Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Kwananshi biyu a asibiti aka sallameshi a ranar kuma ya dage sai sun wuce kano waziri yace bazasu tafi a ranar ba.. dole suka bari the next day shima kuma bada son waziri ya bari suka tafi ba..ba yanda zaiyi ne kawai sbd yanda yaga Bobby ya daga hankalinshi ne amma da bazai bari su tafi ba musamman daya kasance har yanxu ba gama warkewa yayi ba…shi kuma yayi hakan ne sbd yanaso ya nesanta kanshi da ita and hakan bazai yiwu ba don idan yana Gombe jin kanshi yake yana kusa da ita amma idan ya koma kano zai samu sauki ya sani…idan ta dawo college kuma tsaf zai iya dena shiga makarantan ma gaba daya balle watarana ya ganta abunda yake kokarin 6oyewa ya tona masa asiri…da wnn shawara na zuciyarshi yayi na’am ya kumayi tawakkali tareda mika lamuranshi ga Allan don yasan shi kadai yakeda ikon canxa al’amura a lokacinda yaso.

Kwana biyu da tafiyarsu Aunty Munubiya da bata koma tare dasu ba ta shirya ta tafi gidan Uncle Lukman wanda yake mazaunin babba cikin ‘ya’yan waziri tunda shi yakebin mahaifinsu Bobby…bayan sun gaisa dashi ya shiga dubanta da alamar tambaya yace”Munubiya lafia kuwa naganki gidane irin wnn lokacin?..”cikeda damuwa tace”wlh ba lafia ba Yaya Lukman..mgn ce nazo da ita akan Bobby”..shiru yayi yana kallonta kafin yace”to meya faru?..”a nutse ta shiga koro mishi bayanin kaunar da yakema jinin Lamido da yanda sukaje tareda Waziri akan batun neman aurenta sai kuma sukaji Lamidon da bakinshi yace ya riga ya tsayar mata da miji…tunda ta fara bayani yayi shiru yana sauraronta baice komai ba saida ta kammala yace”to yanxu me kikeso ayi Munubiya?..da bakinki fa kikace Lamido ne yace ya mata miji kuma a yanda nasan Lamido dai zaiyi wahala yayi mgn ya canxa musamman mgnr aure”…yana rufe baki tace”na sani amma bai kamata mu nade hannu mu kasa yin komai matsayinmu na ‘yan uwan mahaifinshi ba…so nake dan Allah yaya Lukman kaje ka samu mahaifin yarinyar nan in person ka nuna bakasan da waccan mgn ta Lamido ba kace nemawa Bobby auren yarinyar kazoyi wata kila zai iya cewa ya hadaka da Lamido..daga nan nasan shi kanshi Lamidon zai sake nazari musamman idan ya kasance yarinyar ba son wancan auren take ba..ko don alaqar dake tsakaninshi da Waziri nasan zai iya janye waccan mgn da yayi”…shiru Uncle Lukman ya sakeyi yana sauraronta…tabbas gaskia ta fada amma shin zai iya kuwa?..gani yake kmr zasu fahimci drama suka shirya musu tunda ai Lamido yasan Waziri yasan da mgnr amma meye abunyi?.Allah ya sani shi kanshi yaji yana son taimakon yaron ko don ya samu damar goge tarin laifukan daya aikata musu a baya ciki harda kin amincewa ya nemosu bayan rasuwar mahaifinsu…yayi nadama sosai yanxu ya kuma ji gaba daya ahalin Attahir sun shiga ranshi matuka ko don sbd yanda basu nuna wani alama na har yanxu suna rike dasu ba dukda yasan zaiyi wahala ace sun manta duk abubuwan da suka aikata masu a baya…ganin yanda yayi nisa cikn tunani Aunty Munubiya ta sake lankwasa murya tace”dan Allah yaya Lukman ka taimakawa yaron nan a matsayinka na qanin mahaifinshi…ko don zumunchi ka daure kayi hakan bakasan tarin ladan da zaka samu ba”…ajiyar zucia ya sauke kafin yace”shknn zanje inshaAllah..zan fara bincikawa inji yaushe Ahmad din yake gida sai inje in sameshi”..nan take Aunty Munubiya ta shiga washe baki tana cewa”Allah ya saka da alkhairi yaya..Allah kuma yasa muji alkhairi”..shima yana murmushi yace”Ameen..duk yanda mukayi dashi zakiji”..tace”to shknn yaya..bari inzo in tafi Allah ya saka da alkhairi”…ya amsa mata da Ameen snn tayi mishi sallama ta tafi..cikin gida ta shiga wurin matarshi itama tayi mata sallama snn ta koma gidan waziri don gobe take shirin komawa kano itama dama ga dalilinda ya tsayar da ita nan.

