Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Lamido na shiga daki daukan waya tayi ta shiga kiran Billy ta fesa mata zancen tafiyarta saudi gobe suna gamawa ta kira besty shima ta fesa mishi..tana shirin kiran Hamma taji karfe nawa ne flight din nasu kiran Prof ya shigo wayarta…dagawa tayi sukasha labari abunsu shima ta sanar mishi zata tafi Umrah gobe amma koda wasa bata fada mishi cewa tana gidansu proprietor ba don tasan for sure hakan zai bata mishi rai…saida suka gama hiransu snn ta kira Hamma shima dai labari sukasha bayan sun gama ta dauki wayan nata ta koma parlour.

Washegari around 11 ta gama shirya kanta tsaf cikin dogon rigan daya siyo mata jiya blue black..tayi veiling da mayafin rigan ta dauki dan small bag daya hado mata dashi duk a jiyan tasa phone dinta a ciki da ‘yan abubuwanta snn ta rataya bag din a shoulder dinta ta fito tanata baza kamshi…Aunty dake zaune tareda Mummy a parlor tana ganinta tace”fa tabarakallahu ah’sanul khaliqeen..sannu Aysha”..dan murmushi ta saki kanta kasa ta karaso cikin parlon tana gaishesu kowa na yaba irin kyawunda tayi yau din nan…Bobby da ya gama shiryawa shima yana fitowa daga flat dinshi idanunshi basu sauka ko inaba sai kanta..heart dinshi har wani irin tattarewa yayi ya koma can gefe guda ya cushe sbd tsabar kyau daya ga tayi..duk yanda yaso ya dauke idonshi a kanta kasawa yayi..tayi mishi kyai fiyeda duk tunanin mai tunani…lokaci daya kuma wani irin kishi ya lullu6eshi daya tuna jrgi zataje ta hau a haka har saudia..ranshi yaji ya baci da batasa hijabin daya hada mata dashi ba..a hankali ya karasa cikin parlon fuska a daure yace mata”shi hijabin laifin me yayi maki da bazaki sashi ba?..”kallonshi tayi taga yanda ya wani hade rai sai ta marairaice zatayi mgn ya katseta da fadin”ki koma kije ki daukoshi ki sameni a mota”..yana fadan haka ya maida dubanshi ga Mummy har yanxu ya kasa sakin fuskanshi yace”Mummy zan kaita airport in dawo”..Mummy tace”to saika dawo..Allah ya tsare”..yace”Ameen”..snn ya juya ya fita daga parlon..itama Aysha juyawar tayi ta koma inda ta baro hijabin ta dorashi kan veiling din da tayi snn ta fito ta sake sallama dasu Mummy da suka rakata har bakin kofa snn ta nufi inda motan nashi yake…ko kafin ta karasa ya gama tada motar yayi warming dinta dan haka tana shiga janta yayi suka fita daga gidan…suna hanya ta sake juyawa ta kalleshi har yanxu fuskanshi babu fus cikin ranta sai take mamakin hali irin nashi…jiya jiyan nan fa ya gama marairaice mata yana cewa ta taimakeshi amma yanxu shi yake wani daure mata fuska kmr ba shine yace idan bata aureshi ba mutuwa zaiyi..ita zuciyarta ya fara tantamar anya ma son nata yakeyi kuwa da gaske?..har suka isa airport baice mata ba itama batace mishi ba..duba agogon hannunshi yayi yaga time dinya kamata ace ya iso ma ya wuce dan haka yace mata”call him kiji idan ya karaso”..batayi musu ba tayi dialling number dinshi..yana dagawa tace”Hamma gamu a airport din fa”..daga daya bangaren Najeeb yace”yea gashi na hangoku yanxun nan..am coming”..daga haka ya kashe wayarshi ita kuma ta shiga dube duben inda zata hangoshi..can ta ganoshi yana nufowa inda suke sbd farin ciki kasa hakura tayi ya karaso inda suke saita tafi da saurinta kawai ta kama hands dinshi tana sakin smile…runtse ido Bobby yayi sbd saukan wani abu da yaji mai kamada saukan aradu a cikin zuciyarshi..shi kuma waye wnn da zataje ta cacime hannunshi haka?..anya kuwa Lamido tanada hankali?..Hamma janyeta hannunshi daga nata yayi yana dungure mata kai yace”zanga randa zakisan kin girma