Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Yana shigowa College zuwa office din Nur da yace mashi yana jiranshi a ciki…da sallama ya shiga yana takawa da kyar sbd matsaloli da suka taru suka cika mashi brain…Nur na ganinshi ya mike ya koma kan sofa shima karasawa yayi ya zauna nan kusa dashi tareda jingina da jikin kujeran yana lumshe ido…Nur yace”kace zamuyi mgn i hope dai lafia?..”girgiza kai Bobby ya shigayi tareda bude idanunshi yace”ba lafia ba Nur..ina cikin damuwa”..gyara zama Nur yayi yace”to inajinka”..ajiyar zuciya Bobby ya sauke yana shakar iska da kyar yace”it’s about Lamido..i think..i think i’ve fallen for her”…dukda Nur ya dade da sanin yana sonta yayi mamaki sosai jin a yanayin daya fada mashi…kamo hannunshi Bobby yayi yana kallonshi da idanunshi da suka sauya kala muryanshi cikin raunin da Nur zai iya rantswa bai ta6ajinshi a ciki ba yace”i am in a serious mess Nur..na rasa nustuwata gaba daya..komai bayamun dadi..komai banajin dadinshi abu daya da yake keeping dina company shine tunaninta..zuciyata ta cuceni duk iya kokarina na ganin na kaucewa abunda nakeji abun yafi karfina Nur..bansan meya kamata inyi ba nasan yarinyar nan bazata ta6a sona ba”..yana rufe baki Nur da yaji asalin tausayinshi na ratsashi ya dafa shoulder dinshi yace”Man take it easy plss..idan kana wnn damuwan kana iya samun problem ka sani..nayi maka alqawarin i’ll help you in anyway possible dan inga ka samu soyayyarta..wnn matsalan nake guje maka shiyasa tun farko naso ayima tufkar hanci baka bani dama ba”..sake damke hannunshi yayi yace”yanxu na baka do your best plss..ka taimakeni before i loose my sanity..inajin zafi sosai duk lokacinda na ganta da wani..yanxu haka da nake mka mgn ko wayana bata dauka kuma bansan laifinda nayi mata..nasan kilan Allah yanaso yayi punishing dina ne kan abubuwanda nayi mata a baya amma wlh bada son raina bane..bansan meyasa ina ganinta raina yake 6aci har yasa nayi mata abubuwanda nayi ba”..rungumeshi Nur yayi cikeda tausayinshi sosai yace”it was all the love Bobby ganewa ne bakayi ba..tun daga ranan da tacemin kace baza tayi presentation ba nasan da akwai wani abu a ranka gameda ita..Lamido is a good girl..tanada hankali sosai and am sure ko bata soka yanxu ba watarana zata soka”…dagowa yayi daga jikinshi yana kallonshi with a wide smile jin abunda ya fada yace”nagode sosai Nur..thank u..kasan a da nayi tunanin sonta kake sai kuma daga baya naga ba haka bane”…Nur yace”well a gaskia bazan boye maka ba i once had a crush on her amma tunda ja fahimci kana sonta saina hakura sbd nasan sonda kake mata yafi wanda zan mata..kuma dakai tafi dacewa bada ni ba and inshaAllah i will do my possible best inga na hada wnn soyayyan..ba karamin matching couple zaayi ba kai da Lamido”…murmushi sosai Bobby yake wanda ya manta when last yajishi so lively haka…maganganun da Nur ya fada sai yajisu tamkar diamond da gold sbd tsananin dadinsu da yaji…cikin murmushin da yaki bajewa fuskanshi yace”thank u so much friend..u are really a friend indeed”…shafa kai Nur ya fara yana wani murmushin shakiyanci yace”gaskia ya kamata ayi saluting Lamido data canxaka haka?..yau Dr Bobby ne da godia haka ba kakkautawa?..”murmushin shima ya kara saki shi kanshi ya dade yana mamakin kanshi..ya dade yana mamakin yanda ya canxa ta 6angarori da dama duk kuma a dalilin Lamido…Nur dake kallon yanda yake blushing yace”amma wait..laifin me kayi ta dena daukan wayanka?..”da sauri Bobby yace”nima i dont know..haka nan ta daukemin wuta rabon dana samu peaceful sleep tun ranar dana ganta last..ina cikin damuwa sosai Nur ka taimakamin dan Allah..I really want to see her..na dade ban ganta ba”…wani murmushin Nur ya saki kafin yace”karka damu yanxun kuwa zaka ganta..let me call her”..yana fadan haka ya dauki wayanshi dake kan table ajiye snn ya nemo numberta yayi dialing..da sauri Bobby ya matso kusa dashi yana kallon wayan kamar zai ganta ne a ciki..Nur yasa a speaker nan kuma sukaji kiran ya shiga..tana dauka tace”Sir ina yini”..Bobby ya wani lumshe ido yanajin yanda muryan nata ke