Washegari around 4:30 Uncle Lukman ya iso gidansu Aysha bayan sunyi mgn da daddy ya tabbatar mashi da cewa yana gida…daddy ya bude kofar parlonshi ta waje ya shiga dashi nan ciki suka fara gaisawa…bayan gaisuwa kai tsaye Uncle Lukman ya fadi mgnr dake tafe dashi saidai bai 6oye mashi komai ba har yanda Lamido sukayi da waziri kan batun aurenta da Najeeb da kuma yanda shi Bobbyn ya shiga wani hali sbd jin mgnr auren nata…bayani sosai yake mashi dalla dalla kaman yanda ya samu labari wurin Aunty Munubiya…daddy kuwa rsabar mamaki kasa kwakwaran mosti yayi a wurin…gaba daya kanshi ya kulle knn all these while yaron nan yana sonta bai ta6a nunawa ba?..tausayinshi yaji ya kamashi matuka yaji inama yanada hanyar dazai taimaka mashi da yayi haka..inama ikon bayar da aurenta a hannunshi yake da ya bashi ita ko bataso saidai mgn a hannun Lamido yake ba hannunshi ba…har Uncle Lukman ya gama bayani tareda rokon idan akwai taimakon da zai iyayi don a samu sauyin al’amura ya taimaka yayi ko don a ceto rayuwar yaron…hankalin daddy ya tashi sosai ya kumaji tausayinshi ya kamashi fiyeda tunaninshi…yasan yaron baida matsala sam and yanada duk wani quality da iyaye ya kamata su duba wajen za6ama yaransu miji kuma zaifi kowa son ace ya hada jini da Mentor dinshi Col Attahir saidai hakan da kmr wuya tunda bai zama lallai Lamido ya tankwaru ba…hakuri yaba Uncle Lukman sosai tareda alkawarin zaiyi bakin kokarinshi yaga abunda Allah zaiyi saidai suci gaba da addu’a…har ya tafi daddy bai dawo cikin hayyacinshi ba…mamaki kawai yakeyi da har yake mata so irin wnn kuma ya iya 6oyewa har na tsahon lokaci haka…sosai yaji yana son hada zuri’a dashi a daya bangaren kuma yana tunanin shima Najeeb din idan sonta yakeyi fa?..itama kuma Ayshan wanda takeso daban shikam ya zaiyi ya kwance wnn kullin ne?..ya zaiyi ya daidaita al’amuran nan?..”kira Najeeb din zakayi ka tambayi ko shima yanada wadda yakeso”..amsar da wani sashe na zuciyarshi ya bashi knn nan take kuma yayi na’am da ita dan haka ya dauki waya ya dannawa Najeeb din kira yace lallai lallai yanason ganinshi idan ya dawo daga office.

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata yafitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
45
Da dare misalin karfe takwas Najeeb yayi sallama parlon daddy kmr yanda yace yazo yana nemanshi…ya karaso ciki ya gaisheshi kafin a hankali ya kira sunanshi”Najeeb”..kai a kasa ya amsa da”Na’am”..daddy yace”tambaya ne nakeson yi maka amma inaso kayi alqawarin zaka fadamun gaskia”..still kanshi na kasa yace”nayi alqawari daddy”..daddy yace”so nake ka fadi tsakaninka da Allah kana son Aysha ko baka sonta?..”shiru Najeeb yayi kai a kasa as tambayar ya masa nauyi sosai..taya zai kalli tsabar idanun mahaifinta yace ba son aure yake mata ba..kai abun da kmr wuya…daddy kmr yasan tunanin da yakeyi knn yace”ka daukeni matsayin mahaifinka ba mahaifin Aysha ba..wata mgn aka zomun da ita mai girma wadda nake sa ran zata iya sa Lamido ya janye mgnr hada aurenku amma fa idan baka so..matukar kana so to ka fada nayi maka alqawarin ko bata sonka zata aureka”..kanshi ya sake dukarwa kasa murya can kasa yace”ni ba son aure nake mata ba daddy…sonta nake tamkar wadda muka fito ciki daya”..wani ajiyar zucia da baisan daga ina ya fito daddy ya sauke cikeda jin dadin wnn amsa ta Najeeb..yanxu dai yasan baya sonta sbd haka zai kai mgn direct to Lamido yaga ko Allah zaisa a dace…nan take ya sallami Najeeb ya tafi tareda ce mishi idan bukatar sake nemanshi ya taso zai kuma nemanshi…haka ya tashi ya wuce yana mamakin wane mgn ne yace ya taso mai girma kuma?..fatanshi dai Allah ya dorasu akan Lamidon ya bar kowa ya auri wanda yakeso.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button