Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Har suka dawo daga wajen bikin nan ranshi a 6ace yake don gani yake kowa ma ya gama kalle masa ita yau din nan..itama da yake haushin abunda yayi mata daxun takeji sai batabi takan fushin da yake ba tacigaba da harkokin gabanta..the next day ma haka suka yini a wajen biki sai dare suka dawo gida daga nan kuma suka shiga zagaya wa gidajen yan uwan Mummy duk tana introducing Aysha wa Family dinta wanda basuje biki ba cewa itace matar Bobby..sosai suka samu tarba mai kyau daga yan uwan nata kowa sai nan nan yakeyi dasu kmr a maidasu ciki..Lamido taga kara iya kara a wajensu abun har mamaki ya bata yanda sukeda son yan uwa haka..sunada zumunchi sosai ba kadan ba sai yanxu taga inda Mummy ta dauko zumunchi don yan uwanta kaf zumunchi garesu da kuma son nasu..bayan sun gama ziyara sai suka shiga yawo da ita cikin garin suna nuna mata wurare da dama a matsayinta na wadda bata ta6a zuwa ba aikam tayi kallo iya kallo ta kuma ji dadin zuwanta garin don taci karo da abubuwa da dama wanda suka burgeta..shi kanshi yanayin tsarin garin ba karamin kyau yayi mata ba don da gani take duk states din nan na kudu idan aka dauke Lagos ba wani kyau na kuzo ku gani ne dasu ba amma yanxu tasan she was wrong don Enugu dai kam tanada kyau iya kyau saidai batasan ko iya wurare masu kyawun taje ba..yanda ta ware take harkanta a cikinsu abun har mamaki ya bata don yanxu ta rage jin kunyansu sosai tana kuma iya sakewa cikinsu ayi labari yanda ya kamata tunda ita din dama gwanar surutu ce..tsakaninta da mijinta ma sai abunda yayi gaba don soyayya ne ake zubashi yanda ya kamata..tun tanajin kunya idan yayi mata wani abun gabansu Mummy har tazo ta fara sabawa don ta fuskanci shifa haka yake kuma ba iya denawa zaiyi ba.

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
63
Ana gobe zasu tafi Aysha zaune parlor tareda bobbyda aunty sumy dake bata labarin yanda ya shiga damuwa sbd ita kafin ta fara sonshi ita kuma banda daria ba abunda takeyi tana kallonshi..shidai yana zaune yana jinsu jira kawai ta wuce gona da iri ya taka mata burki don bazai yadda ta 6arar masa da mutunci ba..aunty sumy na kwaikwayon muryanshi tace”Ina fada maki da farko idan akace yana sonki har wani masifa yakeyi yana denying cewa shi ba sonki yake ba amma daga baya har zuwa yake yasa Mummy a gaba yana mata kuka yana cewa mutuwa zanyi..indai ban aureta ba Mummy mutuwa zanyi for sure..Mummy kuma sai ta daga hankali tayita lallashi tana bashi bakin cewa ai watarana zaki soshi”..aunty sumy ta karasa mgn tana kallonshi tana cigaba da daria..Lamido ma daria takeyi iya karfinta tana kuma mamakin wai shine yake kuka akanta kmr dai bashine wnn mutumin daya takurawa rayuwarta ba..da sauri ta juya tana kallonshi da murmushi tace”do u really cry because of me partner?..i can’t believe this?..”daure fuska yayi ya mike yana wani cin magani shi bai yadda ba kar a rainashi yace mata”hiran ya isa haka tashi mu tafi”..dan langabewa tayi still tana danne daria tace”please mana”..kamata yayi ya mikar da ita tsaye ya sake cewa”let’s go”..kmr zatasa kuka tace”to where?..”yace”to my friends house”..aunty sumy tace”yaushe kakeda aboki a Enugu bamuda labari”..yace”gidan Mi’iraj zamuje”..gyada kai aunty sumy