Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Nur na gama parking a kofar gidan uncle dinta ya juya yana kallon Bobby dake zaune baya yace”5 mins na baka kayi round up don na gaji so nake na huta”..harara Bobby ya watsa mashi kafin yace”ba dole ka gaji ba kaje ka dirki rawa kaman ba namiji ba”..banza Nur yayi dashi ya bude motar ya fita ya rage daga shi sai amaryarshi a ciki..a hankali ta dago tana kallonshi shima kallon nata yakeyi suna hada ido ya sakar mata smile dinshi mai kyau yace”I love you”..kai kawai take gyada mishi tana murmushi tama kasa cewa wani abu..kallonshi take kmr yanda yake kallonta..murya can kasa ta kira sunanshi”Partner”..ba tareda ya dauke idonshi a kanta ba yace”yes my partner”..hannu takai ta kama nashi hannayen tana kallon eyeballs dinshi tace”kayi kyau”..murmushi ya saki kafin yace”not as u baby..na tabbata ban kaiki kyau ba”..kallonshi kawai take ta kasa dena murmushi sbd farin ciki..Bobby ya lumshe Ido ya bude kafin ya sake matsawa kusada ita yana cewa”love gobe iyanxu kin zama matata na zama mijinki”..Kai ta sake gyadawa cikeda farin ciki..shi Kuma ya sake lumshe idonshi ya bude tareda daukan hands dinta ya dora chest dinshi har yanxun idanunshi a kanta yace”shknn daga gobe duk abunda naga dama zanyi maki and nobody will asked why?..”gyada kai ta sakeyi babu bakin mgn..shi kuma a hankali ya hada fuskanshi da nata before yacigaba da fadin”i can hold u to my arms..i can hug and kiss u baby..i can even…”bata bari ya karasa ba ta toshe bakin da hannayenta..kmr zatasa kuka tace”partner ba saika karasa ba plss..kunya nakeji”..murmushi ya saki yana girgiza kanshi yace”then kinada babban aiki a gabanki..a very huge one”..janye jikinta tayi daga nashi tana turo baki tace”kuma ni fasawa zanyi”..daria sosai Bobby ya saki tareda janyota ya rungume a jikinshi..soyayyarta yakeji na karuwa cikin heart dinshi fiye da yanda yakeji a baya..Allah kadai yasan yanda yakejin kmr ya janyo gobe sbd a daura mashi aure da ita ta zama property dinshi ko hankalinshi zai kwanta..itama lamo tayi a jikinshi ta lumshe tana shaqan daddadan qamshin da yake fitarwa..lokaci mai tsaho suka dauka a haka gaba daya sun manta da kowa da komai burinsu bai wuce su dawwama a haka ba har mahdi ya bayyana..gaba daya sabon son juna ke sake ratsa zukatansu abun kmr hadin baki..Nur da ya gaji da zaman jiransu a waje daddagewa yayi yayi knocking glass din window aikuwa firgigit suka dawo hayyacinsu Bobby ya raba jikinshi da nata a hankali yana kallon face dinta da tayi kasa dashi tana murmushi…bude kofa Nur yayi tareda lekowa tana kallonsu kmr zaisa musu kuka yace”Lamido a sakar mana shi haka mu wuce dan Allah..wlh na gaji so nake in samu in huta”..kai kawai ta iya gyada mishi tana kokarin kwace kanta a hannunshi amma yaki sakinta..daga Ido tayi tana kallonshi shi kuma ya lumshe Ido tareda pecking forehead dinta snn ya saketa yana cigaba da kallonta with a bright smile yace”good night wife”..juyawa tayi ta fita daga motar da sauri har tana hadawa da gudu.

Wedding Fatiha…

Tun safe both bangarori suka fara shirin daurin aure da za’ayi 11 na safe a nan cikin Lamido’s Palace..Bobby har nafilah saida yayi na nuna godia wa Allah for witnessing wnn ranar in his life and for praying Allah ya basu zaman lafia da zuri’a nagari..ya roki Allah ya bashi ikon riketa Amana ya kuma bashi damar kulawa da ita iyakar karfinshi..addu’a yayi musu sosai yana idarwa kuma ya fada bathroom yayi wanka snn yazo ya fara shiryawa..some of abokanshi da suke tare dashi sai tsokanarshi wai ya cika zumudi shikam saidai yayi murmushi kawai sbd yasan bazasu ta6a ganewa ba..bazasu fahimci abunda yakeji gameda yarinyar ba shiyasa duk suke wnn surutan.
A gidan Waziri ma sun gama shiryawa tsaf Waziri da kaf yayanshi maza da ‘ya’yan ‘yan uwanshi da abokanshi dana yaran nashi kai har ma da jikoki duk sun hallara a gidanshi lokaci kawai suke jira su tafi inda za’ayi daurin auren.
Su Mummy ma suna gida suna nasu shirin don a yau zasu wuce da amarya kano zuwa da yamma suma zasuyi igbo day dinsu a can.

