Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Wahsegari ta tashi normal babu fever as usual dama kullum kalau take tashi da safe sai dare yake sake dawowa..da kanshi ya mata wanka ya bata one of three quarters dinshi ta saka da wata shirt dinta dake dakin nashi snn ta fito zuwa wurin su Billy..da mamakinta sai taga suma sun tashi itada Yusra har ma sunyi wanka sun shirya..zama tayi suka fara labari kafin Kuma daga baya tace su shiga kitchen su fara girki don yau dai ba bazata bar Mummy da sawa ayi musu girki ba tunda ta samu sauki.. tare suka shiga kitchen din da Billy Yusra kuma suka barta a nan parlor tana kallon cartoon..Billy ce ta shiga peeling Irish yayinda ita kuma Aysha ta dauko chicken a freezer ta shiga gyarawa zatayi musu pepper soup..karnin Kazan na bugun hancinta taji wani irin amai ya taso mata aikuwa ta matsa jikin sink da sauri ta shiga kwarara aman..Billy ta bar peeling Irish da takeyi ta karasa nan kusada ita tana mata sannu..bayan ta gama ta bata ruwa da kuskure bakinta snn taja stool ta zauna tana maida numfashi..Billy dake murmushi tun daxun ta karasa ta dauki Kazan ta shiga wankewa tunda ta gama gyaran tace”ohh Allah da iko yake”..a kule Lamido ta juya tana kallonta tana daure fuska tace”ban gane ba”..Billy ta gama wanke kazar tasa ruwa snn ta dora a kan gas ta zuba duk abunda ake buqata snn ta rufe tukunyar ta koma kan Irish tacigaba da ferewa ta kuma kasa dena murmushi..ganin yanda taki kulata tace”Billy wai meye haka?..”Billy tace”kici gaba da 6oyemun kinada ciki nima ramawa zanyi wlh”..shiru tayi kmr bazata ce komai ba sai kuma can tace”shi ya fada maki koh?..”Billy tace”wlh ba wanda ya fadamun..bayan duk wnn fever da amai da kikeyi still sai inyi zaune sai wani ya fadamun kinada ciki kmr dai ba health personell ba..have u forgotten am a registered midwife?..”Aysha ta dan saki murmushi tana cewa”to registered midwife munafuka”..Billy ta shiga wanke Irish data gama peeling tace”ba wani munafurci fa.. addu’a na ya karbu knn”..tana rufe baki Aysha tace”wlh ke kimamun baki muguwa.. inshaAllah kema yanda bakinki ya kamani sai nawa ya kamaki..ke preterm ma zaki haifa inshallah 7 months da biki kawai saidai Muji ance kin haihu”..Billy ta kwashe daria tana cewa”aikam bakinki saidai ya tsaya kanki inshaAllah”..Lamido tace”idan na fara labour zan roka maki tunda kinsan ance adduar mace mai labour karbabbiya ce”..Billy tasa daria..haka dau suka cigaba da aikinsu suna hira kmr wanda sukayi jiya bai ishesu ba..Bobby dai ko da ya fito yana jiyo sautin dariarta a kitchen tayi Hamdala dan yasan tunda yaji haka sauki ya samu knn.

Karfe 11 suka gama shiryawa bayan sunyi sallama da Mummy suka shiga mota zuwa gidan aunty sumy kmr yanda Aysha ta dage ma Bobby kan sai ya kaisu sun gaisheta..ita da Billy da Yusra suna motarshi yayinda Husna da Miemie suke motar Nur da sai wani giggiwa yake yau gashi ga pretty a mota daya..sai kuma abun ya hadu da Husna mai shegen rawar kai itama aikam baka sukaita zuba masa iyayi yana kallonsu da murmushi yana kuma mamakin wnn iyayin da suke dashi a shekarun nan nasu…aunty sumy ta karbesu hannu bibbiyu ta dinga nan nan dasu kmr ta maidasu ciki don so..sosai suma suka ware suka saki jiki da ita suka kwashi labari don itama ba daga baya ba wajen surutu..Nur ne kadai ya kasa sakewa duk yajishi a takure sbd nauyinta da yakeji yayinda ita kuma ko a jikinta don batasan ma yanayi ba..Bobby banda tsokanarshi ba abunda yake yana masa daria amma bai kulashi ba sbd baida lokaci tanka mashi tunda a gidan surkai yake..sun jima sosai a gidan don a nan sukayi lunch daga nan kuma suka mata sallama suka wuce bayan ta cika su Billy da gifts iri iri..basu zame ko inaba daga gidan nata sai wani park mai kyau..sunyi enjoying wajen sosai don sai after four suka bar wajen..daga nan kuma ya kaisu shopping yace kowa ta dauki abunda takeso..su Husna an samu abunda akeso nan aka shigo kwasan kaya kmr wanda zatayi changing wardrobe..Billy dai kasa daukan komai tayi sai Lamido ce ta daukan mata snn ta dauka ma Yusra..har su Ammi saida yace ayi musu tsaraba dan haka sukayi spending lokaci mai tsayi a nan cikin mall din basu gama ba..bayan sun bar wurin yanaso ya biya eatery suyi takeaway na abinci Mummy ta kira tace he shouldn’t buy food that already an gama preparing musu dinner..haka suka koma gida sukayi dinner din a nan zuwa lokacin Aysha dauriya kawai take don abokin daren nata ya fara dawowa wato fever amma bata bari sun gane ba har suka gama hiransu snn suka wuce tareda Yusra da Billy kmr dai jiya Husna da Miemie Kuma suna gidan Mummy.