tayi tace”kaidai kawai bakason matarka tasan how much u love her”..tana rufe baki yace”ai ko yanxun tasan Ina sonta sosai..baby ai kinsan dai inasonki da yawa Koh?..”girgiza kai tayi tana makale shoulder dinta tace”nidai ban saniba”..wara ido yayi yana kallonta sai kuma ya shiga janta yana daria yace”to bazaki sani ba..now ki wuce muje idan ba so kike in daukeki da kaina ba”..juyawa tayi tana kallon aunty sumy kmr zatasa kuka tace”aunty kiyi mishi mgn plss”..aunty sumy na murmushi tace”karki damu idan kun dawo zamu cigaba daga inda tsaya”..da sauri ta saki wani murmushi tana cewa”yauwa aunty godia nake”..shi kuma ya juya yana kallonta ya saki wani murmushi yace”idan kika cigaba nima zuwa zanyi in samu saurayin Miemie in bashi labarin duk abubuwan da kikeyi ince masa to yayi a hankali ‘yar gidan yarinya zai aura”..ai tun kafin ya karasa ta jefo mashi throw pillow dake kusada ita tana daria tace”sai nayi maganinka wlh..dan rainin hankali”..daria sosai shima ya saki tareda kama hannun matarshi suka fita daga gidan.. already dama Mummy ta fita tun safe tare dasu Miemie so su kadai suka rage a ciki.

Tunda suka shiga mota take juyawa tana kallonshi akai akai tana sakin murmushinda ya kasa tantance na menene..ganin yanda take kallonshi sai shima ya dan juya ya kalleta for like 2 secs snn ya dauke kanshi yanacigaba da driving..Lamido da ta matsu taji karshen labarin nan tace”dan Allah da gaske partner ka ta6a yin kuka sbd ni?..”kai ya gyada mata ba tareda kallon inda take ba yace”of course..ba sau daya ba ba sai biyu ba”..yana rufe baki tayi wani irin zaro ido kmr wanda taji abun tsoro hadda su rufe baki da hannunta cikin so much excitement tace”ikon Allah..i can’t believe this”..juyowa yayi ya kalleta kafin ya maida kanshi ga titi yace”u have to believe..ba karamin wahala nasha kanki ba”..sake gyara zama tayi tana facing dinshi tace”tell me more plss..i want to know”..murmushi ya saki tareda gangarawa gefen titi yayi parking snn ya juyo yana kallonta..kallonshi itama takeyi with a smile don da gaske abun really get to her jin cewa mijinta har kuka yayi sbd ita..it’s kind of romantic..kamo hannayenta yayi ya rike yana kallon cikin idanunta babu alamar wasa tattare dashi yace”i have suffered alot..na wahala sosai..duk wani taurin kai da zafi irin nawa saida na nemesu na rasa because of u..at first nayi tunanin tsanarki nayi sai daga baya na gane it was not hatred but love..duk wnn abubuwan that i have been doing to u inayinsu ne with the out of pain and anger..gani nake kmr zuciata batamun adalci data bari na fara sonki ba..wnn dalilin yasa koda yaushe nake maki masifa duk a kokarina na ganin nayi denying the fact that ina sonki amma the love was very powerful..it was more powerful than my heart shiyasa all my effort go in vain sbd na kasa cireki a raina”..dakatawa yayi yana kallonta eyes dinshi har wani ja sukayi sbd tunawa da mawuyacin halin daya shiga a wancan lokacin..itama kallonshi takeyi ko kifta ido batayi sbd yanda takeso lallai taji karshen wnn labarin nashi..ta lura har yanxun abun na ta6ashi don gashi nan ta gani a idanunshi..bata ta6a sanin ya wahala haka a kanta ba..hannunta ya saki tareda kai hannu ya kara karfin ac sbd zafi da yaji yanaji from no where snn ya dawo da