Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Sorry for the late update pls..kunsan sallah ya kusa so ina can ina kujiba kujiba????

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
51
Washegari da around 4 ya gama shiri tsaf don zuwa daukosu kamar yanda sukayi da ita jiya..tun daxun yake tsaye gaban mirror sai faman kalkale yakeyi kamar mace..wayanshi ne ya shiga ringing yana dubawa yaga Rayhan kan screen dan haka ya saki tsaki tareda ignoring call din har ya gama ringinshi dinshi bai dauka ba..wani kiran ya sake shigowa still bai dauka ba yana gama ringing ya dauki wayan da nufin sawa a silent sai kuma kiran Nur ya shigo..fasa sawa silent din yayi tareda answering call din yana cewa”what?..”daga daya 6angaren Nur yace”dole kace haka mana dan rainin hankali kaman ba kaine Lamido tayita ladabtar mana da kai ba”..tsaki Bobby ya saki yana ta6e baki yace”is this why u called?..”da sauri Nur yace”no plss..ina cikin matsala ne wlh almos similar to wanda ka shiga a kwanakin baya and i need ur help”..ajiye comb dake hannunshi yayi tareda daukan keys dinshi ya fita daga dakin kafin yace”then ka bari idan hadu gobe sai muyi mgn amma ba a waya ba”..yana rufe baki Nur yace”no plss nidai kayi alqawari zaka taimakamin”..dan girgiza kai yayi yana mamakin wnn sudden behavior na abokinshi yace”wai kayi gamo ne hala?..wane irin alqawari zan daukan maka kuma?..”Nur yace”alqawari dai kmr yanda kaji na fada”..gyada kai yayi yace”then nayi alqawari shknn?..”Nur yace”shknn sai munyi mgn tomorrow”..yace”ohk”..snn ya kashe wayar yana girgiza kai..wani lokacin Nur sai yayita behaving kaman wani karamin yaro wlh..kai tsaye yana fita parlon Mummy ya shiga yayi sallama da ita snn ya fita don zuwa dauko su Aysha daga hostel..yana hanya ya kira ya sanar da ita tahowarshi don haka kafin ya karasa sun gama shiryawa tsaf shi kawai suke jira..bayan ya isa ya sske kira ya sanar mata ya iso basu 6ata lokaci ba suka fito tareda Billy..relaxing yayi nan cikin mota yana kare mata kallo as usual duk yazo wurinta dama kafin ta isa gareshi sai ya gama kalleta tsaf shiyasa ko hijab tasa yake iya gane abunda take sanye dashi ta ciki..doguwar riga ne a jikinsu iri daya saidai color daya banbanta amma daidai da hulunan dake kansu iri daya ne likewise takalmansu..ya fuskanci qawance ne tsakaninsu na gaske bana wasa ba and suna son juna tsakani da Allah ba wani mai zucia biyu a cikinsu..kafin su karaso as usual ya bude mata front seat suna karasowa ta shiga Billy kuma ta shiga backe seat bayan sun rufe kofa ya sake tada mota suka bar cikin hostel din…suna daukan haya ta juya tana kallonshi da wani smile daya kusa sashi zubar dasu a titi sbd tsabar rikitashi da yayi tace”partner kayi kyau”..kallonta ya danyi sai kuma ya saki murmushi yana cigaba da driving dinshi ita baima san yanda zai bayyana irin kyawun da tayi mashi bane..kawai shidai baison tana yin shiga irin haka tace zataje wani wurin amma bazai iya hanata ba yau tunda anko yaga sunyi ita da Billy amma ko Allah yasan shidai baso yakeyi ba..sam baison tana fita babu hijab sbd yanda yake ganin kmr idanun kowa kanta zasu dawo don a ganinshi babu namijin da zai kalleta baiji ta birgeshi ba ko don kyawun fuskarta ko kuma surar jikinta…dan turo baki tayi tana kallonshi tace”bazaka ce nima nayi kyau ba koh?..”juyawa yayi ya kalleta for like 2 secs kafin ya sake maida hankalinshi ga driving da yakeyi yace”kinyi more than kyau”..harara ta dan watsa mashi alaman bata gamsu da abunda ya fada kuma har yanxu bata bar turo mishi baki ba..Billy dake sauraronsu tana murmushi tace”sir ina yini”..kallonta ya danyi ta mirror kafin yace”lafia lau Bilkisu meyasa bakiyi mata fada ne?..”Billy tace”Allah inayi mata sir kawai dai halin nata ne sai