Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Nur na barin office din dama kai tsaye inda ya ajiye motarshi ya nufa ya bude ya shiga ciki sai ga Billy itama ta karaso ta dan langabe kai tace”sir nima ka ajiyeni hostel plss”..kallonta yayi kafin yace”why?..bazaki bari ku koma tareba?..”da sauri tace”nasan proprietor zai dawo da ita sir dan Allah ka mai dani”..bai sake cewa komai ba ya bude mata motar yace”to shigo”..ba musu ta shiga ciki Nur ya tayar da motar suka fita daga asibitin.

Karfe sha daya da kusan rabi Lamido ta shiga bude idonta a hankali har ta waresu fes akan Bobby da har yanzun kanshi ke kife nan kusada ita yana nashi baccin..zare idanun tayi da kyau tana kallonshi da mamaki ganin ya wani kwakwume mata hannu ya rike cikin nashi..daddagewa tayi ta kwace hannun nata tana zabga masa harara kamar idonta zasu fadi kasa..daidai lokacin shima ya farka tareda dago kanshi a hankali sai yaci karo da nata idon tana hararanshi…baice komai ba ya mike da sauri ya fada bathroom..wanko face dinshi yayi ya fito sai yaga ta hade kai da gwuiwa kamar zatayi kuka…da sauri ya karasa inda take ya zauna nan gefen gadon yana dubanta a hankali yace”what again?..”dagowa tayi tana kallonshi fuska daure tace”ni ka mai dani hostel”..kallonta ya tsaya yi for some secs kafin ya hada hannayenshi waje daya in a pleading tone yace”nace fa am sorry..da gaske bazan kara ba kiyi hakuri plss”..batace komai ba sai juya mishi baya da tayi zata fara hawaye yace”idan Allah noo..please am sorry..ki yafemin”..goge hawayen tayi kafin ta juyo ba tareda ta kalleshi ba tace”to ka mai dani hostel nidai”..yace”zakiyi hakuri ki dena fushi?..”gyada mashi kai tayi..da sauri yace”thank u so much”..tana turo baki tace”kuma kada ka sake tabani nidai”..yace”ban karawa inshaAllah..ki tayani da addu’a”..da mamaki ta kalleshi tace”addu’an me?..”shiru kawai yayi yana kallonta dan baisan yaushe mgnr ya fito ba..a hankali yace”kafan yayi sauki?..”still kai ta daga mishi tana cigaba da turo baki shi kuma sai yayi kasake yana kallonta kaman wani soko..kallonta yakeyi full of love and affection..yarinyar na burgeshi fiyeda tunanin mai karatu..komai tayi burgeshi yake sai yaga tana kyau da duk wani abu da tayi shiyasa yake kishinta sosai…a yanda yake kishinta shi ko cewa za’ayi babu wanda zai na kallonta duk dunia sai shi kadai so zaiyi amma yasan hakan ba mai yiwuwa bane…agogon hannunshi ya duba yaga its almost 12 and Allah ya sani yana tunanin yanda zai maidata hostel cikin daren nan dan yasan Nur da kyar idan ba tafiya yayi ba..dagowa tayi ta kalleshi zata sake mgn wayanshi dake cikin aljihu ya fara ringing..ya zaroshi da sauri ganin Mummy ke kira yayi picking tareda kaiwa kunne..a daya bangaren Mummy tace”kana kina Bobby?..ya jikin nata?..”yace”da sauki Mummy”..tace”ka tabbata da sauki ba wani problem din?..”yace”yes Mummy”..sai kuma ya juya yare zuwa igbo yace mata”Mummy babu mota hannuna and inaso in maidata hostel yanzu..Nur ya wuce tun daxu”..Mummy tace”saidai in turo Sab ya kawo maka..amma why not ka bari ta kwana asibitin sbd a sake tabbatar da samun saukin nata..kuma ga dare yayi”..ajiyar zucia ya sauke yana kallon Aysha da tayi masa kuri da ido tana kallonshi jin ya wani canxa yare cikin ranta tace”dan kyar idan ba gulamana yakeba wlh..inyamurin banza”..ba tareda ya dauke idonshi daga kanta ba yace”bazata yadda ba Mummy..nima kaina ba son zuwa hostel din nasu nake da daren nan ba amma idan ban maidata ba daga min hankali zata yi nasani”..shiru yaji Mummy tayi kafin can tace”ko zaka kawota nan gida ta kwana zuwa safe ka maidata hostel din?..”shirun shima yayi kamar me nazari yace”anya kuwa zata yadda Mummy?..rigima zatai tayi wlh”..dan murmushi Mummy ta saki jin abunda ya fada kafin tace”ba rigiman da zatai inshaAllah..if tana