A can gidansu Aysha ma shiri sukeyi sosai tun daga kan daddy da sauran ‘yan uwa da abokan arziki har zuwa kan Lamido da nashi mutanen shima sai kuma Hajia Ammi da familynta..sosai suke shiri don tun yanxu Estate din nasu ya fara cika da mutane from different angles na Nigeria..manya manyan mutane suna nan da yawa wasu jama’ar daddy ne wasu kuma jama’ar Lamido.

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
56
Karfe Sha daya da ‘yan mintina dubban mutane suka shaida daurin auren Attahir Attahir Waziri(Bobby)da kuma Aysha Ahmad Lamido akan mafi karancin sadaki kaman yanda addinin musulunchi ya tanadar…jama’a sosai ta ko ina Estate din ya cika fal tun daga gidan Lamido har zuwa ciki wajen gidan su Aysha mutane ne keta 6ullowa ta ko ina…ango Bobby tunda yaji anyi sanarwar aure ya dauru tsakaninsu shaidu sun shaida kuma an shafa fatiha sai yaji wani irin nustuwa mai hade da kwanciyar hankali sun sauka a zuciarshi..wani irin feeling yakeji irin na wanda ya samu cikar burinshi bayan yasha wahala…mutane sai zuwa suke suna congratulating dinshi dukda hayaniya dake tashi a wurin ga masu algaita suma da suketa faman busa tun kafin a fara daurin auren…a nan cikin Estate din sukayi reception daga nan kuma suka shiga cikin gida don gaisawa da iyaye..har suka gama gaisuwan suka bar gidan Bobby baiga matarshi ba duk sai yaji hankalinshi ya tafi wurinta burinshi kawai ya sanyata a Idonshi..har sun shiga mota zasu koma can gidan dasu Mummy suke don suna can suna jiran dawowarsu wai za’ayi pictures kasa hakura yayi ya shiga Kiran wayanta amma bata dauka ba dan haka kai tsaye yace ma Nur ya kaishi gidan uncle dinta tunda yasan a can take kwana..kallonshi Nur yayi da mamaki yace”seriously..su Mummy na gida suna jiranmu fa snn ga abokanmu da suka fara wucewa can me kakeso muce musu idan suka rigamu zuwa?..”kama hannunshi Bobby yayi suka dan koma gefe ya wani marairaice kmr ba ango ba yace”Nur try and understand mana..zuwa fa kawai zamuyi mu ganta da gaske ba dadewa zamuyi ba”..ajiyar zucia Nur ya sauke tareda komawa ya sallami wasu daga friends dinsu dake jiransu snn ya dawo tareda wasu suka shishshiga mota zuwa gidan uncle din nata gaba dayansu…a kofar gida yayi parking snn ya sake kiran wayanta ganin bata dauka ba ya kira na Billy..sukayi sa’a kuma ta dauka nan yake fada mata sunzo suna kofar gida..wani irin ihu da yaji sun saki ya tabbatar mishi a hands free ta sakashi knn…walida ce ta fito tayi musu iso har cikin parlor..Lamido na zaune sun wani sanyata tsakiya fuskanta a rufe kmr wanda take yin kuka..hankalinshi yaji ya tashi badai yarinyar nan kuka take ba..ganin ya nufo inda take direct duk sauran mutanen da suka zagayeta suka mike daga wurin Bobby na isa ya mikar da ita tsaye kawai ya rungumeta tareda lumshe ido hawaye farin ciki na ciko idanunshi..he can’t believe yau shi aka daurama aure da Lamido..rungumeshi tayi itama sosai tana hawaye sosai kmr Wanda akama auren dole..tunda taji an daura aure jikinta yayi wani irin sanyi data tuna shknn fa yanxu gidansu zata bari gaba daya..tafia zatayi ta bar su Ammi da daddy da Husna da Yusra?..oh Allah ashe haka auren yake?..dukda ta saba tafia ta barsu idan zataje makaranta amma wnn tafian yana da bambanci da Wanda ta sabayi a baya…tafi ta sowar da occupants din wurin suke shi ya dawo dasu hayyacinsu..a hankali ya dagota daga jikinshi yana share mata hawaye gamida girgiza mata kai alamar she should stop..sake 6are baki tayi zata dora daga inda ta tsaya kawai ya hade fuskanshi da nata yana mgn a hankali yace”baby stop..crying..mana”..lumshe ido tayi tana kokarin maida hawayen da suka kasa tsaiwa idanunta..hotuna da videos dai sun shasu a wurin jama’ar dake wurin kowa kokari takeyi ta samu na sawa a status..a takaice dai haka akayi pictures din da za’ayi musu Aysha bata dena kuka ba shi kuma angon nata bai dena aikin lallashi ba..kasa ma tafia yayi wai bata dena kuka ba saida Nur yayi da gaske snn ya samu ya wuce suka tafi..gidan Waziri suka fara zuwa nan ma sukasha hotuna tareda Waziri da uncles dinshi daga nan kuma sukayi can gida inda su Mummy suma suka dora daga inda suka tsaya..karfe biyu da wani abu suka fara shirin tafia kano Wanda zasu dauko amarya already dama sun tafi tun daxun don haka wucewa kawai zasuyi daga nan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button