ita..batajin mgn wlh”..tana rufe baki Aysha ta juya tana kallonta tace”kiji tsoron Allah wlh..haka kikaje kika hadani da Ammi ma kikasa taitamun fada ba tareda laifin komai ba”..murmushi kawai Billy tayi batace mata komai ba shima murmushin yayi hade da girgiza kai ba tareda cewa wani abu ba..ganin yanda suka maidata kamar wata yar iska tayi mgn sunyi banza da ita sai taja bakinta ta tsuke itama tana harare harare ita a dole anyi mata ba daidai ba..har suka isa gida ba wanda ya sake mgn cikinsu..ciki ya shiga yayi parking kmr ko yaushe snn Billy ta fara budewa ta fita don ta basu space..itama tana kokarin budewa ta fita ya kama hannunta da sauri yana langabar mata da kanshi yace”bana hanaki fitowa a haka ba?..”langabar da nata kan tayi itama kafin tace”kaga anko fa mukayi da Billy ai babu dadi ince mata bazan sa ba”..janyota yayi jikinshi sosai yana kallon eyeballs dinta yace”sai kice mata na hanaki fita a haka ai zata fahimta amma kin kama kin fito a haka yanxu Allah kadai yasan adadin mazan da zasu kalleki kafin mu koma”..kallonshi take a hankali tace”partner kaima fa dan bakaga kyau da kayi bane nima sai ince mata zasuna kallonka mana”..hannunta ya kama ya dora saitin heart dinshi yace”ko sun kalleni it won’t change a thing sbd my heart beats for only u and u alone..i don’t think har dunia ta tashi zan samu macen da zan sota kmr yanda nake sonki..ina sonki sosai nefa..try and understand mana”..kallonshi kawai Aysha keyi tana sakin murmushi cikin ranta kuma tana godia wa Allah daya bata shi a matsayin miji..dukda basu riga sunyi aure ba tana da tabbacin za’a jima ba’a samu macen da tayi dacen miji dake sonta irin yanda yake sonta ba..soyayyanshi is genuine wanda ta tabbata yafi wanda ita take mashi nesa ba kusa ba…ganin kallon da take mishi tana smiling ya dan hura mata iska a ido yana kallonta yace”what are y thinking about?..”a hankali tayi pointing nashi da finger dinta tace”you”..kallonta yayi kafin ya samu damar cewa wani abu yaji saukan warm lips dinta akan forehead dinshi ta manna mishi kiss that last for almost 3 mins kafin ta janye bakin a hankali tareda bude motar ta fita tana sake kasheshi da wnn smile din nata…Bobby mutuwan zaune yayi a wurin yana bin bayanta da kallo har suka shiga cikin gidan itada Billy..lokaci guda moo dinshi ya sauya gaba daya sai kace wanda yasha wani abun…wnn kiss da tayi mashi ba karamin hargitsa mashi lissafi yayi ba..jikinshi ya mutu murus wanda hatta numfashi da kyar yake shaqansa..lumshe ido yayi tareda komawa yayi relaxing kan kujera yana sauke ajiyar zucia..wani irin yanayi yakeji tattare dashi wanda yafi duk wanda yasan yanaji a baya..jikinshi yayi sanyi qalau da har ya kasa daga legs dinshi balle ya samu ya fita daga motar..haka yake fama da wnn desire din these days ko kallonta ya fiye yi saiya samu matsala ballantana kuma yanxu da tayi mashi abunda bata ta6a yi mashi ba tunda suke tare..kawai addu’a yake Allah yasa bata ta6a yiwa wani namiji haka ba don a yanda yakeji tsaf zai iya kauce hanya sbd yanda dan abu karami daga gareta yake kai mishi karo..effect sosai wadan nan abubuwan suke dashi a kanshi wanda ya zama mishi dole yayi baya baya da ita don gudun kada azo ana samun matsala..saida ya gama tattara sauran energy dinshi kaf snn ya bude motar ya fita yana takawa a hankali ya nufi cikin gidan..a central parlor suke zaune da Mummy da friend dinta maman Rayhan sai kuma Rayhan din dake zaune gefen Mom dinta tana karema su Aysha dake gaisawa da Mummy kallo…karasowa cikin parlon yayi a hankali bayan ya daure fuska ya shiga gaida Mom din Rayhan kafin itama Rayhan din ta mike da sauri tana kallonshi da wani murmushi tace”Uncle Bobby sannu da zuwa..tun daxun nake jiranka”..kai kawai ta iya gyada mata yana