kusa ka bata wayan muyi mgn”..bai sake cewa komai ba ya mika mata wayan yana dubanta a hankali yace”My Mom..wants to..talk to u”..batayi musu ba ta karba tana turo baki tasa wayan a kunne..Mummy tace”daughter ya jikin naji?..”da sauri tayi kasa da kai kmr Mummy na ganinta tace”Mama ina yini”..Mummy daketa faman smiling tace”lafia lau daughter..ya jiki?..”tace”Alhamdulillah”..Mummy tace”MashaaAllah..dama ce mishi nayi ya kawoki gida sbd dare yayi bai kamata yaje hostel dinku yanzu ba..snn ya sake duba kafan naki to make sure ba wani problem kuma..hope bazaki ce aah ba?..”Lamido tayi shiru tana tunanin amsar da zata bata..gani tayi gwara ta kwana gidan nasu akan dai ta kwana asibiti..afterall ba daki daya zasu kwana ba dan haka bazata damu kanta ba…saida Mummy ta sake mgn snn a hankali tace”toh Mama”..Mummy tace”nagode sosai daughter Allah miki albarka..yanxun zan turo Sab da mota yazo ya dauko ku”..Aysha tace”toh”..daga haka kuma Mummy ta kashe kiran..ajiye wayar tayi tana kallonshi kama zatasa kuka tace”shine zaka hadani da mamanka koh?..”murmushi ya saki kafin a hankali yace”am sorry”..turo baki kawai tayi ba tace komai ba..shi kuma sai ya cigaba da kallonta before saying”kinci abinci?..”banza tayi mashi kamar bataji ba..ya sake cewa”Aysher am talking”..nan ma shiru ba mgn dan haka ya dan daga murya yace”Lamidooo”..juyowa tayi a fusace tana kallonshi tace”ni banaso”..kmr wani abun tausayi yace mata”am sorry tou..zakici abinci?..”ta girgiza kai alamar no snn ta sake komawa ta kwanta..shima baice mata komai ba sai kallonta kawai da yakeyi kamar yau ya fara ganinta…after like 20 minutes Sab ya iso asibitin bai shigo ciki ba ya kirashi a waya ya fada mashi ya karaso dan haka ya mike ya isa inda take bayan ya tattaro mata takalmanta dake kasa yace”get dawn mu tafi..ya iso”..ba tace komai ba ta sauka daga gadon ta zura takalmanta snn ta shiga takawa a hankali sbd zafi da taji kafan na mata..daxun da yake kwance take sai bataji ciwon komai ba amma yanxu zafi takeji sosai saidai bai kai na daxun ba tunda tana dan iya takawa…ita ta wuce gaba Bobby na binta a baya har suka fita waje..ko yaya ta danyi kwakwaran mosti sai yaga kaman faduwa zatayi bai dai yi kokarin riketa ba har suka iso parking lot..Sab na hangosu ya fito ya bude musu motar..tana karasowa ya nuna mata front seat yana fadin”sannu”..wani harara Bobby ya sakar masa kafin ya bude back seat ya zurata ciki shi kuma ya shiga front seat din Sab dake murmushi ya shiga driver seat snn ya tayar da motar suka tafi…baya cikakken minti biyu bai juya ya kalleta ba..gaba daya hankali da zuciyarshi suna gareta..gani yake kmr wani abu zai faru da ita idan baya gani shiyasa yake juyawa akayi akayi..Sab dai driving dinshi yakeyi amma a karon farko yau yaga wani irin canji tattare da yayan nashi kuma dukda Mummy bata sanar dashi wacece Lamido a wurinshi ba shi ya gama tabbatarwa kanshi matsayinta sbd wnn special attension da Bobby yake bata bana wasa bane..ba ko wane ordinary mutum ake bama wnn attension din ba sai mutumin da ake mutuwa so da kauna shi kuma ya tabbata Uncle Bobby son yarinyar nan yake…haka har suka karasa gida ba wanda yace tak a cikinsu sai Bobby daketa faman juyawa yana ganin halinda take ciki sai kace wadda take labour…Sab na gama parking ya bude mota ya fita shima Bobby ya fita snn ya zagaye ya bude mata kofa yana dubanta a hankali yace”to sauko”..ba musu ta fito daga motar tana wani dangale kafa kmr mai karaya a jiki..taku daya biyu tayi sai ta koma da sauri ta zauna cikin motar da bai riga rufe kofar ba tana girgiza kai idonta har sun ciko da hawaye tace”bazan iyaba”..kallonta kawai Bobby keyi yana mamakin taki irin nata..durkusawa yayi nan inda kafan nata yake yana kallo shidai baiga wani alamun har yanzu yana ciwo ba tsabar langwai ne