Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin lokaci kankani akayi bikinsu aka gama…sbd sanin da yayi cewa yan uwanshi da mahaifinshi ba son auren suke ba sai ya nema mata gida a kano ta zauna itama tacigaba da karatunta…tsakaninshi da Gombe saidai yaje ya gaisa dasu ya dawo kanon ma kuma bai cika zama ba sbd a lokacin yana aiki a Delta state…tun bayan aurensu kuma ko mutum daya baizo daga cikin ‘yan uwanshi da sunan yazo ganin matarshi ba…a haka suka dauki tsawon shekara daya bata ta6a ganin wani nashi a inda take ba..a lokacin ta damu sosai da rashin zuwan nasu shi kuma saidai ya bata hakuri yace mata komai zai wuce…ana haka ya samu kira daga waziri kan lallai ya tattaro ya dawo Gombe da zama a cewarshi wai matarshi ke hanashi zuwa ziyararsu yanda ya kamata…baiyi nasa musu ba ko kadan as baison ya sakeyin laifi a wurinshi haka ya tattarata kaman yanda wazirin yace suka koma gidanshi dake cikin Gombe…da farko Nadia taji dadin komawan nasu sbd tana ganin idan tana kusa da yan uwanshi zasufi saurin kar6anta a matsayin suruka sai kuma daga baya ta gane mutanen nan bazasu ta6a kaunarta ba…kyara da tsangwama ba kalan wanda bata gani ba a wurinsu abun har ya kai ko taro sukeyi bata isa ta shiga cikin matan brothers dinshi ba dan zasu yita jifanta da munanan kalamai suna cewa ita inyamura ce..hatta yaransu sunan da suke kiranta dashi knn inyamura…a lokacin data samu cikin Sumayya tayi farin ciki sosai sbd tana ganin kilan idan ta haihu zata iya samun soyayyar waziri dana sauran ‘ya’yanshi ko dan sbd abunda zata haifa…mahaifiyar mijinta dama bata ta6a samun matsala da ita ba hakama Munubiya..kawai dai basa iya sakewa su nuna damuwa da ita sosai sbd gudun 6acin ran waziri…duk wnn abun da ake Attahir bai ta6a daga baki yace zaiyi mgn ba sbd yasan ko yayi ba amfani zaiyi ba tunda goyon baya suka samu wajen waziri…’yan uwanshi da dama tuni yasan basa kaunarshi sbd soyayyan dake tsakaninshi da waziri shiyasa suke amfani da wnn damar suna rura wutar tsanarshi cikin zuciyar babanshi…yana sane sarai suke tunzurashi yake aikata duk abubuwan da yakeyi shiyasa bazai taba bude baki yayi complain ba fatanshi daya Allah ya rabashi da mahaifin nashi lafia.

Lokacin da aka haifi Sumayya Attahir yayi farin ciki sosai hakama qanwarshi mahaifiyarshi sun tayashi murna matuka saidai babu daman nunawa sbd waziri…lokacin da ya dauketa ya kai masa ita ko kallonta baiyi ba yace ya fitar mishi da ita a wurin…wnn abu ba karamin 6ata ranshi yayi ba…yana ganin ko arniya ya aura bai kamata ace his own father yayi treating yarinyarshi irin haka ba..abun ya 6ata ranshi matuka…wnn dalilin yasa baiyi shawara dashi kan sunan da zaa sama yarinyar ba kamar yanda sauran ‘yan uwanshi sukeyi duk wanda matarshi ta haihu shi ke za6an sunan da za’a sa…baiyi shawara da kowa ba yasa mata Sumayya sunan qanwar Nadia da bata dade da rasuwa ba a lokacin…aikam taji dadi sosai dan bata ta6a zaton zaisa sunan yar uwarta ba.

Haka rayuwa yacigaba da tafiyan musu yau dadi gobe babu har Sumayya ta fara wayo..a lokacin itama sai aka fara tsokanarta da inyamura ko kuma su kirata da ‘yar inyamura..wnn abu ba karamin daga hankalin mamanta yake ba amma ba yanda ta iya haka a koda yaushe take bata hakuri tareda fada mata cewa watarana komai zai wuce wnn dalilin yasa ko ina bata zuwa kullum tana gida nane da mamanta idan mahaifinta na gari kuma tana nane dashi…duk wnn abun dake faruwa Nadia bata nuna mishi damuwarta sbd yanda yake iya bakin kokarinshi yaga basuyi lacking komai ba itada ‘yarshi.

