Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Daya da mintina bakwai Motan daddy ya shigo cikin haraban makarantan…wani taro ne ya kawoshi kano shine yaga before ya wuce Gombe ya kamata yazo ya ganta dan ya kwana biyu bai zo ba..ko sanar da ita zuwanshi baiyi ba sbd yanaso yaga how she’s doing a school din…dama duk zai zo bai ta6a sanar mata ba saidai kawai ta ganshi kwatsam yazo…dagashi sai driver dinshi da security guda daya…bayan sunyi parking yace da security yaje bakin gate ya tambayi masu gadi ko zasu santa dan yanata kiran wayanta bai shiga gashi kuma baiga student ko daya a premises din ba ba mamaki suna clesses dinsu…da hanzari security ya tafi bakin gate kamar yanda aka umarce shi ya tambaya ko sunsan Aysha nan sukace mai basu santa ba and abun bai sani ba shine idan zai shekara yana tambayan Aysha zasuce mishi basu santa ba because ba wanda ya santa da Aysha a cikinsu…ko yan class dinsu mantawa suke sunanta Aysha sbd yanda sunan ya 6ace 6att kowa yake kiranta da Lamido…komawa yayi ya sanar dashi sunce basu ganeta ba dan haka daddy ya bude mota ya fito yana karema premises din kallo still trying her number wai zaici saa ya sameta yanxu…daidai wnn lokacin motan Bobby ya shigo haraban school din…gefen motan daddy driver yayi parking nashi snn ya bude mishi mota ya fito…tun daga cikin mota yake kallon wnn mutumi that kana ganinshi zaka gane babban mutum ne kuma mai dattako yana tunanin me yazoyi college dinshi kuma?…har zai wuce office dinshi yaga kaman bai dace ba..bisa ga dukkan alamu mutumin wani yake nema duba da yanda yaga yanata kokarin kiran waya kuma bata shiga…juyawa yayi zuwa inda suke yana tafiya a nutse kaman yanda ya saba har ya karasa inda suke…fuska dauke da murmushi dan haka nan yaji mutumin ya mishi wani irin kwarjini yace”sorry to interrupt sir..are u looking for someone?..”murmushi daddy ya saki tareda mika mashi hannu alaman suyi musabiha yace”yarinyata nazo gani wlh kuma inata kiran wayanta baya shiga”…Bobby da yaji nauyin ya bashi hannu su gaisa yace”if babu damuwa mu karasa office dina sai insa a nemo maka ita”..daddy ya fadada smile dinshi lokaci daya yaji yaron ya kwanta mishi a rai yace”ba damuwa muje”…Bobby ya wuce gaba shi kuma yabishi baya..security dinshi zai biyosu yayi mishi alaman he should stay…suna zuwa office din ya bude suka shiga still yana murmushi ya nuna mishi sofa yace”Bismillah sir”..ba musu daddy ya zauna yana sakejin yaron na burgeshi sosai…shi kallon sani ma yake mishi sai yaga kaman ya ta6a ganinshi a wani waje…Bobby ya bude fridge ya dauko ruwa da lemo ya ajiye mishi kan table snn ya zagaya seat dinshi ya zauna ya dauki landline dinshi yace”ya sunan yarinyar da za’a kira sir?..”daddy bai maji me yace ba as hankalinshi gaba daya yana ga katon picture din Bobby dake manne a wall din office din…fuskanshi dauke da suprise look ya juya yana kallonshi yace”u mean kai son din Col Attahir ne?..”Bobby yayi shiru yana kallonshi da mamaki shima…daddy ya sake juyawa ya kalli pic din snn ya kuma juyowa gareshi har yanxun cikeda mamaki yace”ina nufin Col Attahir Waziri na Gombe..are u his son?..”a hankali Bobby ya gyada mishi kai alaman yes…wani irin bright smile ya gani shimfide kan fuskan daddy wanda ke nuni tsantsan farin cikin haduwa dashi…juyawa ya sakeyi ya kalli hoton then back to Bobby kafin yace”ikon Allah…kasan mahaifinka shine sanadiyyar matakin da nake kai a yanxu?..he was a very good and generous man..my mentor…har yanxun banida wani abun kwaikwayo kamanshi…he was a very kind hearted person..a very responsible person..”ya karasa mgnr da wnn bright smile kan face dinshi sai kuma eyes dinshi dake nuni da tsananin kewarshi da yaji sakamakon tunawa da mutuwarshi da yayi…Bobby dai mutuwan zaune yayi sai kallonshi kawai yakeyi kaman statue…wani irin qima yaji
