Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin lokaci qanqani sai shakuwa ya shiga tsakaninsu kamar dai yanda Bobby ya daura damara a farko…sam yanxu basu fiya fada ba dan tanabin kusan duk abunda yace tayi sbd ya canza mata posting…ranan da farko da aka sake shiga theater da ita saida tayi wnn suman saura kadan ta fadi Bobby yayi saurin tareta ta fada jikinshi…gaba daya hankalinshi dama yana gareta sbd yasan something like this might happen…dole sai fita sukayi da ita suka kira wata tayi replacing dinta amma daga baya a hankali sai ta fara sabawa…gaba daya tsoron sai ta dena jinshi tunda gashi za’a shiga theatre da ita har ayi a gama bata ji jiri kota suma ba saidai dan wanda baza’a rasa ba…a zaman kuma ta koyi abubuwa da dama dan sai yanxu take gane ashe zama a theater din yanada amfani…a haka ta cinyeshi two weeks dinta a theatre.

Yana zaune office dinshi yana duba patients wayanshi ya fara ringing bai daga ba saida ya sallami matar ta fita..ya saki dan murmushi ganin wanda yake kira snn yayi picking ya gaidashi with respect…a daya 6angaren daddy yace”Attahir kana lafia?..”yace”ina lafia sir..ya aiki?..”daddy yace”Alhamdulillah..kana gida ko asibiti?..”yace”ina asibiti”…daddy yace”alright send me the address na shigo kano sai inzo mu gaisa”..da sauri yace”right away sir..itama tana asibitin yanxu haka”..murmushi daddy yayi kafin yace”ni kai zanzo gani ba itaba”..murmushin shima yayi kafin suyi sallama ya tura mishi address din…cikin mintina qalilan daddy ya karaso hospital din..Bobby da kanshi ya fita ya shigo dashi yanata yaba kyau da tsaruwar asibitin har suka dangana a office dinshi…zaunawa yayi shi kuma Bobby ya bude fridge ya kawo mashi ruwa da lemo snn shima ya zauna suka sake gaisawa…daddy yayita janshi da hira yana yaba asibitin nashi shidai tun yana jin kunya har ya sake ya shigayi mishi bayanin yanda suke gudanar a aiki a asibitin..har Schools da Colleges da yake dasu a sauran states saida ya fada mashi…ya kuma sanar dashi cewa yanxu haka yana preparation na bude Freedom University a Lagos…daddy ya jinjina ma kokarin yaron sosai ya kuma jinjinama kwazonshi da yake iya hada aiyuka da dama haka shi kadai..dukda cewa yana assistant a ko ina shima ba karamin kokari yake ba..nan take yaji ya sake burgeshi matuka..soyayyarshi ta ninku a cikin zuciyarshi fiyeda na baya..saidai ko kusa baiyi mamaki ba sbd yasan jinin Col Attahir zai iya aikata fiyeda haka ma a doron kasa matukar ya gaji mahaifinshi…suna zaune suna wnn hira Aysha ta shigo office din tana kokarin zaro wayanta daya dameta da kara sakamakon kira da akeyi tace”ko uban waye wnn yake damuna da kira oho?..”a tare suka juya suna kallonta jin abunda ta fada…daddy yace”sannu shugaban masu hankali”..batasan lokacinda ta saki waya da jakan nata ya fadi kasa ba sbd muryan wanda taji..sam batayi tunanin ganinshi ba wlh…lokaci daya kuma ta saki murmushi bayan ta dauki bag da wayanta ta karasa cikin office din tace”daddy sannu da zuwa”..girgiza kai kawai daddy yayi yana kallonta..can kuma ya juya yana duban Bobby da kanshi ke kasa yace”nasan kana nan kana fama da ita kou?..”dan dagowa yayi ya kalleta sai kuma ya saki murmushi yana girgiza kai yace”ai tayi hankali yanxu”..daddy yace”kana dai kareta amma ni nasan akwai abubuwanda dole saita yisu zataji dadi”..murmushi kawai Bobby yayi baice komai ba..ita kuma ta wani turo baki a cikin ranta tace”wato da kallon mara hankali sukemin knn da za’a wani ce nayi hankali yanxu”…muryan daddy ya dawo da ita daga tunaninda take nan ta gaisheshi snn yace taje ta kira Bilkisu..bayan few minutes suka dawo tareda Billy itama ta gaida daddy yana tambayarsu ya posting sukace Alhamdulillah…bayan sun gama yace suje kafin ya wuce zai nemesu zaiyi mgn da proprietor dinsu ba musu suka bar office din..shi kuma daddy ya shiga tambayan Bobby if da akwai abunda takeyi wanda ya kamata ya sani Bobby yace sam tayi hankali yanxu ta dena rashin ji..daddy yaji dadi sosai ya kuma ce still dai yanaso yacigaba da monitoring dinta har zuwa lokacinda zata bar makarantan domin koshi a yanxu yaga canji tattareda ita hakan kuma alamane na Bobby ya rike amanar daya bashi knn…Bobby ya amsa mashi da zai kula da ita sosai can cikin zuciyarshi kuma wani abu yaji yazo ya tokare mashi wuya…tunda daddy ya ambaci har zuwa lokacinda zata bar makarantan yaji wani irin sanyi ya kamashi…ashefa watarana gama karatun zatayi ta koma garinsu koh?..shi wlh sam baya kawo hakan a cikin ranshi…baisan ko sbd yanxu yana son kasancewa tarea ita ba amma sam tunanin haka bai taba zuwa mashi ba..yanxu kuma da daddy ya fada saiya tuna mashi cewa watarana da gaske zata bar college dinshi dama kano gaba daya kuma hakan na nufin bazai sake ganinta ba har abada…tunanin hakan saida yasa gabanshi yayi mummunan faduwa..to meyasa bayason rabuwa da ita?..meyasa a kullum yakejin sabbin al’amura gameda ita?..meyasa kuma idan ya ganta da wani yakejin kaman ya rataye kanshi sbd kunci?..for sure zuwa yanxu yasan kishinta yake saidai ko kusa bayaso yayi admitting yana sonta sbd hakan na nufin wargajewar abubuwa da dama a tare dashi..yayi nisa cikin tunani har baiji lokacinda daddy ya mike yana mishi mgn ba…saida ya dafa shoulder dinshi snn firgigit ya dawo hayyacinshi…daddy ya zuba mashi ido sosai yana kallon yanda duk yanayinshi ya sauya lokaci guda…bai tambayeshi dalilin hakan ba sbd a ganinshi ba huruminshi bane dan haka yayi mishi sallama yace zasu wuce Gombe…Bobby yayi mashi rakiya har inda motocinshi suke bayan ya sallami su Aysha ya shiga motar suka fita daga asibitin…Aysha kuma kai tsaye ta bishi office dinshi sbd mgnr changing posting da yace zaiyi mata.