kawai irin nata..shi baisan yanda za’ayi duk ranar da akace ga Lamido a labour room ba..kilan saita daga hankalin kowa kafin ta haihu..tunanin haka ya sashi sakin murmushin da bai shirya masa ba kafin ya kama kafan a hankali ya shiga tofa mata addu’a akai ita kuma ta wani lumshe ido tana jin abunda yakeyi…saida ya dauki almost 5 mins yana mata addu’a a kafar kafin ya gama..ya ajiye kafar tareda mikewa yana dubanta yace”to yanxun ki gwada mu gani nasan zaki iya”..ba tace komai ba ta sake sauka daga motar ta shiga takawa a hankali kmr mara laka a jiki..shi kuwa murmushi kawai yakeyi yana bin bayanta cikin ranshi yana jinjina tsananin raki irin nata..yasan da baiyi mata yanda yayi daxun ba da wlh haka zatayi ta zama kafar yana sake rurucewa shi kuma tana daga mashi hankali amma da bai bari raunin da yake dashi yayi tasiri a kanshi ba yayi mata abunda ya kama ta ai gashi yanzu har ta mike tana taka kafar…har suka shiga parlor bai dena kallon yanda take tafia yana sakin murmushi ba..Mummy da Anty Sumy dake zaman jiransu a parlor suna ganinsu duk suka mike aunty Sumy tayi saurin kamota ta karaso cikin parlorn da ita tana cewa”sannu Aysha”..Mummy ma bayan sun zauna tace”sannu daughter”..murmushi kawai Aysha tayi tareda dan dukawa tace”Mama ina yini”..Mummy tayi saurin mikar da ita tana fadin”lafia lau..ya jikin maki?..”kai a kasa tace”naji sauki”..Mummy tace”toh Allah ya kara sauki”..tace”Ameen”..sai kuma ta juya tana gaishe da aunty Sumy..itama ta ansa da ta bayanta ya jiki tace da sauki..Bobby dai na zaune yana kallonsu feeling relieved sbd ganin da gaske jikin nata yayi sauki..shi kanshi yafi son ta kwana a nan din yanda ko wani matsalan zai tashi cikin dare bazai rasa abunda zaiyi ba unlike in tana hostel da bai zama lallai ma yasan halin da take ciki ba..Mummy ce ta dubeshi ganin yanda yake smiling tace”ya jikin naka kaina?..”murmushi kawai ya kara saki maimakon ya amsa mata sai cewa yayi”Mummy ba taci abinci ba”..yana rufe baki Lamido tace”banajin yunwa fa”..Mummy tace”ya kamata kici wani abu kafin ki kwanta..Sumayya shiga kitchen ki hada mata ko tea ne tasha bari na shiga da ita ciki tayi wanka”..Anty Sumy ta mike zuwa kitchen ita kuma Mummy ta kama hannun Aysha suka nufi flat dinta…other bedroom dinta da ba amfani takeyi dashi ba ta shiga da ita ta ajiyeta kan gado ita kuma ta shiga bathroom ta hada mata ruwa mai dan zafi ta fito mata dasu towel da komai da zatai amfani dashi snn ta fito tana dubana tace”toh shiga kiyi wanka zakiji dadin jikin ki”..ba tace komai ba ta mike zuwa bathroom din Mummy tabita da kallo tana murmushi..zuwa yanxu ta tabbatar ita din farin cikin Bobby ce shiyasa a kullum addu’anta bai wuce Allah ya karkato da hankalinta gareshi ba…tana kokarin fita daga sakin aunty Sumy ta shigo da tea da omalet ta ajiye sai kuma ga Bobbyn nan shima ya shigo hankalinshi kan Mummy yace”Mummy batada kayan sawa ko in fita in samu mata wani kayan yanxu?..”kama hannunshi Mummy tayi tana murmushi tace”ka kwantar da hankalinka bazata rasa kayan da zatasa ba a gidan nan”..murmushin shima yakeyi kafin yace”nagode sosai Mummy”..ta sake kama daya hannunshi tace”sai yanxun nake sake tabbatar da cewa my son is in love..Allah ya karkato da hankalinta gareka”..ya rungumeta yana cewa”Ameen Ameen Mummy na..wlh ina sonta sosai..ni kaina bansan irin son da nakeyi mata ba”..shafa kanshi kawai Mummy keyi tana murmushi…Anty Sumy da tun daxun take kallonsu tace”ina ganin wariyar launin fata a gidan nan”..harara Mummy ta wata mata ita kuma ta fita daga dakin tana dariya…Mummy ta dagoshi daga jikinta tace”oya kaje ka samu kayi wanka kaima sai kaci abinci”..baiyi mata musu ba ya juya ya fita daga dakin itama Mummy ta fita don samo mata kayan da zata saka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button