mutumin ya sakeyi a idanunshi…kawai yaji yana sonshi sbd wnn maganganu da yayi kan dad dinshi…a rayuwa yanason ya hadu da mutumin da yasan babanshi ba don komai ba sai don kawai yayita bashi labarinshi yanajin dadi amma banda familyn dad din nashi…su wadan nan ko zasuyi me bazai iya yadda wani alaqa ya sake shiga tsakaninshi dasu ba…bayan few minutes of silence daddy yacigaba da cewa”no wonder tun a kallon farko da nayi maka naga kaman na sanka…its because kana kama da dad dinka sosai and ba iya kamanninshi kawai ka dauko ba harda halayenshi…kawai daga gani na kaji ya kamata ka taimakamin har ka kawoni office dinka without knowing who i am and wnn na daya daga cikin halayen mahaifinka…bai ta6a ganin wani na bukatar taimako bai taimaka mishi ba…ubangiji Allah ya jikanshi yasa yana aljannah”…Bobby ya lumshe ido sbd dadin addu’ar da yaji a hankali yace”Ameenn”…daddy ya zuba ruwa a cup yasha snn yace”kasan sa akwai alaqa ta sarauta tsakanin shi mahaifinmu Lamido da kakanka Waziri..wnn dalilin ne yasa dana fara aikin Custom aka hadani da mahaifin naka”…kallonshi kawai Bobby keyi yanajin dadin labarin…shi daddy yacigaba da fadin”kacigaba da irin wnn habit din yanada kyau kaji?..Allah ya maka albarka”…yana murmushi ya amsa da”Ameen..nagode sir”..daddy yace”no thanks a tsakaninmu…u are like a son to me”…sake murmusawa Bobby yayi yana shafa kanshi…tunda yake bai ta6a cin karo da mutumin da ya kwanta mishi a rai ba kaman wnn mutumin ba..da ganinshi mutumin kirki ne and he ha so much respect for him..baisan ko sbd yasan dad dinshi bane oho amma yaji yana ganin girmanshi sosai…saida ya sake daukan landline snn yace”Sir baka fadi sunan yarinyar ba”…murmushi daddy ya kuma saki yace”kaga har na manta da ita sbd tunowa da Mentor na da nayi…May his gentle soul continue resting in peace”..sake lumshe ido Bobby yayi tareda cewa”Ameen Ameen”..daddy yace”sunan yarinyar Lamido…Aysha Ahmad Lamido”…idanu a waje sosai Bobby ya dago yana kallonshi jin sunan daya ambata…he can’t believe wnn responsible mutumin shine zai haifi wnn fitinanniyar yarinyar…ganin irin kallon da yake mishi daddy yace”do u know her in any way?..”da sauri ya shiga girgiza kai yace”ah no sir..bari insa a nemota”…daga haka ya kira secretary dinshi using the landline…tana dauka yace tazo yana son ganinta…bayan ta shigo yace mata”did u know a girl called Lamido?..”secretary ta danyi shiru for the mean time kafin tace”yea na santa sir..mai kukan allura kou?..”banza yayi kaman baiji me tace ba yace”kije midwifery section ki nemota..tell her that her father is here waiting for her”..secretary ta amsa da”ohk sir”..snn ta juya ta fita daga office din…daddy ya bita da kallon jin tace mai kukan allura…knn hakan na nufin Aysha har a nan dinma kukan alluran take?..kawar da tought din yayi ya juya ga Bobby yace”kanada sister sumayya koh?..”gyada kai Bobby yayi yace”yes my elder sis”…murmushi daddy ya kuma saki yace”a lokacin bazan manta ba inajin sunanta a bakinshi…yanaji da kids dinshi sosai dan koda yaushe cikin mgnrku yake…and kanada brother mai sunan Waziri kou?..”nan ma kai ya sake dagawa yace”Sabeer”…daddy na cigaba da murmushi as old memories rush back yace”ina tunawa da sunanku ai..he was man of the people shiyasa duk na kasa dashi suke sonshi sosai”…gyada kai kawai Bobby yake yana murmushi…he doesn’t want the conversation to end.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button