Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
36
Matron da Billy ne suka fara shiga dakin snn Nur shi kuma Bobby ya shiga daka karshe…har lokacin bata dena sakin ajiyar zucia cikin baccin da take yi ba…a hankali ya karasa inda take hannayenshi zube a aljihu ya tsaya kusada gadon yana kallonta tun daga fuskanta da yayi jaa as a result of kukan da tayi har zuwa legs dinta da rigan jikinta ya danyi sama kadan sai fair skin dinta daketa glowing…kallonta kanta yayi shima ya ganshi a bude duk gashinta a waje kawai sai yaji ranshi ya baci..kan wane dalili zasu barta a haka tunda sunsan zasu iya shigowa har inda take..kawai sun bar jikinta da gashinta a bude gashi nan Nur yana ta kallo abunshi..kallon Billy yayi da face dinshi dayaji kaman shi yake daure kanshi da kanshi a takaice yace”batada hula ne?..”da sauri Billy tace”sir da kanta ta cire wlh..wai bazata iya bacci dashi ba”..yana sake dinke fuska yace”shi kuma jikinta da kuka bari a bude fa?..”kallon jikin nata tayi da sauri tanaso taga inda suka bari a buden sai taga rigan ta ya danyi sama..batace dashi komai ba ta karasa ta janyo mata rigar har kasa snn ta dauki hulanta data yar nan kasa shima ta shiga kokarin zurawa a kanta daidai lokacin kuma ta dan bude ido snn ta sake mai dashi ta rufe..Billy na gama sa mata hulan takai hannu zata cire murya a cushe Bobby yace”idan kika cire hulan nan sai ranki ya 6aci wlh”..bude ido tayi da sauri tareda mikewa zaune tana kallonshi…ta dauka a mafarki taji muryanshi amma sai taga da gaske shi din ne a gabanta..to me kuma ya kawoshi bayan abunda ya gamayi mata daxu..daure fuskanta tayi ta wani kauda kai gefe tana harare harare..shima ya daure nashi fuskan dan yasan idan ba haka yayi mata ba tsaf zata sake cire hulan ta bar gashi a bude tunda ba hankali ne ya isheta ba..Nur dai na tsaye gefe yana kallon ikon Allah..mamaki yake na ganin yanda Bobby ya wani hade rai yana mata fada kaman ba shine yake kokarin sa mishi kuka ba daxun sbd ita ba..wato har yanzu dai wnn ki fadin nashi yana nan baije ko inaba..idan ba haka ba why kaida ke dab da shiga matsala sbd son yarinya kuma still kanada kafin hali daure mata fuska haka…karasawa yayi ya durkusa nan kusa da ita yana kallon legs dinta dake nan kan gadon yanaso ya gane wadda take ciwon a ciki amma ya kasa..daga ido yayi ya dan kalleta sai kuma ya kawar da kan nashi jin wani bakon abu dake zagayawa cikin jikinshi..duban nashi ya maida ga Billy kafin yace”wanne kafan ne yake ciwo?”..a hankali tace mishi”na dama”..bai sake cewa komai ba ya juya yana kallon kafan damar nata..ganin bai ganin komai sai yakai hannunshi a hankali da nufin ya dago kafan Aysha ta saki wani irin kara tana fadin”Noo”..kallonta kawai yayi baice komai ba sai kuma ya mike still yana duban Billy yace”ki bata hijab tasa muje asibiti”..wara idanu Aysha tayi jin abunda ya fada idonta har ya cicciko da hawaye tace”nidai bazanje asibiti ba wlh..ni bazaa yi mun allura ba banaso”…kallon Nur Bobby yayi cikin sigar ka taimaka mun…Nur ya saki murmushi tareda karasawa inda take yace”Lamido ba allura za’a maki bafa..duba kafan kawai za’ayi ko da akwai matsala ta ciki”..yana rufe baki tace”nidai dan Allah banason zuwa sir..bazan iya takawa ba”..kallonta kawai yakeyi rungume da hannu ita kuma sai tayi kasa da ido tana goge tears dinta tace”to zanje..amma dan Allah banda allura wlh ciwo