Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan wata uku…

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
69
Bayan wata uku…
Cikin Aysha ya shiga wata na tara knn cif and edd dinta baifi saura 3 days..gaba daya ta canxa daga Lamido da kuka sani a baya ta dawo wata irin salaha kmr dai ba itane ke ba iyayenta ciwon kai ba..sosai ta zama kalar tausayi dama ga cikin nata da girma sosai musamman yanxu da haihuwan ta kusa sai girman ya sake fitowa..ga kuma nauyinshi da takeji wani lokaci har cewa take kilan twins zata haifa maybe scanning machine dinsu ne baida kyau shiyasa bai nuna haka ba..duk ta Fadi haka saidai Bobby yayi daria dan yasan baby daya ne cikinta saidai girman kawai..ga masifa data koya da rashin hakuri Dan abu karami zata hau fada tana cewa ai dama dole ya dena sonta sbd yanxu tayi Muni shidai banda daria ba abunda yake mata..wani lokaci har video yake mata bata sani ba idan tana wnn sababin yasan idan ya nuna mata nan gaba daria zatayi..sai kuma fever da take yawan kwana dashi da ciwon baya wanda har yasa take cewa kilan mutuwa zatayi..sosai take daga hankalinshi duk tayi wnn mgnr amma bai taba nuna mata ba.. addu’a kawai yake mata tareda fatan Allah ya sauketa lafia..a bangaren mummy ma tana kulawa da ita sosai dan da dadewa itace ta dauki nauyin dafa mata duk abunda takeso tunda ba komai take ciba..yanda take lalla6ata ita har kunya ma takeji amma sai taga su ko ajikinsu..siyayya kuwa zuwa yanxu ba abunda basu gama siya ba tun daga kan kayan baby har zuwa ita kanta nata kayan..bedroom guda ya ware cikin nata yasa akayi renovating dinshi zuwa baby room mai kyau aka kuma cikashi da kayan yara iri iri tun daga kan furnitures har zuwa su toys da sauran kayan wasa na yara..tsakaninta da Amminta ma yanxu mutunci sukeyi sosai dan yanxu tayi hankali ta dena rashin kunya a cewar Ammi shiyasa suke dasawa abunsu..kusan kullum sai sunyi waya da ita dan ko ita Ayshan bata kira ba Ammi zata kirata taji ya jikinta..tana kuma turo mata addu’o’i tace taitayinsu daga nan har lokacin da Allah zai kawo haihuwar wai sai yazo mata da sauki..sosai itama take tausayawa ‘yar tata sbd halin da take ciki shiyasa Husna na gama ssce daddy yace tazo ta zauna tareda ita ko ba sbd aiki ba at least zata dan dauke mata kewar gida da take fama dashi..zuwan Husnan kuma ya yayi mata dadi sosai dan kusan kullum suna tareda ita da Miemie a gidan su suke mata komai saidai mai aiki ta tayasu kawai..shima Bobby yana bakin kokarinshi kwarai wajen ganin batayi lacking wani abu daga gareshi ba including time dinshi da kuma caring..sosai yake tsayawa ya kulada ita don ko wurin aiki ma sai ya tabbatar ya gama mata komai snn yake wucewa hakan da yakeyi kuma ba karamin faranta mata rai yake ba..tana jin dadi sosai idan taga yanda daga shi har Mummy da siblings dinshi ke nuna tsantsar so da kula wa cikin nata har watarana takejin ta matsu ta haihu sbd taga irin kaunar da zasu nunama babyn..gani take kmr Mummy da Bobby sunfi ita kanta da babyn ke jikinta kaunarshi amma batasan ko dan riga yazo dunia bane..a halin yanxu dai duk wani fatanta bai wuce Allah ya sauketa lafia ba.