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank State…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
68
Washegari around 2 Hamma Najeeb yazo ya daukesu suka wuce bayan sunyi sallama da Mummy da kuma Aysha da taci kuka ta koshi kmr idan sun tafi bazata sake haduwa dasu ba..sosai takejin zatayi kewarsu..Mummy da Bobby sun cikasu da tsaraba sosai na abun arziki haka suka tafi suma sunajij kewarta kaman yanda itama takejin nasu..Yusra har kuka saida tayi wai zata zauna tareda Adda amma haka nan ba yanda suka iya suka rabu suna kewar juna.

Laulayi sosai Aysha ke fama dashi dan tun zazzabin yana tashi da dare har saida abun ya dawo kusan ko yaushe akwai fever jikinta ga kuma ba dama taci abinci sai ya dawo kmr zata fitar da kayan cikinta..sosai take shan wahala cikin lokaci karami ta rame tayi wani irin haske fau wanda kana gani dama zakasan ciki ne daita..Bobby kullum yana tareda ita dan zuwa yanxu ko hospital bai fiye zuwa ya dade ba sbd yanda hankalinshi bai kwanciya idan baya tareda da ita..ko abinci bata iyaci saidai taita kame Kamen kwadayi amma abincin kirki dai bazata tsaya taci ba sai idan jan ido yayi mata..sosai shima take bashi wahala dan gani yake ko ita da cikin ke jikinta bazata kaishi shan wahala ba..kullum fatanshi shida Allah ya rabata da cikin lafia don sosai ya matsu yaga ya rike da ko ‘yarshi..wani lokaci sai ya zauna yayita surutu shi kadai wai babynshi yake mgn..ko Kuma yakai kunnenshi cikin nata wai yanaso ya jiyo heartbeat din babyn..sosai yake kulawa da ita da kuma cikin dake jikinta don duk wani abu da mai ciki ke buqata yana mata likewise wanda ba’a buqata ya nesanta ta dashi..lokacin da cikin ya isa antenatal da kanshi yake zuwa hospital da ita yayi mata duk wani necessary abu snn suje ayi mata duk tests daya kamata..scanning ma da kanshi yake mata don haka nan ma wani lokaci zaice suje yayi mata scanning yanason yaga ya kwanciyar babynshi yake..haushi yake bata sosai idan taga yana wnn abubuwan don gani take duk ranan da ta haihu kilan dena ma kulata zaiyi ya koma kan babynshi..tana ganin abubuwa iri iri dai akan wnn cikin ba daga Bobby ba ba kuma daga Mummy dasu Hajia Aunty Sumy ba..har kunya suke bata idan sukayi wani abu akan cikin amma su ta fuskanci ko a jikinsu..koda yake zuwa yanxu ta riga ta gama gane cewa jinin igbo dake running a jikinsu shike haifar musu da wnn rashin kunyan dan abubuwa da yawa idan sukayi saidai ta tsaya tana kallonsu tunda hausawa dai da Fulani tasan bazasu iya rabin rabin abunda sukeyi ba..tun cikin nada 3 months suka fara siyan kayan baby suna ajiyewa daga shi Bobbyn har zuwa kan su Mummy ta kasa gane Wanda zafi zakuwa da haihuwarta..yanda suke tulan kayan suna ajiyewa kai kace a kanta za’a fara haihuwa duk dunia..kulum cikin browsing unisex kayan yara suke designers masu kyau wai they don’t want the baby to lack wani abu a dunia..kulawa sosai take samu ta kowane bangare amma hakan bai hanata wani lokaci ta sanyashi gaba tana kuka wai itadai ya cuceta musamman yanxu da cikin ya fara girma sai yasa mata wani irin qiba kusan duk kayanta sunyi mata kadan saidai taita fama da dagayen riguna…gashi mugun kunyar cikin takeji shiyasa ko Ammi ta kasa fadawa saida wasu sisters din daddy sukazo suka ganta da cikin shine da suka koma suka cema Ammi sai ta fara shirin tarban jika..sosai Ammi tayi mamakin wai Aysha nada ciki amma ta kasa fada mata dan dai ta Santa da rashin kunya kilan dai hankali ta farayi shiyasa ta kasa fada ma kowa kuma wai har uwar tata Fiddausi bata fadama ba lallai Aysha ta fara hankali kam..cikinta nada wata shidda aka sanya bikin Hamma da Billy four months masu zuwa aikam tasha takaici sosai wai ba’a tashi sa ranar ba saida aka daidaici lokacin haihuwarta sbd baaso taje biki..Billy taita mata daria tana tsokanarta wai Kilan lokacinda za’a fara bikin ita tana cikin labour room tana fama da kanta hakan kuma ba karamin bata ranta yakeyi ba dan har kuka saida tayi da akace four months aka saka.
Wnn knn…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button