Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Ita kuwa Aysha office din da aka fara posting dinsu taje nan ta samu sauran colleagues dinta a wurin kowacce an sallameta an kuma yi mata signing… daga nan aka basu certificate shknn aka sallamesu kowa ta kama gabanta…ita da Billy tare suka fito zuwa parking lot amma basuga motan Sa’eed da yace zaizo daukansu ba…suna kokarin zama sai gashi nan ya karaso dan haka suka karasa inda yayi parking…ko a hanya Aysha kasa 6oye excitement dinta tayi Billy sai tsokanarta take wai daga yanxu tanayi mata laifi zata hadata da proprietor tunda shine maganinta…ita kuwa sai hakilo take bestynta na tayata…yana ajiyesu a hostel suka shiga ciki shima ya wuce.

Around 5 pm suna zaune room 3a gaba daya sai labari suke suke darawa…they are all happy sun gama Clinical Posting dinsu lafia…wayan Aysha data bari cikin dakinsu nata ringing bata ji ba sbd hayaniyan da sukeyi…wata da tazo wucewa taji ringing din shine ta dauka ta kai mata dakin da suke…tana duba screen taga Baby boo jiki sai ta mike da sauri ta fita daga dakin tana fadin”my husband is calling”…Rahma tabita da kallo tana daria tace”Billy wai ina mgnr Sir Abdool ya kwana ne naga Lamido har tayi mishi kishiya sbd wulakanci”…Billy tace”ki bari kawai wlh tunda nake ban ta6a ganin mace kaman Lamido ba…she is indirectly rejecting him for that sugar daddy”…gaba daya daria suka saka kafin wata tace”nima dai ina mamakinta wlh..ta samu mutum kmr sir abdool da yake bala’in sonta wai ta kyaleshi for someone else..she is kind of different”…nan kuma akalar hiran nasu ya koma kan Lamido and her love for sugar daddies kowa yana fadan albarkacin bakinshi…tana fita ta fada room dinsu hadda rufe kofa snn tayi picking…before she says anything yace”My baby am back”…wani ihu data saka saida ya janye wayan daga kunnenshi…lokaci daya kuma ta toshe bakinta tana zaro ido feeling so ashamed of herself for behaving like this…sam batasan sanda ihun yayi escaping bakinta ba wlh..she is just super excited he’s back dama ga farin ciki rabuwa da inyamuri ga kuma another good news…shi kuwa Prof daria ya saki sosai jin tayi diff kaman ruwa ya cinyeta yace”baby girl why are u quite?.”kamae zatasa kuka tace”sorry…ban san yaushe ya fito ba wlh..am just happy u are back”…murmushi ya kara saki yace” don’t worry yanxun dai ki samu ki fito waje in ganki”…idanu ta sake budewa tace”wait..u mean kana hostel dinmu?..”yace”komai bazan iya yi ba har sai na ganki”…ai bata jira ya karasa ba ta kashe wayan da sauri ta rarumi hijab din Billy dake nan kan bed dinta ta dora kan jean da shirt dake jikinta ta zura takalma ta fita…a bakin gate din nasu kuwa ta ga motanshi batasan time data saki murmushi tana karasawa wurin ba…bude mata motan yayi ta shiga snn ta rufe ta juya tana kallonshi…kallon nata shima yakeyi yanajin tamkar bai ta6a missing wata halitta ba kaman yanda yayi missing dinta…ita kuwa banda murmushi ba abunda takeyi…a hankali taji ya kira sunanta”Ayshaa..”ta sake dagowa tana kallonshi don tunda suke bata ta6a jin ya kirata da Aysha ba…before she says anything yayi adding”Baby girl am tired plss…am tired of this hide and seek i really want to meet ur dad..i need to talk to him about us..about our marriage am not a small boy da zanyita wasting time dina ina soyayya a waje”…shiru tayi tana sauraronshi thinking of what to tell him…har ga Allah ba wai batason aurenshi bane no kawai dai tafiso ta fara kammala karatunta then sai ayi mgnr aure amma ta fuskanci he won’t let that happen…his last statement yasa ta dan kwa6e fuskanta kaman zata fashe da kuka tace”wato wasting time dinka kakeyi ma kou?..soyayya dani shine waste of tim…”bata karasa na ya katseta da fadin”No baby that’s not what i mean…ina nufin am tired..i want to marry you plss”…batasan time din da ta saki murmushi sbd yanda yayi da face dinshi ba…tana dubanshi tace”baby saurin me kakeyi ne?..xaka aureni inshaAllah..”zai sake mgn tace”Please mana..k ganinka ban gamayi ba ka fara wani mgn daban..nidai allow me to look at u sosai inyaso daga baya sai muyi mgnr auren”…murmushi ya saki yana girgiza kanshi sarai ya ganeta..wai shi yarinyar nan zatayi ma wayo…bai sake cewa komai din ba kuwa sukaita kallon junansu kaman wanda suke staring competition…har tafiya ta hanashi wai bata gaji da kallonshi ba…haka yayita zaune har sai da aka fara kiran magrib snn ta kyaleshi ya tafi ita kuma ta koma hostel.