zagayawa cikin dukkanin systems dinshi..he missed her like crazy..jin muryanta kuma sai ya sake kwadaita mishi son ganinta..yasan yau idan bai ganta ba matsala zai samu gaba daya..he don’t think zai iya daukan rashin ganin nata anymore..he just can’t..he need to see her…idon Nur na kallonshi yana kallon yanda ya fada duniar shauki sbd jin muryanta yace”hajia Lamido manyan mata..ya studies?..”tace”Alhamdulillah sir dama inaso inzo wurinka akan mgnr malam Mukhtar”..yace”then kizo office yanxu dama nima nemanki nake”..tace”ohk gani nan”..daga haka Nur ya kashe wayar yana duban Bobby yace”she’s coming”..kai kawai Bobby ya iya daga mashi yana tunanin yanda zasu kwashe da ita…mikewa Nur yayi ya koma seat dinshi yana zama sai gata ta shigo office din sanyeda uniform dinta as usual da glasses dinta a ido…tana gama kulle kofa ta juyo zata nufi inda yake zaune kawai idanunta duka hango mata shi a zaune ya waniyi crossing hands dinshi yana kallonta kaman wani soko…dan daure fuskanta tayi ta dauke kai snn ta karasa gaban table din Nur tace”Sir i think zanje sai in dawo some other time”..da sauri Nur yace”amma why?..”bata amsa mashi ba ta juya da sauri zata fita Bobby ya mike da saurin shima yasha gabanta…ta dago tana kallonshi fuskan nan a kwabe tace”nifa wucewa zanyi”..mai mata bazan sai aikin kallonta da yake kaman ba gobe…matsawa tayi zatabi gefenshi ta wuce nan ma ya sake tare mata hanya kawai saita dago tana kallonshi kaman zatasa kuka…Nur da yaga wasan nasu ya fara daukan zafi sai ya mike daga inda yake ya ra6a ta gefen Bobby zai fita daga office din ya dan rankwafa saitin kunnenshi yace”Man karka raga mata wlh..make her fall for u”..yana gama fadan haka ya fice daga office din Lamido tabishi da kallo kamar zatasa kuka…sake matsawa tayi zata wuce shima ya sake tare mata hanyar…tayi kasa da kanta kawai tana turo baki kawai sai jin mutum tayi dab da ita dan har numfashinshi a jikinta ke sauka..ta matsa baya tana sake turo baki shima ya sake matsawa inda ta matsa din..ta sake taking two step backward shima yayi haka kawai saita shiga yarfa hannunta tace”sir ni me nayi?..”baice mata komai ba sai binta da yacigaba dayi har ta fada kan sofa..maimakon ya zauna kan sofa sai ya janyo table dake wurin ya zauna a kai yanda zaina kallonta da kyau..muryanshi kasa kasa yace”why are u ignoring my calls?..no why are u ignoring me?..”sake turo baki tayi tace”sir ni banyi ignoring dinka ba”..yace”shi kuma kin daukan wayana na meye?..”tace”ba komai”..kallonta ya tsayayi for like five minutes kafin ya sauie ajiyar zuciya ya sake yin kasa da muryanshi yace”nayi maki wani abun ne?..”ta girgiza kai…yace”then why all these?..why are u doing these?..if saboda na kwace maki rings dinki ne zan maido maki kayanki amma ki dena wahalar dani haka plss”…kallonshi tayi jin abunda ya fada kafin tace”nifa bakayi min komai ba..kawai naga mutane sun fara tunanin soyayya mukeyi shiyasa na dena kulaka”..diff yayi yana kallonta jin kalamanta…yace”yanxu sbd ana tunanin muna soyayya shine zaki dena daukan wayana?..”tace”to sir muda ba soyayya muke ba meyasa zamu ba mutane kofar da zasuyi tunanin soyayya muke?..”tana rufe baki yace”nina fada maki haka?..ko kinsan mind dina ne?..”dagowa tayi ta kalleshi da mamaki sai kuma ta kawar da kanta tana wani daure fuska tace”wlh ba soyayya muke ba”..cikin 6acin ran da yaji ya fara diran mishi yace”wai yaushe kika rainani ne haka?..kinsan zuciyata ne?..well idan baki saniba to let me tell you now..i love you..i love you with my whole heart kuma i want to marry u”..a rikice ta sake dagowa tana kallonshi taga yanda ya tsareta da ido kawai saita rufe fuska da hannayenta ta rushe da matsnancin kuka…hankalinshi yaji ya tashi sosai ga wani irin rauni da yakeji kawai saiya dafe goshi yana sauke numfashi..wai dama haka soyayyan yake ko kuwa nashi ne yake zuwa mishi da wann problems haka?..yana kokarin solving matsala sai kuma ga wani ya kawo kai sun taru suna neman fasa mashi zucia..ganin da gaske kuka takeyi yayi kasa da murya yace”yi hakuri i was kidding..bana sonki..amma seriously idan