satar kallon Aysha da ko ba’a fada ba yasan kallonsu take..Mom dinta na murmushi itama tace”tun tuni take damuna da mgnrka Bobby kusan kullum haka zamu yini tana kiran Uncle Bobby shiyasa yau dai nace bari mu samu muzo dan ni kaina rabona da mahaifiyarka tun bikin Zahraddeen”..murmushin yake ya iya saki yana gyada kai duk yabi ya diririce sbd presence na Aysha a wurin..Mummy ma ba karamin kunya maganganunsu suka bata ba gashi ta rasa yanda zatayi tayi stopping nasu don haka da sauri tace”to ka wuce ciki idan mun gama gaisawa sai ka maidasu”..kmr abunda yake jira knn ya kama hanyar flat dinshi da sauri..Itama Rayhan da saurin ta mike tabi bayanshi tana cewa”Mommy bari inyi mgn dashi plss”..daga haka itama ta shiga flat din nashi..Mummy ta juya a hankali tana kallon Aysha data kasa jurewa ta shiga binsu da kallo har suka shiga flat din nashi kawai saiji tayi hawaye sun ciko idanunta..wnn kuma wace irin masifa ce?..da sauri tayi kasa da kanta tana kokarin maida hawayen da suka ciko mata ido amma Mummy ta riga ta gani and hakan kuma ya bala’in tada mata hankali..kada fa yaran nan suzo suna samun matsala ta dalilin wnn abun..mikewa tayi da nufin binsu flat din nashi sai ga Miemie da aunty sumy sun shigo parlon tareda ilham da alama unguwa sukaje…Miemie na ganinsu ta karasa kusa dasu da fara’arta tana gaishesu haka ma ilham da hugging Aysha saida tayi sbd farin cikin ganinta..ganin haka Mummy ta dubi aunty sumy dake gaisawa da Mom din Rayhan tace”wuce dasu parlonki su samu su huta kafin na shigo”..ba musu aunty sumy ta kwashesu zuwa flat dinta tareda su Miemie da suketa murna kamar basu ta6a ganinta ba..Billy dai sai kallonsu takeyi tana sake yabawa da kirki irin nasu..ta tabbata Lamido ba karamin dacen samunsu matsayin dangin miji tayi ba basuda matsala ko kadan..Lamido kuwa ji take kaman ana hura mata wuta a cikin jikinta sbd tsabar zafin da taji ya rufeta..ita bataso suka bar parlon ba so tayi su zauna taga iya tsahon lokacin da zasu dauka a dakin nashi basu fito ba..har wani jiri taji kaman zai dauketa sbd tashin hankali..bata ta6a sanin haka takeda kishi ba sai this very moment..kawai ayyanosu takeyi wai suna can suna abunda bai kamata ba kilan ma har kissing juna zasuyi and iya tunanin haka kadai yasa ta kware da yawun bakinta nan take kuma tari ya sarketa kmr zata shide..Miemie daketa faman zuba ma Billy surutu hankalinsu yayi kanta gaba daya suka shiga kokarin taimaka mata..aunty sumy ta dauko ruwa da sauri ta kawo musu Billy ta amsa ruwan ta bata a baki tasha sai kuma tarin ya sake karuwa sbd another kwarewa da tayi da ruwan data sha din..nan take hawaye suka shiga kwararowa fuskanta wanda ko kusa bana kwarewa da tayi bane kawai na ciwon ganin wata mayya tareda namijin da duk dunia batada kamarsa a yanxun idan aka dauke iyayenta…yayi mata ciwo sosai yanda yarinyar ta iya binshi har flat dinshi kuma bai koreta ba..da sauri aunty sumy ta dauko waya ta shiga dialing number dinshi sbd batason dagawa Mummy hankali tunda tana tareda bakuwa..kamar jiran kiran nata yakeyi yana dagawa tace mishi”come to my parlor plss..ur Aysha bansan meya sameta ba”..ai tun bata kai karshe ba ya katse wayar tareda fitowa zuwa flat din nata da sauri..tana shiga yayi toxali da yanda take shaqan numfashi da kyar baisan lokacinda ya karasa tareda zaunawa nan kusa da ita ba..yakai hannu yana kakarin janyota jikinshi da karfi tace”don’t..touch..me”..tsayawa kawai yayi yana kallonta kmr bai gane me tace ba..hannu ya sake kaiwa zai zare nata hannun data rufe hanci da bakinta dashi still ta sake cewa”i said don’t touch me”..kama hannun nata yayi ya janyeshi daga fuskar ita kuma ta daddage ta make hannun nashi tana wani sauke numfashi tana muzurai tarin kuma sai ya tsaya cak kmr