idanunshi gareta kafin yacigaba”a lokacin Allah kadai yasan yanda nakeji idan na ganki da wani..ji nake tamkar zuciata zata tarwatse ta dalilin abunda nakeji..wnn dalilin yasa zakiga duk wani abu da zakiyi idona yana kanki musamman daya kasance kedin fitinanniya ce bakijin mgn”..tun kafin ya rufe baki takai mishi duka a chest dinshi tana wani narkewa tace”nine fitinanniya koh?..”janyota yayi jikinshi yana shafa bayanta yace”eh mana..kin bani wahala sosai amma yanxu duk ya wuce tunda na aureki”..dagowa tayi tana kallonshi da murmushi tace”ni kuma da gaske a lokacin na tsaneka..ko ganinka banason yi sbd masifan nan naka kuma tsoronka fa nakeji sosai nunawa ne kawai banayi”..murmushi shima yakeyi yace”na sani wlh..nasan maybe duk dunia ba wanda kika tsana irina a lokacin sbd takurawan da nake maki”..kanta ta gyada tareda kama hannayenshi tana dubanshi sosai tace”sosai ma kuwa..kawai gani nake u are against my happiness but i was wrong”..tsura mata ido yayi yana kallonta for some minutes kafin yace”kinsan tun yaushe nasan ina sonki?..”girgiza kai tayi da sauri alamar bata sani ba..yace”ranan wata Monday 11th of July around 8:15 am”..shiru tayi tana kallonshi ido a wajen jin har su date da time ya rike na tsahon wnn lokacin..kallon yanda ta bude idon yayi sai ya saki murmushi bayan yayi pecking dinsu yace mata”yes ranan da kuka fara clinic posting dinku na first semester year two..ranan kunzo zakuyi reporting a Freedom kawai naga kinshiga motar wnn tsohon mutumin”..kamo hannunta yayi ya rike sosai yace”wlh Aysha kasa fitowa daga cikin motata nayi..i was just sitting inside looking at direction na motar nashi inajin kaman inzo in fito dake daga ciki..yanda naji zuciata ta buga a wnn lokacin na tabbatar da cewa am in love amma naki admitting..kuma fa nike Shan wahala ba wani ba amma still naki amincewa sonki nake..ban kara shiga damuwa ba sai ranan da daddy da bakinshi yace ya bani amanarki..tun daga wnn lokacin abubuwa suka fara kwa6emun amma still ban yadda ina sonki bafa”..ya karasa mgn da murmushi a fuskanshi dan shi kanshi sai yanxu yake ganin wautan da yayi a wancan lokacin..Kiri kiri wai yana feeling abu kuma yana denying sbd wani dalili nashi mara tushe..rungumeshi sosai Aysha tayi tana tunawa da yanda yayita cin zalinta a wancan lokacin kuma wai duk a snn ma yana sonta…murmushi ya saki har yanxu tana rikeda hannunta yace”and kinsan the funny part of all these?..”girgiza mishi kai tayi alamar no..yace”farkon tsanar da nayi maki sbd kin kasance Fulani ne Kuma from Gombe..a wancan lokacin na tsani yan Gombe sosai especially Fulani sbd wani abu daya ta6a shiga tsakaninmu da su waziri..amma when i met u..komai ya lalace kmr dama turoki akayi don kizo ki rusa wnn hatred dake tsakanina da Fulani dama Gombe gaba daya..daga lokacin dana fara sonki da yawa daga halayena canxa ba tareda ni kaina nasan lokacinda suke canxawan ba..wayar gari kawai nakeyi in ganni kmr ba Bobby ba”..a akaice labari sukasha sosai kowa Saida ya bama dan uwanshi labarin yanda sukeji game da juna a baya sun ma manta da ba gida suke ba cikin mota suke kuma a kan titi..after a very long conversation ya sake tada motar suka tafi gidan Mi’iraj din da yace zasuje.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button