Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Da dare ya shigo parlon Mummy cikin wani baqin yadi daya haska skin dinshi sosai sai baza qamshi yake abunshi…Mummy da aunty sumy na zaune sai faman listing abubuwan da zasu fara siya na lefe suke don shirye shirye sosai sukeyi na biki da baifi saura few months ba..ya karaso ciki ya zauna yana kallon list din da suke yace”Mummy har yanxu list din bai kare bane?..”Mummy tace”ai list bazai kare ba Bobby kasan sha’ani irin wnn wahala ne dashi..idan ba list din akayi ba sai kaga anxo an manta da wasu abun ba’a siyo ba”..dakatawa tayi tareda dagowa tana kallonshi kafin tacigaba”wait..tun yaushe ma nace ka kawota inason mgn da ita kaki?..”shafa kanshi yayi yace”Mummy ba laifina bane bafa..wai kunya takeji bazata iya zuwa ba”..girgiza Kai Mummy tayi tace”to zan kirata da kaina in fada mata”..mikewa yayi ya zuba hannunshi cikin aljihu yace”zan dan fita Mummy”..Mummy tace”to a dawo lafia”..aunty sumy dake ta sauraronsu tun daxun tace”duk wnn wankan nata ne knn?..”dan 6ata rai yayi yana kallonta yace”ke waya fada maki haka?..ni ba wurinta zanje ba”..aunty sumy ta dago tana kallonshi da murmushi tace”ai ba zama zanyi har sai kazo kace aunty na tafi wajen Lamido snn zan gane wajenta zakaje ba”..zuyawa tayi tana duban Mummy tace”dan Allah Mummy baki lura duk yasa manyan kaya wajenta yake zuwa ba?..”dagowa Mummy tayi tana murmushi tace”nima dai na lura Sumayya..ni bansan yaushe ma ya fara sa manyan kaya ba shida kullum cikin suits yake kaman ba bahaushe ba”..Mummy na rufe baki Bobby daketa faman smiling ya dan kwabe face dinshi yace”Mummy ni ba bahaushe bane mana..am Igbo”..hararanshi Mummy tayi tace”for where?..kai bafulatani ne”..aunty sumy tace”rabu dashi Mummy..kaje ka fadawa Aysha haka kaga idan bata fasa aurenka ba”..murmushi yake yana girgiza kai yace”nasan maganinki ai..babansu Miemie kawai zan kira ince ya dawo daga England ya daukeki ku koma gidanku tunda takura mana kikeyi”..daria kawai tasa tacigaba da aikin gabanta jin ya ambaci baban su Miemie..Mummy ma bata sake mgn ba shi Kuma yayi musu sallama ya fita yanata smiling..da mgn daya yayi maganinsu…yana fita ya nufi motarshi da yasha car wash sai kyalle yake ya bude driver seat ya shiga tareda tayar da ita ya fita daga gidan..these driver dinshi ba karamin hutawa yake ba sbd almost everyday shi yake driving kanshi yanxu especially idan yasan wajenta zaije..shifa gani yake ana daura musu aure ma driver office kadai zan dinga kaishi amma duk wani personal al’amuranshi da kanshi zai dinga zuwa yanayi ko don sbd matarshi..shi bazai iya bari driver ya tuka mashi mata ba har ga Allah..kawai gani yake zaiyita kallonta ne ta mirror shi kuma da wani namiji ya kalleta gwara shi a kwana ana kallonshi bai damu ba…driving yake yana murmushi gami da shafa Kai sbd tunowa da ita da yayi..har kullum sonta karuwa yake a cikin ranshi musamman yanxu da yake receiving equal treatment daga wurinta..daxun rigima sukayi sosai sbd tayi mgn a sauko musu da biki tace bazata iya ba shine yayi zucia har ya baro school din bai nemeta ba yasan tana can ta cika fal tana jiran yaje ta sauke mashi…har ya isa college dinsu bai bar tunawa da ita yana murmushi ba..daidai gate dinsu yayi parking snn ya dauki waya yayi dialing numberta don ko sanar da ita zaizo baiyi ba..tana dauka ko jira tayi mgn baiyi ba yace”baby am outside”..ta wani hade rai ita bata yadda ba ya 6ata mata rai tace”ni banida lafia”..murmushi yakeyi yace”eyya meya sameki?..”a shagwabe