dama dai zuwanshi yaje jira..kallonta ya shiga da puppy eyes dinshi ita kuma ta dauke kai tana kokarin maida hawayen da suke sake ciko mata idon..kawai gani take kilan ya dade yana raina mata hankali akan yarinyar…aunty sumy da batasan dawar garin ba sakin baki tayi tana kallonsu da mamaki haka ma su Miemie..kallonta yayi yana marairaicewa yace”aunty kice tayi hakuri plss”..yana rufe baki itama tace”aunty baimin laifin komai ba”..galala aunty sumy ta tsaya tana kallonsu da sabon mamaki..Bobby ya kori su Miemie da yaga sun wani tsaresu da ido kafin ya sake maida dubanshi ga aunty sumy da ido ya shiga yi mata alamar ta rokar mishi ita aunty sumy kawai tasa daria..daria suka bata daga shi har Ayshan wlh..idan akace kuruciya na damun mutum dai sai a hankali wlh..juyawa tayi da nufin ta basu wuri suyi rigimarsu su gama Mummy ta shigo parlon hankalinta gaba daya kan Aysha tace”daughter meya sameki?..”dan murmushi ta kakalo kai a kasa ta girgiza kai alamar ba komai..Mummy tayi shiru tana kallonta kafin tace”to ku taso mu koma parlor tuna baqin sun tafi”..mikewa sukayi ba musu suka sake komawa wancan parlon..shidai Bobby har yanxu hankalinshi bai bar kanta ba…bayan sun zauna Mummy ta danyi kasa da muryanta tace”kiyi hakuri da abunda ya faru kinji?..ba abunda kike tunani bane”..kai kawai ta iya gyadawa Mummy amma Allah kadai yasan me takeji..Allah Allah take kawai su tafi yanda zata samu wankeshi tas da soso da sabulu..nasiha sosai Mummy ta shiga yi musu wanda duk akan abunda ya faru ne tana sake assuring dinta cewar ba komai ba wani abu ne tsakaninta da Bobby ba amma kishi ya rufe mata ido kwata kwata bata yadda ba kawai gani take itama Mummyn yana raina mata hankali ne kmr yanda itama ya raina mata kilan yana soyayya da ita a bayan idanunsu..idan ba haka ba why zai bata such freedom?..why zata samu damar binshi har flat dinshi kuma ba tareda wani shakku ko tsoro ba idan har ba soyayya suke ba?..a takaice sun 6ata lokaci sosai Mummy nata faman musu nasiha ko dalilin da yasa tace tana son ganin nata ma bata fada mata ba..shidai Bobby yana zaune yana kallonta yasan duk wnn 6a6atun da Mummy take da kyar idan tanaji don a yanda yake ganin fuskanta kadai ya isa yasa yasan yau fa mai rabata dashi sai Allah…bayan ta gama musu nasihan da suka zo tafia har ita akayi musu rakiya bakin mota su A’i sai yake ake ana washe hakora irin komai normal din nan nan kuwa basu san ta ciki na ciki ba..ta bude front seat ta shiga Billy ta shiga back seat kafin shima ya shiga ya tada motar su tafi gabanshi har wani faduwa yake sbd tunanin yanda zaiyi ya fitar da kanshi daga wnn gundumemen zargi…har suka isa hostel babu Wanda yayi mgn cikinsu..ita Billy tana zaune back seat tana danna waya yayinda Lamido da Bobby ake kallon kallo a tsakanin juna shi yana tunanin yanda zasu kwashe da ita yanda yaga tana hade rai ita Kuma tana tunanin Kalan rashin mutuncin da zata mashi sbd raina mata hankali da yayi…yana gama parking a gate din hostel Billy ta bude motar ta fita bayan tayi sallama dashi ta shiga cikin hostel din shi Kuma ya juya a hankali yana kallon Aysha data shiga kici kicin bude motar zata fita amma yasa lock don haka ta kasa budewa..matsowa yayi yana dubanta a hankali yace”baby listen to me plss..I will explain”..tun bai rufe baki ba ta kama masa wani kallo Idonta har ya ciko da hawaye tace”ka cuceni”..juyawa tayi zata fita yayi saurin janyota ya sakata jikinshi murya can kasa yake ce mata”am sorry..am so sorry ki bari inyi maki bayani plss”tureshi ta shigayi tana dukan chest dinshi da duk karfin da Allah ya hore mata ta kasa cewa komai..ganin ba sakinta zaiyi ba kawai ta sake kankameshi tana fashewa da matsanancin kuka..kishi takeji sosai na wnn shegiyar inyamurar yarinyar..bata