yakemun”..Nur yace”baza’ayi maki allura ba inshaAllah..yanzu matron da Billy zasu taimaka maki ki mike tunda bazai iya tafiya ba”..batace komai ba sai hawaye data cigaba dayi..tsoro takeji kar suje suyi mata allura ita dai..a muguntan Dr Bobby tasan wlh da kyar idan baiyi mata allura ba tunda baida imani…Billy ce ta dauko hijab ta saka mata snn suka kama hannunta itada matron din don fita da ita waje…taku daya ta iyayi ta saki wani kara da saida Bobby yaji shi har cikin zuciyarshi…nan da nan saiga hawaye a fuskanta ta shiga kokarin durkushewa nan kasa sbd azabar zafi da taji har cikin bones dinta…girgiza kai kawai take murya can kasa tace”bazan iyaba”..kallonta duk suka tsaya yi harda Bobby da yakejin kukan nata har can cikin ranshi..ji yake kamar yaje ya sungumeta yayi waje da ita amma ba halin yin haka…sai da kyar da taimakon Billy suka samu ta yadda ta mike suka riketa har zuwa inda sukaƙi parking…kafin su karasa Nur ya bude musu kofa dan haka suna zuwa suka Sanya ta ciki Billy ma ta shiga suma suka shiga snn Nur ya tada motar suka tafi…Bobby dake zaune front seat jingina kanshi jikin kujeran yayi tareda lumshe idanu..jin kukan nan nata yakeyi har cikin zuciyarshi yayinda wani irin zafi da kunchi suke sake rufe shi..Allah kadai yasan yanda yakeji nunawa ne kawai baiyi amma yana cikin matsala gagaruma ma kuwa…kasa cigaba da hakuri yayi ya juya yana kallon yanda take rikeda kafan tana kuka..murya can kasa yace”kukan ya isa haka dan girman Allah”..ko kulashi ba tayi ba ta cigaba da kukan ta…a takai ce har suka isa Freedom bata bar kuka ba…Bobby duk ya rikice ya tasa inda zai tsoma kanshi yaji dadi..Nur na gama parking duk suka bude mota suka fito banda ita da ko motsawa ba tayi ba…Billy ta zagayo ta bude mata kofa tareda kamo hannunta tace”ki daure mu karasa ciki”..rike hannun nata tayi snn ta sakko da kafan a hankali sai kuma ta gagara mikewa..Nur dai na tsaye yana kallonsu shi kuma Bobby ganin sake bata musu lokacin take kawai ya karasa wurin baiyi wata wata ba ya daga ta cak ya nufi cikin asibitin da ita..sai ihu taka tana ita ya sauketa amma ko tanka mata baiyi ba har ya karasa office dinshi su Billy na binsu a baya..Nur ya karasa ya bude office din suka shiga..kai tsaye ya direta kan gadon dake nan cikin office din fuskan nan a daure kamar bai taba dariya ba…yana ajiye ta ya bude wani drawer ya dakko wani muscle pain killer ya ajiye kan trolley snn ya shiga bathroom ya zuba ruwa cikin wani bowl mai zurfi ya hada da towel dan karami snn ya dawo dakin..daga Nur har Billy kallonshi kawai suke ba wanda yace kala..kujera ya janyo ya zauna nan kusada ita snn ya zaka towel din cikin lukewarm watare daya debo ya matseshi snn ya kama kafan nata ya rikeshi da kyau yanda bazata iya kwacewa ba ya shiga danna mata towel din a wurin..banda ihu da musu mutsu ba abunda take amma ta kasa kwace kafar daga hannunshi sbd rikon da yayi mata bana wasa bane..danna mata kawai yakeyi ba tareda ko kallonta yayi ba sbd gudun abunda hakan zai haifar mashi..yasan idan ba haka yayi mata ba ba bari zata yi ayi mata abunda ya dace ba and Allah ya sani bazai taba samun sukuni ba idan ba gani yayi kafan nata ya warke gaba daya ba..idan zai biye ta zuciyarshi nan ma bazai iya mata abunda ya dace ba kuma shidai akan ya bari wani ya tabata gwara shi yayi mata duk abun daya kama ta idan yaso daga baya sai yayi aikin rarrashi