuna ranan dinner wan Rayhan ma itace sahun gaba a masu rawa and yanada yaqinin suma itace ta koya musu…mamaki yake why yarinya kamarta take da shegen rashin ji haka..tanada fitina that yake ganin sam yafi karfin shekarunta…dukda ba sani age dinta yayi ba yasan tayi wuta takai 20 maybe ma bazata fi irin 19 ba haka…shidai da shine yake da ‘ya kamarta ko zata mutu bazai kaita karatu wani garin ba wlh sbd fitinanta yayi yawa…she is so stubborn that yake ganin aurar da irinsu kawai ya kamata ayi a huta…kai tsaye office din Nur ya nufa ya samu zai fita daga office din sbd meeting da yake dashi da entire college staff din yanxu…da mamaki sosai yake duban Bobby dan zai iya tanstewa bai ta6a ganinshi cikin college a irin wnn time din ba kuma ranar monday…komawa ciki yayi yana sake kallonshi yace”mazaa hope everything is fine?..meya kawoka college at this time?..”ta6e baki Bobby yayi yace”yaran nan na hostels zakasa a kiramin”…wara idanu Nur yayi cikeda another mamaki yace”ban gane yaran hostel ba?..wane yaran?..”tsaki Bobby ya saki cikin fara gajiya da questions dinshi yace”wadanda suka maidamin building club mana?..or are u tryinyto tell me baka gansu suna rawa ranan da muka shiga hostel din ba?..”shiru kawai Nur yayi yana kallonshi yasan definitely da akwai abu a qasa…idan ba haka ba why zaice a kirasu kawai sbd yaga suna rawa a hostel…ya bude baki zaiyi mgn Bobby ya katseshi da fadin”hold that to ur self plss…kawai kasa a kirasu kaima ka wuce meeting dinka…u are wasting our time”…wrist watch dake hannunshi ya duba yaga fa time na tafia and yanaso suyi meeting din nan dan haka ya fita daga office din yasa a kira mishi su kaman yanda yace snn shima ya shiga meeting dinshi bayan ya kudurce a ranshi sai yaji dalilin wnn abubuwan da yake.

Yana zaune office din after like 10 mins suka shigo gaba dayansu…idonshi na kansu har karaso ciki duk suka durkusa nan gabanshi yace su mike tsaye…bayan sun mike ya sake baza idanu yana son ya hangota amma sam bai ganta ba..yasan kuma zaiyi wahala idan ba da gangan tayi haka ba…bai tambayesu itaba ya shiga yi musu nasiha a nuste…gaba dayansu mamaki sukayi da sukaji ba masifa zaiyi musu kaman yanda sukayi tunani ba…nasiha ce yake musu mai ratsa jiki wanda da yawa daga cikinsu basu san there is this side of him ba sai yanxu…gaba daya kallon wanda bai san komai ba sai masifa suke mishi amma yayi proving dinsu wrong at this very moment…ya nuna musu illan da jin kida da rawa ke iya haifarwa especially gasu da suke mata snn yayi musu na killace jikinsu koda a cikin hostel ne domin kuwa ko babu maza hostel din bazaa rasa aljanu ba and gaba dayansu sun san aljanu da son mata mussaman masu kyau kyau dan haka suka dauki nasihan nashi da muhimmanchi…godia suka hau mishi bayan ya gama tareda alqawarin zasu kiyaye gaba inshaAllah…dadi sosai yaji wanda har hakan ya nuna a face dinshi ta hanyar dan murmushi daya saki and da yawa daga cikinsu was like”wow!..ashe haka smile ke mishi kyau shiyasa yakeda tsada a wurinshi?..”shidai bai sake ce musu komai ba har suka juya zasu fita…kasa hakura yayi ya dan dakatar dasu da fadin”are u sure gaba dayanku ne nan?..”wata daga cikinsu that is already crushing him tace”no sir akwai guda daya batazo ba..tana hostel batada lafia”..kanshi kawai ya iya gyada musu nan suka juya suka fita…mikewa shima yayi ya fita a office din cikin ranshi yana ayyana yanda zaiyi da yarinyar nan duk ya hadu da ita…baisan meyasa duk ta tsaya mishi a rai ba…sam ya kasa mancewa da ita duk kuma kokarin da yakeyi na ganin yayi hakan…deep down yasan ko rantsuwa yayi tana sane taki zuwa baizaiyi kaffara ba cox he is 100%sure kin fitowa tayi sbd gudun haduwa dashi…shi kanshi kuma baisan why yakeson punishing nata kan laifin da bashi ta aikawa ba…ba kuma shi zai samu matsala ba idan ma aljanu sun shafeta as result of abun da tayi…sam ya kasa gane kanshi these days…abubuwanda he don’t use to care about sun fara damunshi yanxu…sam da ba haka yake ba…yana ganin ko a titi zai ganta tana rawa bai zama lallai ya dameshi ba amma yanxu a cikin hostel dinsu ne and abun ya dameshi fiyeda tunanin mai karatu…yana karasowa ya bude mota ya shiga driver yaja ta suka fita a harabar makarantan.

Wahegari saida yayi da gaske snn ya iya hana kanshi zuwa college din don ji yake kawai idan bai ganya yaci mutuncinta ba bazai samu nutsuwa ba…amma haka ya hakura sbd gudun tarin tambayoyin da zaisha wajen Nur wanda for sure yasan bayada amsarsu…tun daga wnn ranan bai sake shigowa college ba sai ranan Thursday that is normal days daya saba shiga dama…around seven something motanshi ya shigo premises din and yana shigowa yayi nasarar ganinta zaune kan wasu chairs itada qawarta da wani da yake tunanin kilan saurayinta ne shima tunda yaga ba wai kamun kai gareta ba…daga ganin yanda suke mgn suna daria zakasan hira ba karamin dadi yayi musu b…sai Allah Allah yake suyi parking sbd ya tura a kirata yanda bata isa tayi escaping ba amma kamar ance ta juya idonta ya sauka kan motanda a kallon farko ta gane nashi ne…bata tabbatar da cewa nashin bane saida ya wuce ta gabansu taga plate number din Dr.Bobby 5 ai batasan time data mike daga wurin ta nufi classes dinsu da wani mahaukacin sauri ba kaman zata tashi sama…ta jikin mirror yake kallonta yaga yanda take ta faman sauri har tana hadawa da gudu kawai sai ya girgiza kai yana kallonta…kafin su karasa parking ya bude mota ya fito har ta shige ciki dan haka direct kawai ya wuce office dinshi…11 da wani abu ya samu call daga hospital that ana buqatarshi da gaggawa haka ya fita ba don yanaso ba driver ya daukeshi zuwa hospital din…emergency theater suka shiga and basu suka fito ba sai around 1…sallah kawai ya tsaya yayi masjid dake nan asibitin snn ya shiga mota driver yaja suka dauki hanyan college.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button