ta6a sanin kishi bala’i bane sai yanxu..knn shima haka yayita ji duk lokacinda yake ganinta tareda wani?..idan haka ne ma yayi kokari sosai dan ko Allah ya San ita bai zama lallai ta iya irin wancan hakuri da yayi da ita a baya ba..wani irin zafi takeji tamkar an dau zuciarta ansa shi cikin frying pan ana soya mata shi…Bobby dai banda shafa bayanta ba abunda yakeyi..bashi yake kukan ba amma zai iya rantsuwa yana jin sautin kukan da zuciarshi takeyi sbd nata kukan da takeyi..hankalinshi tashi yakeyi sosai..yasan yanda mutum keji idan irin wnn kishin ya motsa and ko kadan baya mata fatan sake experiencing wnn feeling din sbd yasan exactly how it feels..ba fatanshi ta dena kuka kadai ba fatanshi kada Allah ya sake kawo dalilinda zai tada kishinta haka sbd ciwo yakeji idan yana ganinta a irin wnn halin..he loves her to the extent that duk wani abu da zai daga mata hankali baya son yazo kusada ita..gashi dai yanxu ita take kukanta amma yanda yakeji yasan ko ita dake kukan bazata kaishi shiga damuwa ba…dagota yayi a hankali yana share mata hawaye gami da girgiza kai shima kmr zaisa mata kukan yace”stop crying plss..nace maki ba wani abu nefa tsakanina da ita ba”..ture hannunshi tana sauke ajiyar zucia sbd kukan da taci ta sake juyawa zata bude motar yayi saurin dawo da ita yana kallon tsakiyar idanunta a hankali yace”please!..please I beg u”..lumshe Idonta tayi tana goge hawayenta shi Kuma ya matsa jikinta sosai har suna shaqan numfashi juna yace mata”when i say u i mean u baby..only u..duk dunia idan kina tunanin akwai wata mace cikin rayuwata apart from u then u are mistaken..I love only u and u alone..you are the best of all the precious things that have ever happened to me..you owns my heart completely and I love u so much..please allow me to explain things to u”..tunda ya fara mgn kawai ta lumshe Ido tana sauraran yanda yake pouring mata love words din nan ya kamata taji dadi amma Sam kishin dake cinta ya hana mata jin dadin kalaman nashi..kawai imagining take dama sun dade tana shiga flat dinshi kilan har ganinshi ta ta6ayi babu kaya ajikinshi..tunanin haka yasa ta sake kwa6e fuska hade da tale baki zata fara kuka kawai taji saukan warm and cute lips dinshi akan bakinta..ta kwalo idanuwa waje da sauri tana rarraba su kmr dai shege a rabon gado..lokaci daya ta hadiye kukan nata tsaf ta zuba ma face dinshi Ido yanda ya lumshe nashi idon yayi holding dinta da two hands dinshi makes him loos so cute a Idonta..lumshe idon ta sakeyi tanajin yanda ya kasa raba lips dinshi da nata ga heart dinshi dake bugawa very fast kawai saita daddage iya karfinta ta janye bakinta daga nashi tana sauke numfashi…bata sake yadda ko kallon inda yake tayi ba ta bude motar ta fita da sauri har tana hadawa da gudu…Bobby ya dafe head dinshi tareda hada Kai da starring yana sauke numfashi da sauri kmr Wanda yayi tsere..lokaci daya regretting abunda ya aikata ya shigeshi..baisan yanda akayi har hakan ya faru ba kawai shidai yaji bakinshi cikin nata anda daga nan Kuma bai sake tantance komai ba sai abunda yakeyi…shknn yanxu kilan kallon dan iska zata fara mishi amma ba laifinshi bane..Allah ya gani he tried his best abun ne yafi karfin tunaninshi..shi da yake kokari bata hakuri ya sake aikata wani laifin da kilan sai yasha wahala kafin ya damu kanta again…lumshe Idonshi yayi yana furta”innalillahi wainna ilaihi rajiun”a hankali..gaba daya yama kasa tashi balle ya tayar da motar ya tafi..driver dinshi ya kira da kyar yayi mashi bayanin inda yake yace yazo yayi picking dinshi..babu wasting of time yazo wurin Bobby ya bashi keys tareda komawa back seat shi Kuma driver ya tashi motar suka tafi bayan yace gida yskeso ya kaishi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button