dan dai yasan rigima ne zai sashi kamar ba gobe..tunda ya fara bai saurara mata ba sai da ya tabbatar kafar ya gasu snn ya kyaleta..ya dauki towel da bowl din ya maida su bathroom ya dawo sai kuma ya dauki maganin da zai shafa mata a kafar yana kallonta..kuka take yi sosai har numfashinta na seizing kamar zai dauke..ga wani uban zufa data hada sharkaf kaman wanda aka gasata a oven..tausayinta yaji ya kama shi ganin yanda take kuka yasan dole zataji zafi amma ya zaiyi?..shima ba a son ranshi yayi mata haka ba babu yanda zaiyi ne kawai..janyo kujeran yayi a hankali ya zauna still yana kallonta duk sai yaji ya kasa aikata komai..juyawa yayi ya kalli Nur wai ko zai taimaka mashi amma sai yaga shi dariya ma yakeyi abun shi sai kuma ya juya ya fita daga office din…Billy ma ba tayi wata wata ba tabi bayanshi don Allah ya gani bazata iya zama nan ciki ba…juyawa yayi yana kallonta suna hada ido ya dauke nashi da sauri ya shiga matsa maganin a hannunshi..sam baison wnn raunin dake kokarin dakatar dashi ne…runtse ido yayi ya bude snn yayi watsi da raunin dake dake kunno mishi kai ya kamo kafan nata a hankali zai shafa maganin kawai sai yaji ta kanakameshi tana sakin wani marayan kuka..lumshe ido yayi yanajin wani irin yanayi a cikin jikinshi…wani irin weird feeling da bai taba tsintan kanshi ciki ba..cikin muryanta da bai fita sosai tace”sir dan Allah..dan Annabi kayi hakuri”…lumshe ido ya sakeyi yanajin zuciyarshi na wani irin tattarewa ya cunkushe can wuri daya yana bugawa da mugun karfi…a hankali yakai hannunshi ya zagaye bayanta dasu bakinshi saitin kunnenta yace”am..sorry..plss”gyada kai kawai takeyi tana cigaba da kuka tace”toh bazaka shafamin ba koh?..”dagota yayi daga jikinshi yayi cupping fuskanta yana kallon cikin idonta yace”hakan bazai yiwu ba Aysher..kiyi hakuri a shafa maki ko yayane zakiji sauki”..girgiza kai ta shiga yi tana cigaba da hawaye tace”dan girman Allah No..mutuwa za..”bata karasa ba ya rufe mata bakin yana girgiza kai duk ya gama goge maganin hannun nashi a jikinta…kamata yayi ya kwantar da ita kan gadon snn ya sake matsa maganin a hannu yayi saurin kama kafar ya shiga murzawa a hankali..banda kuka da ihu ba abunda Lamido take har wani shidewa take sbd azaba shi kuma bai saurara mata ba saida ya tabata maganin ya shiga ciki snn ya ajiye kafar..har yanzu kuka takeyi tana sauke ajiyar zuciya shi kuma ya kama hannunta a hankali ya sake cewa”am..so..sorry love”..ko sauraranshi ba tayi ba ta kwace hannunta tana cigaba da kuka shi kuma yayi tagumi kawai yana kallonta..Allah kadai yasan yanda kukan nan nata ke daga hankalinshi..ita kanta da tasan yanda yakeji idan tanayi da batayi ba ko dan sbd shi…haka yayita kallonta tana kuka da yayi yunkurin taimaka mata zatace bataso..duk tabi ta sake daga mishi hankali da kukan nata..saida bacci ya dauketa snn ya sauke ajiyar zuciya..mikewa yayi daga inda yake zaune ya leka ya tabbatar baccin tayi da gaske snn ya gyara mata kwanciya a hankali yanda bazata tashi ba..lumshe ido yayi yakai lips dinshi forehead dinta ya manna mata peck a hankali murya can kasa yace”get well soon love..i love you”..daga haka ya gyara mata kafar snn ya janyo kujeran dab da ita ya zauna tareda rike hannunta cikin nashi ya dora kanshi gefen gadon shima daga haka bacci ya sadado yayi awon gaba dashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button