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba… masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
30
Kallonta kawai yakeyi tunda ta shigo office din zuwa yanxu…duk yanda yaso ya dauke idonshi a kanta kasawa yayi…baisan meyasa yakejin wani new feeling tattare dashi ba…baisan meyasa mgnr daddy ya tsaya mashi a rai ba..abu daya daya sani shine ko kusa bayason rabuwa da ita..baiki ta dawwama tana karatu a FCNM ba sbd ya dinga samun ganinta kullum amma saidai sam hakan ba mai yiwuwa bane…sanin kanshi ne hakan bazai ta6a yiwuwa ba koda a garin ga6a ga6a suke kuwa…watanni kadan da ya tabbata basu kai shekara ba suka rage mata ta gama karatunta and this means watanni kadan ya rage masa a tareda ita..watanni kadan ya rage masa kafin ya dena ganinta har abada tunda shidai yasan nor matter the situation bazai ta6a kai kanshi Gombe ba balle watarana yace zai nemeta su gaisa tunda ya shiga garinsu…gaba daya wadan nan tunanin sun cika mashi zuciya sun kuma hanashi sukuni…Aysha da taga idanunshi ne kadai a kanta amma mind dinshi is elsewhere ta dan buga table dake gabanshi tace”Sir am talking”..da sauri ya lumshe idanunshi kafin kuma ya budesu a kanta yanayi mata kallonda zata iya rantsuwa da Allah tunda suke bai ta6ayi mata irinshi ba…voice dinshi can kasa yace”what happened?..”narkewa tayi tana wani kallonshi kasa kasa tace”sir kace fa idan nayi two weeks zaka canxamin posting”…dan wara idonshi yayi a kanta kafin yace”then ki dawo office dina”..ta wani turo baki tace”nidai no dan Allah..cewa fa kayi duk inda nakeso zaka kaini?..”gyara zama yayi still yana kallonta yace”to ina kikeso?..”da sauri tace”eclamptic ward nakeso naje nayi two weeks..the remaining two weeks kuma sai inyisu a Ante Natal Clinic”…gyada kai yayi alaman ya gamsu kafin yace”zakije inda kikeso but on one condition”…da sauri tace”meye condition din?..”yace”bazaki shiga harkan kowane doctor ba a wurin..infact bama doctors kadai ba kowane staff indai namiji ne i want u to stay far away from him”..da sauri ta shiga gyada kai tana murmushi tace”bazan shiga harkan kowaba wlh..aini bana da interest kan doctors ko health workers sbd son matan su yayi yawa..besides inama da wanda zan aura”..fuska a tamke yace”to waya tambayeki?..nace maki inason ji ne?..”dan turo baki tayi tace”to kayi hakuri nidai”..yace”tashi ki barmin office”..ta marairaice tace”sir posting dinfa?..”yana nuna mata kofa yace”i said out”…maimakon ta fita saita fara bubbuga legs dinta a qasa zata fara mishi kuka tace”toba kai kace zaka canxamin idan ma nutsu ba?..alqawari fa ka dauka”…kallon yanda take tale baki yayi kawai sai ya saki murmushi hade da girgiza kai…wnn yarinya shidai bai ta6a ganin irinta ba wlh…ita kuwa kuka ta fara na karya kafin ya dakatar da dariyan da yakeyi yace”da nace saikin nutsu ai ba nutsuwan kikayi ba..yanxun fa kika gama min rashin kunya a nan”…ta wani zaro ido tana cewa”rashin kunyan me nayi?..”fuska a dan daure yace”kikace baki son doctors da health workers..sbd tsabar rashin kunya hadda cewa kinada wanda zaki aura”..if u see yanda ya karasa mgn face dinshi daddaure zakayi tunanin bashi ne ya gama daria a while ago ba..abun yayi mashi ciwo da har ta iya bude baki ta wani ce mishi tanada wanda zata aura?..sai kace cewa yayi shi zai aureta?…ganin yanda ya sake dinke fuska sai tayi kasa da murya tace”to am sorry”..a takaice yace”naji..tashi ki tafi”..kaman zata tashi sama haka ta dauki jakanta ta fita daga office din nashi rai a 6ace tanata faman bambami ita kadai…shi kuwa tana fita ya kifa kai da table din gabanshi ya shiga sauke numfashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button