Bayan Sumayya saida ta dauki tsowon shekaru hudu kafin ta samu wani cikin…farin cikin da Attahir yayi da jin labarin cikin har mamaki ya bata…da dadewa tasan yanada son yara tunda tana ganin yanda yakeji da Sumayya amma yanda yake farin ciki da cikin ko wanda bai ta6a haihuwa ba sai haka…wnn dalilin yasa yake kulawa da ita yanda ya kamata…duk yake gari da kanshi yake kaita antenatal idan baya nan kuma tayi driving kanta…a kullum cikin godema Allah take sbd yanda mijinta har yanxu kiyayyan mahaifinshi dana brothers dinshi baisa ya canxa mata ba..ga kuma budi da Allah ke kara mishi a kullum.

Lokacinda haihuwa yazo mata sai akayi rashin sa’a baya gari…daga ita sai Sumy a gidan gashi tanata kiran wayanshi bai shiga as dama ya fada mata zasu shiga jeji she might not reach him sbd network issue…ba yanda ta iya haka ta kira number wani brother dinshi tayi mishi bayanin halinda take ciki yace mata baya gari saidai ta kira wani…bata hakura ba ta sake kiran wani shi kuma yace zai turo matarshi amma shiru har kusan bayan awanni bai turo kowa ba..gaba daya ta fita hayyacinta as ciwon kara gaba yakeyi sosai gashi kuma batada number wani cikin brothers din nashi sai su biyu ga kuma sumayya daketa faman kuka tun daxu ganin halinda mamanta ke ciki…tayi kokarin kiran munubiya a waya itama bata sameta ba..a karshe dai dole sai sumayya ta aika tayi mgn da wata neigbour dinta ba bata lokaci matar tazo ta taimaka mata suka tafi asibiti…lokacin wajen karfe 9 na dare…suna zuwa aka kar6eta akayi labour room da ita..midwives kusan uku ne kanta suna kokarin taimaka mata amma har gabannin asuba bata haihu ba ga dan karen wahala da takesha…sun kira doctor da yake on call sun mishi bayani yace zaizo kawai ayi masa Cs kafin doctor din yazo kuma sai ta fara fitting(jijjiga)..hankali tashe one of midwives dake kulada ita ta sake kiran doctor ta fada mishi tana fitting yace gashi nan kan hanya ya kusa zuwa…dama tunda suka fada mishi yanda blood pressure dinta yayi rising yasan da kyar idan baiyi leading to preeclampsia ba.

Doctor na karasowa basuyi wasting time ba suka shiga da ita theatre…neighbor dinta data kawota asibitin na tareda Sumayya da aka samu tayi bacci da kyar sbd jiya bata samu tayi sosai ba…before a shiga da ita theatre din kiran mijinta ya shigo wayanta dake hannun matar data kawota…nan tayi picking ta kumayi masa bayanin halinda ake ciki…hankalinshi ya tashi sosai ya kuma ce gashi nan tahowa Gombe yanxun nan…suna gama mgn ya wuce airport ya taki sa’a kuma ya samu flight din Kano nan ya sayi ticket ya zauna jiran lokacin tashi yayi.

Bai samu isowa Gombe ba sai around 10…daidai lokacin kuma ake fitowa da ita daga theatre..baisan time din da hawaye ya cika idonshi ba ganin yanda aka turota kan trolley bed an rufeta da wani green kyalle kaman babu numfashi a jikinta…shiyasa tun jiya yakejin hankalinshi ba kwance ba ashe halinda suke ciki knn.
Kai tsaye akayi moving nata Amenity dake female surgical ward…wanda suka kawota suka dagata daga kan trolley bed snn suka dorata kan bed din dakin suka fita…Nurse din da tayi resuscitating baby ta mika mishi babayn ya amsa da sauri itama ta juya ta fita..ya rage dagashi sai Sumayya a dakin dan matar data kawota kin shogowa tayi tace mishi zata koma gida…yayi mata godia tareda kyauta mai tsoka snn ta tafi…a hankali ya karasa kan wani kujera ya zauna har yanxun yana rikeda babyn a hannunshi…ya sauke idanunshi kan babyn da a kallon farko yaga tsantsan kamannin da yakeyi dashi…lokaci guda wani murmushi da bai shirya mishi ba yayi escaping lips dinshi…soyayya babyn yaji yanaji sosai har cikin jininshi..haka suka hada kai shi da little sumayya sunata kallon babyn daketa mustu mutsu abunshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button