tace”fever”..yace”alright let me come inside in dubaki”..tun kafin ya rufe baki tace mishi”nidai No..salon ka shigo duk suyita kallonka”..yace”then indai bakiso in shigo ki fito..na baki 3 mins idan ban ganki ba am coming inside”..daga haka ya kashe wayar yana cigaba da murmushin wnn rigiman nata…suna gama wayar ta juya tana kallon Billy dake kunshe daria tace”munafuka”..daria Billy ta fashe dashi harda su tafa hannaye tace”munafurcin me Kuma nayi Lamido?..”harara ta watsa mata tareda mikewa zuwa wardrobe dinsu ta dauko zumbulelen hijab ta dora kan jean da Jessy dake jikinta as always snn ta fita daga dakin bayan ta Maka ma Billy harara..ita dai da kallo ta bita tana cigaba da murmushi tace”wai Ina matsayin matar yayanta takemun wnn iskancin..Lamido Allah ya shiryeki”.
Tana fita Kai tsaye inda ta hango motarshi ta nufa..shi Kuma yana zaune ciki yana kare mata kallo don wurin akwai haske dal kmr ba dare ba..hijabinta yakai qasa amma Saida ya fahimci jean da riga ne a jikinta sbd fitowa da wandon yayi ta kasa..lumshe Ido yayi ya bude tareda jingina kanshi da kujera yana cigaba da kallonta har ta iso inda yake..ta bude motar ta shigo snn ta maidashi ta rufe tanata wani ciccin magani ta juya tana kallonshi..murmushi ya Kara saki tareda kama both hands dinta ya rike yana kallon eyeballs dinta yace”menene?.”turo baki tayi tace”Pogba”..idanu ya ware da kyau a kanta cikin mamaki yace”Pogba Kuma?..”Kai ta daga mishi akamar eh nan take kuma ranshi yaji ya 6aci..shi duk tunaninshi sbd ya wuce bai nemeta bane daxun take fushi ashe abun nata ne ya motsa bai saniba..sake hannunta dake cikin nashi yayi snn ya sake dubanta cikin kokarin 6oye 6acin ranshi yace”what about him?..”a dan fusace tace”wai mutumin nan mu zai wani tozarta ya bar Manchester United..kasan yanxu wai Juventus…”bata samu sararin karasawa ba sbd wani kallo da ya shiga binta dashi ita sai yanxu ma ta tuna ashe fa tayi kato6ara..innalillahi wainna ilaihi rajiun ta fada cikin ranta..”wane ruwa na kuntowa kaina ni Aisha?..”ta fada a hankali yayinda take kallon yanda yanayinshi ya sauya lokaci daya..dunia idan akwai abunda ya tsana bai wuce wnn Pogban ba..ya tsaneshi to the extent that yakejin duk wani dan Manchester da Yan ball din ma kaf ya tsanesu..dukda cewa shi Pogban musulmi ne amma da gaske tsanarshi yakeji sbd wnn son da yaga tana mashi.. marairaicewa tayi sosai kmr wadda ke dab da fashewa da kuka tace”partner am sor”..bata karasa ba ya dora finger dinshi kan lips dinta yana kallon cikin Idonta yace”u don’t have to apologize”..girgiza kai ta shigayi tana kallon 6acin rai Karara kan fuskanshi tace”nidan am sorry plss..wlh mancewa nayi”..baice mata kala ba ya dauke finger dinshi daga bakinta tareda komawa yayi relaxing kan seat din da yake..hankalinta taji ya tashi sosai tasan duk yayi irin wnn fushin da ita to abu ba karamin 6ata ranshi yayi ba..shaf mancewa tayi da wnn kishin nashi wlh da bata ma fara ambaton Pogba a gabanshi ba sbd yanda ya tsaneshi..matsawa tayi jikinshi sosai tareda Kai hannu ta kama left hand dinshi murya can kasa tace”partner”..banza yayi mata baice komai ba..ta sake cewa”partner talk to me manaa..nace am sorry fa”..still baiyi mgn ba sai ma hannunshi daya zare daga cikin nata ya shiga kokarin bude motar zai sauka kawai yaji ta rungumoshi ta baya tana cewa”partner am so very sorry plss..am sorry I hurt u amma ba da gangan nayi haka ba kasan I love u”..lumshe Ido Bobby yayi yanajin heart beat dinshi na sauyawa lokaci guda..kawai sai