Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Haka kwanaki sukayita tafiya kullum Aysha na shan baqar wahala a wajenshi dan ba ranan da zatazo ta wuce bai sata kuka ba…gashi ita kuma ta kasa sabawa da wahalar da yake bata kullum idan ta gani bata ma sanin yaushe kukan ke zuwa…a haka suka kwashe two weeks suna abu daya har suka shiga sati na uku wich is their final week daga shi zakuyi resuming school…if u see how she is happy zakayi zaton graduation ne zatayi gaba daya…nan kuwa murna take sbd Allah ya kawo karshen wahalar da takesha hannunshi dan ko makiyinta bazata yi mishi fatan ya shiga hannun dr bobby ba dan bashda kyau ko kadan…cikakken mara mutunchi ne na gidan gaba shiyasa take addu’a idam sun rabu a nan Allah yasa rabuwarsu knn dan ko a College bata fatan ko hanya su sake hadawa dashi…laf cikinsu ita kadai ce batayi rotating wards ba sbd yanda ya makaleta a office dinshi amma su sauran kusan wards uku kowacce taje…ita Billy daga ANC ta koma Family Planning Unit daga nan kuma taje Ante Natal Ward duk tayi two two weeks a wurin amma ita duk yabi ya takureta a wuri daya ya hanata gaba ya hanata baya sbd baqin hali irin nashi…ita har yanxu tana mamaki idan akace mata musulmi ne dan har ga Allah wnn baqin halin nashi ba idabi’an musulman kwarai bane..ko da yake shima kilan musulmin ne kawai amma bana kwarai ba…shiyasa dole ma tayi murna Allah zai rabata dashi ta huta da ja’iba.

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitar min dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
19
Yau Thursday Aysha na zaune office dinshi ita kadai as shi tunda ya fita sallah bai dawoba dan haka ta bararraje abunta tana ta faman waya da Babynta da har yanxun bai dawo daga tafiyar da yayi ba…bayan sun kammala wayan tayi dialing number Ammi dan da gaske so take taje gida weekend amma Hamma yace wai ta bari ba yanxu ba…ringing biyu Husna ta daga wayan tana cewa”Addah..”tace”na’am ina Ammi?..”Husna ta dan turo baki tace”ke Adda bakida kirki wlh..daga daga wayan zaki wani ce ina Ammi ko gaisawa bazaki bari muyi ba?..”dan murmushi ta saki tana gyara zamanta tace”to sannu Husna ina yini..ya gida ya studies?..”daria Husna tasa jin yanda take gaisheta tace”kai Addah”…itama tana cigaba da smiling tace”to ai naga ba’a iya maki ne shiyasa na gaisheki”…Husna tace”umh to ina nan lafia ya posting?..”da sauri kaman wadda aka tsikara tace”posting dai yazo karshe ki tayani murna wlh..gobe Allah zai rabani da inyamuri in huta da azaba”…daria Husna ta sakeyi tace”nifa Adda har yanxu daria kike bani idan kika kirashi inyamuri..ina laifin ma kice dr bobby”…ta6e baki Aysha tayi tace”ki zauna saina kirashi dr bobby…mutuminda kowa yasan inyamuri ne shi..ranar bakiji wayan da naji yanayi da wani ba kilan dan uwanshi ne sukata inyamurancinsu abunsu”…sauke ajiyar zuciya Husna tayi tace”to congratulations Allah zai rabaki dashi gobe..amma zaku iya haduwa a cikin college fa”…tun kafin ta rufe baki Aysha tace”bakinki ya sari danyen kashi..nidai kiba Ammi waya inyi mgn da ita..where is my habibty?..”tace”yanxun nan suka fita da Hamma…Ammi kuma tana daki tace bacci zatayi kar in tasheta”…Aysha tace”karya kikeyi dan Allah ki kai mata it’s urgent plss pls plss..kinji ‘yar kanwata”…kafin Husna tayi mgn ta jiyo voice din Ammi tana cewa”Husna daukan min waya kikay kou?..”da sauri ta mika mata wayan tace”dama Adda ce ta kira gashi”…batayi mgn ba tasa hannu ta amsa wayan…Aysha ta wani narke kamar tana gaban Ammin tace”my Ammi”..tsaki Ammi taja tace”zakiyi mgn ko bazakiyi ba?..”ta sake narkewa tace”Ammi zanyi…amma fa nayi missing dinki sosai wlh…wai yanxu Ammi ni ko dan pampering dina sbd bana gida bazakiyi ba kuma fa nice fisrt love dinki tunda ni kika fara haif…”bata karasa ba Ammi tace”Aysha zakici ubanki wlh…abokiyar wasanki ne ni da zakina fadamin such maganganu..wato sbd kinga kwana biyu