Yau Friday suna zaune parlor ita da Miemie da Husna suna kallon wani film Sab ya shigo gidan da sallama yana hararar Miemie da gaba daya hankalinta ke ga film da suke kallo..bayan ya karaso ciki ya zauna sai ya dan saki fuska yana duban Aysha da murmushi yace”sannu Aunty Aysha”..murmushi itama ta saki tana girgiza kai tace”bazaka dena cemun sannun nan ba koh?..”yana cigaba da daria yace”ai dole ace maki sannu matar Uncle Bobby..wnn babyn namu nasan da kyar idan baya baki wahala don da gani nasan fitina zaiyi wlh”..daria gaba daya suka saki har su Husna da hankalinsu ya dawo kan hiran nasu..Husna tace”wlh uncle Sab kmr kasan nima tunanin da nakeyi knn..na tabbata indai ya dauko halin Adda to wlh ba karamin fitinanne za’ayi ba”..ta karasa mgn tana daria Aysha Kuma tace mata”zanyi maganinki wlh..ki bari insamu time dinki”..Sab yace”ai idan ya dauko halin babanshi bayan fitina ma sai ya hada da masifa da rashin mutunchi..ta6 Uncle Bobby ai ba baya bane wajen wadan nn dabi’un”..da sauri Miemie tace”wlh kuwa uncle Sab..ni kaina gani nak…”bata karasa ba ya katseta ta cewa”C’mon keep quiet wayasa dake a wurin nan?..”turo baki tayi tana rungume hannunta tace”ai nima ba da kai nakeba”..kwafa yayi yace”kicigaba da murguda min bakin nn watarana saina karyashi wlh..badai ni kikaje kikama munafurci a wurin Mummy ba..zan kamaki ne”..sake daure fuska tayi tace”nidai gaskia na fada mata ai..kuma ba ruwanka dani Uncle Bobby yace ka dena shiga harkata”..ya bude baki zaiyi mgn Lamido tace”ya isa haka dan Allah..na rasa meyasa ku kullum cikin fada kuke kmr tom and Jerry”.. Sab yace”yarinyar nan batada kunya bakisan halinta bane..wai har ni zataje tayima gulma a wajen Mummy”..Husna tace”ASP Uncle Sab da gaske ba gulma tayi Maka ba..a gabana Mummy ta tambayeta”..wani irin daria Sab yayi yana cewa”bazaki dena Asp Uncle Sab din nan ba koh?..”dariar itama takeyi tace”to ai Asp ne naga”..murmushi kawai yayi ya gyada kai kafin wani cikinsu ya sake mgn Bobby da Nur sun shigayi parlon a tare..da sauri Sab ya mike yana kallonsu da murmushi yace”sannunku da zuwa”..Bobby yace”kai baka zuwa sallahn jumu’a knn?..”Sab yace”yanxun na dawo ai..ask Aunty Zata fada maka ban jima da shigowa ba”..Bobby bai sake cewa komai ba suka karasa parlon suma suka zauna..Miemie da Husna suna gaishesu suka bar parlon shima Sab yana gama gaisawa dasu ya fita dan dama akwai inda zaije…kallon Aysha da har yanxu take zaune yayi kafin a hankali ya mike ya koma kusada ita ya zauna yayi mata side hug yana fadin”how is my baby doing?..”a dan kufule tace”ban sani ba”..yayi murmushi yana nuna cikin nata yace”bafa wnn babyn nake nufi ba wnn”..hannunshi ta ture daga jikinta tana duban inda Nur yake zaune tace”Sir Ina yini”..murmushi ya saki yana kallonta shima yace”lafia lau Lamido..ya jikinki?..”kanta a kasa tace”Alhamdulillah”..Bobby yace”baby bana hanaki kiranshi da Sir din nan ba..call him Nur mana ai sunanshi ne”..girgiza kai tayi tana dan murmushi tace”bazan iyaba”..tana rufe baki Nur yace”kinji mutumiyar kwarai..duk iskancinka dai haka zaka hakura ka barta tace bazata iyaba”..Bobby yayi daria kawai tareda dan rage murya yana kallonta yace”kinsan mene?..”kai ta girgiza mashi alamar bata sani ba..yace”zuwa mukayi dai yau mu fadawa Miemie cewa muna sonta”..dan wara ido tayi tana kallonshi tace”da gaske?..”yace”eh mana..nine ma zanyi masa zancen sbd a abokin Nur nazo yau ba Uncle Bobby ba”..murmushi kawai Aysha tayi tana girgiza kai tasan wnn mgnr wasa yake mata..mikewa zatayi yayi saurin kamata ya mikar da ita snn yace ta turo musu Miemie idan ta shiga..tana murmushi itadai ta wuce zuwa bedroom dinta ta tura musu Miemie kmr yanda suka bukata…tana zuwa ta nemi wuri ta zauna kasa Bobby yace ta koma kan kujera ta zauna..ba musu tayi hakan sai kuma duk sukayi dif aka rasa wanda zai fara mgn cikinsu..can Bobby ya nisa tareda Kiran sunanta..ta amsa kanta kasa dan har wani faduwar gaba taji tanayi ba gaira ba dalili..a nutse sosai ya fara mata bayani ta sigar da yasan zata fahimce shi sosai.. already dama Saida ya fara mgn da Mummy da parents din Miemie snn yazo gareta so ba tareda wani shakku yake mata bayani ba..itadai tsit tayi tana sauraran yanda yake koda mata abokinshi sai daga karshe kuma yace zai barta dashi ya karasa Mata sauran bayanin..bayan ya bar parlon Nur ya dora daga inda ya tsaya itadai kusan mutuwar zaune ma tayi jin wai da gaske Uncle Nur ne ke sonta..sosai ya kakkashe mata jiki da salon soyayyarshi wanda ita halin yanxu dai bazata iya gane shin tana sonshi ne ko kuma bata sonshi ba..shima baiyi gaggawa ba yace she should go and think about it idan ma tanada Wanda zatayi shawara dashi tayi idan ta gama yana jiran feedback dinshi..haka ta mike ta bar parlon jiki a sanyaye kmr kazar da kwai ya fashewa a ciki.
Wnn knn…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button