yaji wasu irin abubuwa sun shiga zagayawa cikin jini da tsokar jikinshi baisan lokacida ya sauke wani gauron numfashi ba..yana jinta a jikinshi yaji duk 6acin ran nashi yayi disappearing sai Kuma wani shauki daya tsinci kanshi a ciki na musamman…tunda yake da ita bata ta6a hugging dinshi haka ba sai yau..this very moment..wani additional sonta yaji yana sake ciko zuciarshi kawai sai ya juya tareda dagota daga jikinshi yayi cupping fuskanta yace”Love why plss..why do u always wants to talk about him..why do u love him this much?..”hannu takai itama tayi cupping nashi face din tana girgiza mashi Kai tace”I do not love him..I love u..only u baby..I love u more than any other person in this whole wide world..u are my soul partner,my future husband,my babies daddy and I love u so much”..sbd tsabar jin dadin kalamanta baisan lokacida ya sake maidata jikinshi yana sauke ajiyar zucia da mugun karfin gaske ba..wani irin sanyin dadi yaji yana ratsa zuciarshi tamkar an sauke mashi mountain daga ciki..these words means the entire world to him..it means a lot to him and he wouldn’t mind tacigaba da fada mashi irinsu daga nan har mahdi ya bayyana..kawai baiso ta dena fada ba..sai yaji kaman su dawwama nan wurin tana fada mashi the most sweetest words daya taba saurara all his life..rumgumeta yayi sosai sai sauke numfashi yake kafin ya dagota a hankali yakai lips dinshi ya manna mata peck a forehead dinta yana kallonta wearing a very wide smile kan fuskanshi yace”I love u more baby..I love u like…”kasa karasawa yayi sbd gani yake babu wata kalma da zatayi daidai da son da yakejin yanayi mata a mizani saidai in zuciyarshi zai bude mata ta shiga ta gani kawai idan ba hakaba duk yanda zaiyi bayani bazata ta6a ganewa ba..hade fuskanshi yayi da nata idanunshi rufe yace”I beg u in the…”bata bari ya karasa ba itama ta dora two fingers dinta akan lips dinshi tana kallonshi tace”I promise not to talk about him ever again..am sorry”..sake rungumeta yayi yana sauke ajiyar zucia..bayan few minutes ya rabata da jikinshi yanata doka murmushi ya kalleta kafin yayi mgn tace”I love u”..ya lumshe Ido ya bude shima yace”I love u more baby..and ba na hanaki fitowa da wando ba?..”kallonshi tayi ta kalli jikinta tanaso taga ta Ina ya gane wando ne a jikinta amma bata ganiba don hijabinta ya rufe har kasa ne.. dan marairaicewa tayi tana dubanshi tace”partner naga ba wani wajen zanje ba ai..wajenka zanzo”..yace”ko wurina ban yadda kina zuwa anyhow ba manaa.. don’t u know u have this beauty and figure da bai kamata kina fita da anyhow dressing ba?..”langa6e Kai tayi a hankali tace”to kayi hakuri na dena”..sake pecking goshinta yayi tareda komawa seat dinshi ya zauna yana cigaba da kallonta with a smile yace”thank u so much love..I love u”..murmushin takeyi itama kafin tace”I love u more”..girgiza kai yayi yana kallonta yace”no I love u more”..itama ta makale shoulder dinta tace”nima I love u more”..murmushi kadai Bobby keyi ya kasa dena kallonta..itama kallonshi takeyi this time around ba tareda wani tsoro ko fargaba ba..bayan almost 10 mins of silence and starring yace mata”Mummy nata damuna fa in kaiki wajenta..yaushe zaki shirya muje?..”dan karya wuta tayi tana dubanshi har yanxu tace”partner kunyanta nakeji nidai”..yace”then kiyi mgn da Billy kuje tare amma da gaske Mummy tace she wants to see u..kilan akwai abunda takeso kuyi discussing da ita”..gyada mishi kai tayi a hankali alamar ta amince.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button