kinata zuba rashin mutuncinka na kyaleki kou?..to zaki dawo gidan nan ki sameni zany maganinki”…da sauri tace”Ammi am sorry dan Allah…kiyi hakuri ban karawa”…wani tsaki Ammi ta kuma ja tace”naji…yanxun zaki fadi ur reason for calling ko kuma iskancin naki zaki cigaba dayi?..”ta wani marairaice kaman abun tausayi tace”zan fada…Ammi dama fa so nake nazo gida weekend shine hamma wai ba yanxu ba…dan Allah Ammi kice yazo ya daukoni kinji..wlh ina missing dinku”…kai tsaye Ammi tace”saidai kuwa kiyi hakuri dan gobe muma zamu wuce Abuja nasan shiyasa yace ki hakura..amma idan muka dawo ai zakizo so stop worrying urself”…da sauri tace”Ammi me zakuyi a Abuja kuma?..”tace”wani taro ne nasu daddynku akayi inviting dinmu and daga ni sai Najeeb zamu tafi banda su Husna dan nasan yanxun xaki ce an tafi dasu baa tafi dake ba…nasan sbd irin wnn halin naki dadyn ma yace a kyalesu a gida”…ba kunya har wani ajiyar zuciya ta sauke dan wlh da zaaje dasu itama daga hankali zatayi sai an biyo an tafi da ita…yanxu kuwa da taji babu su sai taji hankalinta ya kwanta..zuwa weekend dinma ta hakura idan suka dawo din sai taje…a hankali tace”to shikenan Ammi sai kun dawo Allah ya kiyaye hanya”…Ammi ta amsa da”Ameen”snn sukayi sallama…tana ajiye wayan idonta ya sauka kan Bobby dake zaune yayi relaxing kan seat dinshi yana kallonta…ta zare idanu sosai hade da dora hannu a kirji cikin tsananin tsoron ko yaji abubuwanda ta fada a kanshi tace”Na shiga uku”…saura kiris daria ya su6uce mishi amma ya fuske…instead sai ya daure fuskanshi yace”so abunda kikeyi min a office knn idan bana nan kou?..yayi miki kyau”…hadiye wani yawu tayi da kyar cikin karfin hali tace”Sir..dan Allah am sorry…kaji”…ko kallonta baiyi ba ya mika mata hannunshi yace”bani wayan”..a razane tace”wich one?..”yace”ur phone”…nan take ta sake tsurewa duk a tunaninta yaji gulmanshi da sukayi tace”Sir dan darajan su Mummy kayi hakuri”…kallonta kawai yayi hade da girgiza kai yacigaba da aikinshi bai sake cewa komai ba…ita kuwa daukan wayan tayi ta turashi cikin jaka tana addu’an Allah yasa baiji wayan da sukayi da Husna ba…karfe uku ya sallameta as usual tana fitowa suka hadu da Billy da sauran ‘yan hostel suka karasa inda bus dinsu yake duk suka shiga sai Hostel dinsu.

The following day duk da wuri suka shigo sbd friday gajeren rana ce and kowa tanaso a sallameta da wuri sbd su samu su wuce…lokacinda ta isa office dinshi yanata attending patients sai ta nemi wuri ta zauna kamar yanda ta saba tana sauraron discussion dinsu..wasa wasa tayi learning abubuwa da dama zaman da tayi office dinshi don sata gaba yake idan yana interacting da patient yace idan sun gama zaiyi mata tambayoyi dan haka take bude brain dinta da kyau tana kwashe duk abunda yake fadi..haka duk prescription din da yayi saiya nuna mata nan ma idan sun gama ya shiga mata tambayoyi iri iri so he’ve learned alot and ko ba komai ta wnn fannin dai zatace yayi abun kirki…da yake patients din ba masu yawa bane around 12 ya gama dasu snn ya fara shirin tafia sallahn jumu’a…before ya fita ya bata log book dinta da yayi signing already snn ya nuna mata kofa yace”A sauka lafia”…wani kayataccen smile ta saki da har both dimples dinta suka bayyana cikin tsantsan farin cikin zata rabu dashi tace”nagode sir”..daga haka ta fice daga office din bobby ya bita da kallo irin na mamaki…tunda yake da ita bai ta6a ganin such smile kan face dinta ba…yanxun duk wnn excitement daya gani kan face dinta na rabuwa dashi ne ko kuwa there is more to it?..kai ai daga gani ma wnn na rabuwa dashi ne…haka nan kuma sai yaji baiji dadin yanda tayi ba..”am i this bad?..”ya fada a fili kaman he’s asking someone…ganin yana wasting time dinshi a banza kawai ya fita zuwa parking lot driver na ganoshi ya bude mishi mota ya shiga suka fita daga asibitin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button