Washegari saturday Bobby tunda ya gama gyming dinshi yayi wanka ya fito suke zaune parlor tareda Mummy da aunty sumy sai labari suke…Nur ne ya shigo parlon da sallama Bobby ya wani hade rai yana kallonshi…yasan tunda yazo gidan nan fita yakeso suyi shi kuma baida intention na zuwa ko ina yau…he wanted to stay home yayi enjoying weekend dinshi like any other person amma it’s like Nur yana baqin ciki da haka…har ya iso cikin parlon ya zauna baice mishi qala ba yanaji suna gaisawa da mummy da aunty sumy sai yayi kaman bai jinsu ya shiga danna wayarshi…bayan sun gama gaisawa Nur ya daga kanshi yana kallon Bobby yaga yanda ya hade giran sama dana qasa kawai sai ya dan girgiza kai yana murmushi…yasan duk wnn attitude da ya fara displaying sbd baison fita ne and shi kuma ya ranste yau din nan sai ya fita dashi sai suga yanda za’ayi…hankalinshi ya mayar kan mummy ya wani tattara gaba daya nutsuwa da kamun kanshi yace”mummy alfarma nazo nema a wajenki dama”…mummy tace”to ina sauraronka Nuru”…yace”ai kinsan ana gina new apartments a college hostel koh?..”Mummy ta gyada kai alaman ta sani…yace”to wlh mummy tun last week mukayi mgn da engineer nan yace ya kamata muje da akwai abunda zai nuna mana amma bobby sam yaki zuwa…yanxun ma da kika ganni kirana yayi yace yana can site din yanaso mu hadu sbd gobe zaiyi tafia kuma zai iya daukan lokaci bai dawoba shiyasa na fito..nasan kona fada masa ba yadda zaiyi ba shiyasa nace gara in biyo ta wajenki”…murmushi kawai mummy tayi tana kallonshi kafin ta juya tana kallon Bobby da har yanxun ran nan a hade yana 6a66ata rai…daria ta saki sosai tana kallonsu…wnn draman nasu ba yanxu aka fara ba…shi Bobby nada taurin kai da kafiya shi kuma Nur akwai naci shiyasa duk irin haka ya hadasu kai tsaye yake zuwa wurinta dan yasan itace kadai zata iya sanyashi ya aikata abu ko bayaso…aunty sumy ma dake zaune tana kallonsu daria take…mummy ta sake juyawa tana duban Bobby tace”ai kaji me abokinka ya fada kou?..”da sauri yace”mummy don’t mind him dan Allah makaryaci ne kawai…babban burinshi yaga ya fitar dani daga gida kuma yasan bai isaba shine zai biyo ta hannunki”…juyawa ta sakeyi tana duban Nur shima ya kwaso rantsuwa yana fadin shi wlh da gaske yake…itama kuma taga alama da gasken yake dan haka ta dubi Bobby tace”yi hakuri kuje kaji?..ai nasan ba dadewa zakuyi ba ko Nuru?..”da sauri yace”eh wlh mummy nan da few minutes zamu dawo”…tace”to kaji bazaku jima ba ka daure kuje kaji?..”fuskan nan ba sarari ya mike zuwa Flat dinshi…shidai ko Allah yasan baiyi niyyam fita yau ba wlh amma shi Nur idan yaso abu kaman d’a yaso fitowa daga cikin mahaifiyarshi…kayan jikinshi yayi changing zuwa tracksuit blue ya debi wayoyinshi snn ya fita bayan ya sake feshe jikinshi da perfumes…Nur na ganin ya fito shima ya mike yayi sallama da su Mummy snn yabi bayanshi dan already har ya kusa kaiwa kofa…suna fita compound ya juya yana kallonshi fuska a cunkushe yace”sai kaje dauko motanka muje dan ni yau na sallami driver na”…Nur na sakin smile yace”dama da shiri na nazo ai..motan yana waje”…harara Bobby ya watsa mai kafin ya kama hanyar wajen…Nur yabi bayanshi yana kyalkyala daria…suna fita ya bude motan suka shiga snn ya tayar da ita ya kama hanyan college…karfe 5 saura suka shiga college amma basu karasa cikin hostel din ba sai after five…a gate din female hostel yayi parking tunda engineern yace mishi yana nan ciki…ya bude mota ya fita shima Bobby ya fito har yanxu fuskan nan a hautsine kaman wanda akaima mutuwa…shidai Nur baice dashi komai ba ya shiga ciki…basu damu da sanar da students shigowansu ba sbd ba cikin apartments dinsu zasu shiga ba dan haka kai tsaye suka zagaya ta backyard inda new apartments din suke…tun kafin su karasa suke jiyo sautin kida na tashi daga wurin amma basu kawo komai ba suka cigaba da tafia…daidai bayan apartment C suke jere kusan su goma kowacce sanye da dogon wando da t shirt amma banda Aysha dake sanyeda wata ash color jessy na manchester da wandon jessyn daya dan haura guiwarta da kadan shima ash ne da ratsin red a gefe da gefe sai kuma number 6 dake can kasan wandon…kanta