baki dena ignoring dinaba zaki sani cikin matsala wlh..koma meye ya faru I apologize and idan laifi nayi maki you are free to punish me amma ki dena bani wnn attitude din i beg of u plss”..dakatar da kukan tayi tana kallonshi hawaye sha6e sha6e a fuskanta tace”kace da wasa kake?..”da sauri yace”yea wasa nake..i never loved u”..ajiyar zucia ta sauke tana goge hawayen idonta tace”thank you”…kallonta kawai Bobby keyi yanajin wani irin daci a bakinshi sbd 6acin rai..yanxu tsanar da tayi mishi har yakai tasa mishi kuka sbd yace yana sonta?..anya kuwa zai samu soyayyar yarinyar nan?..anya kuwa zai iya jure wnn matsalolin?..ganin ya tafi wani dunian daban ta mike tsaye tana dubanshi tace”sir ni zan tafi”..dagowa yayi ya kalleta from head to toe before saying”ina hijab dinki?..”kallonshi tayi tace”wane hijab?..”rai a dan 6ace yace”ba nace ki dinga sa hijab idan zakizo makaranta ba?..wato mantawa kikayi koh..?”da sauri tace”nazo dashi fa yana class”..nuna mata inda ta tashi yayi yace”to zauna bamu gama mgn ba”..ba musu ta koma ta zauna tana wani ta6e baki tace”amma dan Allah kayi sauri ana jirana ne”…kallonta kawai yake dan baisan amsan da zai bata ba..wai shi yarinyar nana take gayawa mgn haka…idan ba ruwa daya daki babban zakara ba ita ta isa ta zauna gabanshi tana fada mashi mgn haka bai gaura mata mari ba..amma yanxun wai shine nan zaune tana zuba mishi iskanci iri iri kuma bai iya ta6uka komai ba sbd soyayya..amma soyayya baima Dr Bobby adalci ba wlh…saida ya bari ta gama ta6e ta6en bakinta snn yace”kinaji?..”tace”ehh..”yace”dan Allah inaso daga yanxu duk nayi maki laifi ki fadamin ba kije kiyita fushi kinakin daukan wayana ba..banajin dadi..snn kullum kika shigo school ki dinga zuwa office ina ganinki kinji?..”kallonshi tayi kaman zatasa kuka tace”sir kullum kuma?..ai ba kullum kake shigowa ba..kumani banaso inzo kayita min fada fa”da sauri yace”ina shigowa kullum mana..every morning zan shigo idan muka gama gaisawa sai in wuce hospital…kawai nidai ki dinga picking calls dina and ki dinga zuwa ina ganinki?..fada kuma indai ba ganinki nayi da wani ba ba abunda zaisa na miki..duk abunda kikaga na maki rashin jinki ne ke janyowa”mamaki sosai ya bata jin abunda yake fada…ba tareda ta kawo komai a ranta ba tace”zanzo..kuma ni ai bana kula kowa..besty ma da ya taf…”bata karasa ba yace”enough..zaki fara kou?..”da sauri ta dora hannu kan bakinta tace”yi hakuri toh..na dena”..kofa ya nuna mata yace”jeki”..da sauri ta mike ta fita shi kuma ya lumshe ido tareda jingina da kujera…shidai zaiga ranara da za’ayi mgn na minti goma da ita ba tareda tayi mentioning wnn bestyn ba…duk yanda yakai da son ganinta da kuma son kasancewa da ita gara ta tafi akan dai ta zauna tana mishi hiran wani wai besty..shi tunda yake bai ta6ajin ya tsani wani kaman yanda ya tsaneta da bestyn nan ba…ya samu ganinta kuma yayi mgn da ita maimakon ya samu farin ciki sai yajishi akasin haka..sam abunda yakeji is not close to farin ciki…wai shi soyayya dai haka yake cikeda rudu da matsaloli dama?..meya jefa kanshi a ciki ne?..innalillahi wainna ilaihi rajiun..yaketa maimaitawa a cikin ranshi…Nur na ganin fitarta daga office din ya dawo ciki yana kallon Bobby yace”Man how far?..ka samu ka shawo kanta?..”ba tareda ya bude idanunshi ba yace”for where?..yarinyar nan tanada rigima wlh..maimakon in samu sauki fa karamin tayi akan damuwan da nake ciki”…zaunawa Nur yayi kusa dashi yana murmushi yace”ai dama da ganin Lamido nasan mijinta sai yaci ubanshi wlh..at times sai inyita tunanin da wnn shagwa6an nata ya takeyi da boyfriend dinta ne kam?..i never tought it’ll turn out to be you sai yanxun”…kallonshi kawai Bobby daya bude idanunshi yakeyi..yasan abunda yake fada gaskia ne..shi kanshi ko a da din ya kanyi tunanin ya mijinda ya aure ta zaiyi coping da wnn halayyan nata sai gashi ya tsinci kanshi cikin tafkin sonta tsundum kuma baya fatan fitowa har abada…fatanshi ya samu ya shawo kanta idan tayi accepting love dinshi to duk abunda zai biyo baya mai sauki ne.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button