wlh”..wani murmushin ta kara saki har dimples dinta suka fito..Bobby kuwa ji yayi kaman zai hadiye zucia ya mutu…shin wai kowa haka yakeji idan yaga yarinyar da yakeso tareda wani ko kuwa nashi ne yake neman wuce gona da iri?..shidai tunda ya fara son yarinyar nan yayi bye bye da farin ciki..bai tsinci komai cikin son nata ba sai tarin damuwa da ciwon zucia…suna karasowa inda yake ta sake kama hannun Hamman nata tace”Hamma wnn shine proprietor dinmu”..kallonta kawai Bobby keyi yanaso yasan alaqar dake tsakaninta da wnn mutumin da taketa kwakwumarshi tun daxu sbd batada hankali..yasan dai zaiyi wahala ace daddy ne ya haifeshi..kallonshi Najeeb yayi yana murmushi ya mika mashi hannun damanshi tamkar yasan tunaninda yake cikin ranshi yace”sunana Najeeb Auwal Lamido”..Bobby ya runtse ido cikin zuciyarshi yace”shikenan cousin dinta ne..ai dama nasan ni na shiga uku”..a zahiri kuma kokari yayi sosai ya dora wani dan guntun murmushi akan fuskanshi snn ya mika mashi hannu shima kafin yace”Dr Bobby Attahir Waziri”..shaking hands dinsu sukayi Hamma na cigaba da murmushi yace”nice to meet u Dr Bobby”..shima wani murmushin ya kara saki da bai kai zuci ba yace”nice meeting u too”..Lamido dai na tsaye tana kallon faces dinsu idan ta kalli na wnn sai ta juya ta kalli na wnn…bayan sun gama gaisawa ya sake mishi godia kan riketa da yayi a gidansu har zuwa yanxu..Bobby bai iya cewa komai ba sai kai daya daga musu..ko tsayawa ganin tafiyarsu baiyi ba ya juya ya wuce abunshi…ciwo yakeji daya kasance shi din cousin dinta ne..yana bude mota ya shiga ya jingina kanshi da kujera murya can kasa yace”here is another threat”..yasan yanda cousins ke taka muhimmiyar rawa wajen ruining relationships..relationship da yake da kwari ma ruining dinshi suke ballantana nashi da ko fara building relationship din baiyi ba…ya tabbata daga shi har son da yake mata suna cikin tsaka mai wuya..on one hand akwai cousin dinta on the other hand kuma akwai bestynta..shikam ya shiga uku da Allah ya jarabceshi da son Lamido..ya tabbata jarrabashi ake sonyi shiyasa aka jarabceshi da matsanancin sonta saidai fatan Allah ya bashi ikon cinye wnn jarrabawa.

Tun daga wnn rana Bobby bai sake mata mgnr yana sonta ba kmr yanda yayi alkawari..kawai jira yakeyi ta gama tunaninta ta fada mishi shi kuma yayi alkawarin zai dauki duk wani decision data yanke…sallah saura sati daya suma suka tafi Umrah gaba dayansu..ko a can ma ya sake haduwa da ita don daddy da kanshi yay inviting dinsu zuwa masaukinsu…duk halin da yake ciki bai bari daddy ya fahimci sonta yakeyi ba sbd yafison ta fara amincewa dash kafin yaji mgnr…kowa ya dukufa sosai da ibadarshi as goman karshe ne kowa yana fatan saduwa da lailatul qadr…addu’an Bobby kusan rabi akan Lamido yake..roko yake idan akwai alkhairi tsakaninsu Allah ya tabbatar idan kuma babu Allah ya cire mashi sonta daga zuciyarshi snn ya hada kowa da rabonshi…a nata bangaren kuma har ga Allah ba karamin tausaya mishi take ba..sau tari tana kamashi yana kallonta idan yaga zaa gani sai yayi sauri ya dauke kanshi..ko a waya ya dena kiranta sbd alkawarin daya dauka na bazai sake disturbing dinta ba har zuwa lokacinda zata gama nazari akan mgnr…ko Billy bata fadama yace yana sonta ba sbd batason yanda Billyn ke nuna dama can tasan yana sonta itace take raina masa hankali…a can sukayi sallah gaba dayansu sai washegarin sallah suka bar Saudi…jirginsu ya sauka a Kano inda daga nan su Aysha suka wuce Gombe yayinda su Bobby kuma suka wuce gida kowa ya fara shirin tafiya Gombe da zasuyi wajen Waziri.