ba dankwali dogon gashinta gaba daya ya sauka zuwa gadon bayanta ta maida hankalinta sosai kan rawar da take koya musu tana miming…wani kullutun abu Bobby yaji yazo ya tokareshi ya hanashi ko hadiyar yawu…duk yawan nan nasu idonshi bai sauka akan kowa ba sai a kanta nan take kuma yaji wani mashahurin kunchi yana mamayeshi…ya lumshe ido ya bude yana son yasan dalilin da yasa idonshi idon yarinyar nan sai ranshi ya 6aci…baisan meyasa kusan komai nata yake kular dashi ba…yanxu dubi yanda ta dage tana koya musu rawa kaman abunda aka turota yi makarantan knn…and the most annoying this is yanda kowa na sanyeda kayan kirki banda ita…kan kowa da akwai hula amma banda nata…gashin kowa a rufe amma banda nata snn wandon kowa har qasa ita nata sbd tsabar tsageranchi a guiwarta ya tsaya…ba kuma wanda ke sanye da kayan yan ball sai ita…shi tunda yake bai ta6ajin ya tsani kayan yan ball ba sai a kanta…sam ya rasa dalilinda yasa ya tsani ya ganta cikinsu…ji yake da yanada hali har supporting man u dinma sai ya hanata wlh sbd ba dabi’a ne mai kyau ba…Nur da tun dazu yake mishi mgn amma yaga hankalinshi bai jikinshi sai ya rungume hannunshi a chest yana kallon inda yake kalla sai yaga Lamido…murmushi ya saki yana sake kallon Bobby still yaga idanunshi kanta ko blinking bayayi kawai sai ya wuce abunshi yana daria…shidai yasan da matsala domin tun ranan da ya kwace zobuna a hannunta jikinshi ke bashi akwai gagarumar matsala amma bai nuna ba…Bobby kuwa a halin yanxu gani yake ko wanda ke prison bai kaishi baqin ciki ba…baisan meyasa ba amma tabbas yasan yana jin wani irin kunchi da 6acin ran da bai ta6a samun kanshi a ciki ba…su kuwa gaba daya ba wanda ya ganshi da haka suketa dirkan rawarsu cikin nishadi sunayi sunabin waqan…baice komai ba ya juya zuwa gidajen matrons yaci karo da wata student din yace taje ta kira mishi one of metrorin dake hostel din babu wasting of time kuwa suka dawo tareda ita…fuskanshi a gimtse muryanshi na nuna tsananin 6acin ran da yake ciki ya nuna mata su Aysha da har yanxun basu bar rawa ba yace”what’s this?..a building dina kuka barsu suke wnn lalatan babu mai tsawatar musu?..”jikin matar har ya dauki rawa tace”yalla6ai ayi hakuri za’ayi musu mgn InshaAllahu..kayi hakuri”…baice mata komai ba ya rungume hannu yana mata nuni da taje ta kirasu aikuwa ta wuce da hanzari zuwa inda suke…tana isa kai tsaye mp da suka kunna kidan dashi ta dauki tayi disconnecting nashi nan take gaba daya suka juya suna kallonta…kafin wani cikinsu yayi mgn ta nuna inda Bobby ke tsaye murya a dan kasa tace”yace a kiraku”…gaba dayansu ba wadda bata tsorata ba ganinshi a tsaye yana binsu da matsiyacin kallo especially Aysha da takejin kaman ta saki fitsari a wando don tsoro…tana daga idanunta suka hada ido dashi aiko ba shiri tayi kasa da nata tana fadin”la’ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minzzalimeen”…cikinta har wani sauti qululu ya bada sbd tsabar figici…batayi aune ba taga gaba dayansu sun nufi inda yake tsaye hankalinta ya sake tashi idonta har kawo kwalla tace”to ko hijab bazamu dauko ba?..”matron tace”wane hijabi kuma bayan ya riga ya gama ganinku a haka”…a haka suka karasa wurinshi saidai ko kallonsu baiyi ba ya juya ga matron yace mata”ki tabbata ko mutum daya bata gudu ba a cikinsu…suzo su sameni ranan monday a office dina by 4″…yana gama fadan haka ya kama hanya sabon apartment din su kuma kowacce ta bishi da kallo baki bude…masu sallallami nayi masu zaginshi ma duk sunayi haka suka mike kowa ta dauki hanyar hostel dinsu…Aysha dai ko kusa bata cikin hayyacinta dan tana ga duk cikinsu ba wadda tasan muguntarshi kaman ita shiyasa tafi kowa tsurewa a cikinsu…yanxu idan yace ya basu suspension me zata cewa Ammi da Daddy ita Aisha?…bama haka ba yanxu idan yace zai basu punishment kaman yanda ya wahalar da ita a Freedom fa?..”yanxu menene abun yi?..”ta tambayi kanta kamar tana jiran wani ya bata amsa…karashen ranar nan dai gaba daya bataji dadinshi ba dan ko baccin kirki batayi ba…Billy tun tana bata baki har ta hakura ta kyaleta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button