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
41
The following day karfe 10 suka dauki hanyan Gombe..mota biyu suka tafi dashi nashi dana aunty sumy sai kuma drivers guda biyu…tunda suka wuce wudil Bobby keta faman kallon hanya yana jinjina buwayar ubangiji wai yau shine ya dauki hanyan Gombe da kanshi kuma da son ranshi ba tareda anyi forcing dinshi ba..ikon Allah knn yafi gaban wasa..ada gani yake kome zai faru bazai iya yafewa waziri da yan uwan dad dinsu ba ballantana har ya dauki kafa yaje har Gombe da kanshi amma yanxu gashi nan kan hanyan zuwa Gomben kuma ba tareda wani ya takurashi zuwan ba…abubuwa da dama yaga sun canxa mishi a hanyar bai san ko sbd shekarun daya dauka baije bane..the more suna kusantar Gombe the more zuciyarshi ke kara sanar dashi cewa Lamido ma fa a Gombe take..to ta yaya zaayi ya ganta shida ba gidansu zaije ba…wani 6angare na zuciyarshi kuma na ce mishi ganin nata sai sanyaya mishi zucia amma sam yaki yadda da hakan sbd yasan ko yanason ganinta ma bashida yanda zaiyi tunda baida wani reason da zai fadama babanta na zuwa gidan nasu..besides so yake ya fara nesanta kanshi da ita don ya fara gajia da walakancinta..banda sharrin zuciyarshi ma data kasa hakura da ita ai da bata isa ta dinga masa wnn iskancin yana shanyewa ba da tuni yayi maganinta..da wadan nan tunane suka shigo garin Gombe..nan ya sake wara ido yana kallon garin da yaji wani irin attachment tsakaninshi da garin ya shigeshi..Allah ya sani shi koda can ba Gombe ya tsana ba..tsanar da yayiwa family dinshi ne yasa yakejin kmr ya tsani garin amma he never hated Gombe domin ko ba komai a nan aka haifeshi…kai tsaye adress da waziri yasa aka turo musu sukabi har kofar sabon gidanshi da bai dade da tarewa ba…bude musu gate akayi suka shiga ciki da motocinsu…waziri daya kagara da zuwan nasu kasa hakura yayi saida ya fito compound lokacinda suka shigo…gaba daya fitowa daga mota sukayi suka nufo wurinshi aiko ya buda musu hannu suna karasawa ya shiga hugging dinsu one by one yana sanya musu albarka..har su Miemie saida ya runguma snn suka dunguma zuwa ciki…Mummy dai na daga gefe tana kallon yanda yake cikin tsananin farin ciki sbd ganin jikokinshi..lumshe ido tayi ita ko a haka Allah ya dauki ranta ta cika burinta tunda ta shirya tsakanin yaranta da yan uwan mahaifinsu..har mamaki ma wazirin ya bata ganin yanda jikinshi yayi sauki sosai kmr bashi ne wanda yayi shekara da shekaru yana jinya ba…babban parlonshi da yake saukar baki ya shiga dasu nan aka shiga kawo musu abinci iri iri daga cikin gidan ana ajiyewa a gabansu…bayan sun gaisa an sake neman yafiyar juna yasa aka kaisu masauki domin su huta kafin ‘ya’yanshi daya kira su karaso…Bobby da sab dakuna biyu aka basu dake nan cikin parlon nashi yayinda su Mummy kuma aka shiga dasu cikin gida…daki biyu suma aka basu Mummy da Miemie daya aunty sumy da Ilham suma suka dauki daya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button