Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Washegari ta tashi da dan dama dama don batayi kuka ba kwata kwata saidai yawan tunani…tun jiya taje tunanin yanyar da zatabi wajen sanar da Prof halinda ake ciki amma ta kasa…hakan yasan ta sanar da Ammi ita kuma tace idan daddy ya dawo fada mashi sai ya kirashi da kanshi yayi mashi bayani sbd kada ma yayi zaton ko yaudaranshi zatayi…da wnn shawara na Ammi ta dan samu nustuwa amma dukda haka tana tunanin halinda bawan Allahn nan zai shiga duk ya samu labari…daddy na dawowa Ammi ta fada mishi yanda sukayi yace ta kawo numbershi ya kira da kanshi suyi mgn..ba musu ta bashi number nashi snn ta zauna nan parlon daddy ya kira number…yana dagawa daddy yace shine mahaifin Aysha sai kuma ya dora da fadin yanda sukayi da Lamido kan batun zuwa neman aurenta da yace zaiyi…hankalinshi ya rashi sosai wanda hatta daddy saida yaji tausayinshi…ya kwantar mashi da hankali tareda cewa sucigaba da addu’a idan Allah yayi akwai rabo a tsakaninsu zasu auri juna idan kuma babu rabo sai kowa ya rungumi kaddara…Aysha dai na zaune tana sauraronsu tanajin tausayinshi na kamata sosai..bawan Allah dama tasan zai shiga mawuyacin hali…nasiha daddy ya sake mata snn yace ta tashi ta tafi Allah ya mata albarka.

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
44
A hankali Bobby ya bude ido daga nannauyan baccinda ya daukeshi as a result of alluran bacci da aka bashi…a take maganganun Lamido suka shiga dawowa kwanyarshi…”shine wanda na za6a mata a matsayin miji..ko bayan raina ban yadda a fasa wnn auren ba”…wnn words zai iya cewa tunda yake bai ta6ajin words da suka tayar mishi da hankali kamarsu ba..kalmomi ne marasu yawa a baki amma tabbas yasan sunada nauyin da zasu iya tarwatsa duk wani farin ciki da yayi saura cikin rayuwarshi…kalmomi ne dake kokarin nesantashi da macen da yafi so duk dunia idan aka dauke Mummy…hakan kuma yana nufin rabuwa da ita na har abada..runtse idonshi da yaji har wani yaji yake mishi sbd tsabar tashin hankali..har yanxun heart beat dinshi bai dawo daidai ba..yanxu shknn Lamido aure zatayi ta barshi?..sake runtse ido yayi zafin da idonshi keyi na karuwa kuma ko alamar hawaye babu a cikin idon..wato shi kanshi kuka ma rahama ne..kawai the taught of her getting married to someone yasa yaji another zazza6i yana son rufeshi…dama tun farkon ganinshi da Najeeb din nan yaji bai kwanta masa ba ashe shine wanda zai zama silar rabashi da ita..dukda ba sonshi take ba yana fatan watarana zata soshi and now Lamido yayi ruining komai…Mummy ce ta shigo dakin tareda Aunty Munubiya da basket din abinci a hannunta..Waziri kuma tin daxun doctor yace a maidashi gida because yana bukatan hutu shima if not yana iya faduwa sbd damuwan daya daurama kanshi..dole haka ya hakura ya koma gidan don shi kanshi yasan idan bai samu hutun ba kaman yanda likita yace yana iya komawa gidan jiya..gaba daya yaron ya tsaya mashi a rai matukar tausayinshi yakeji..ashe dama har yanxun ana samun irin wnn soyayyar?..shikam wane taimako ya kamata yayima yaron nan matsayinshi na kaka kuma waliyyinshi?..wane kokari ya kamata yayi don ganin ya samu wnn jika ta Lamido daya kwallafa rai a kanta?…Mummy na isa ta zauna nan kusada shi tareda kamo hannunshi ta rike cikin nata kawai ta shiga binshi da ido…a hankali yasake bude idonshi a kanta kafin ya kuma maidasu ya lumshe muryanshi na fita da kyar yace”mu..koma gida..Mummy pls..i don’t want to stay here anylonger”..damke hannunshi Mummy tayi hawaye na ciko idanuwanta tace”zamu tafi..amma first ka fara kwantar da hankalinka ka samu sauki tukunna”..tun kafin ta rufe baki ya shiga girgiza kai still idonshi a kulle yace”bazaki ganeba Mummy..aure za’a mata..aure zatayi ta barni..kakanta yace ya za6ar mata miji Mummy bazan iya cigaba da zama garin nan ba mu koma kano please!.”kuka ne sosai yaci karfin Mumny dake rikeda hannunshi ta kasa cewa uffan…Aunty Munubiya kanta saida kwalla ya cika mata ido..karasawa tayi kusa dashi bayan tayi dropping basket dake hannunta tace”dama sbd ita kazo Gombe ba sbd grnadfather dinka ba?..kana tunanin idan kuka tafi yanxu waziri zaiji dadi ne?..”mikewa ya shiga kokarin yi zaune da sauri Mummy ta taimaka mashi ya jingina da pillow..har yanxun ya kasa bude idanunshi don yana budewa zafin da yakeji cikinsu ke sake karuwa..yakai duk hands dinshi ya dafe forehead dinshi dasu cikin muryanda ke nuni da tsagwaron damuwar da yake ciki yace”Aunty bazan iya zama ba..bazan iya zama bayan nasan zata auri wani ba”..yana rufe baki Aunty Munubiya tace”to idan ka koma kanon kana tunanin ka dena ganinta ne?..karewa ma naga a college dinka take karatu kuma hutu na karewa zata koma tunda ba gamawa tayi ba shima sai kace zaka bar college din sbd ita?..get a grip of yourself mana Bobby..be a man inshaAllah Allah bazai barka haka ba”…sauraronta kawai Bobby keyi without saying anything..bazasu gane bane..bazasu ta6a gane halinda yake ciki ba shiyasa duk zasuyi wnn maganganun…a yanda yakejin zuciyarshi yasan dab take da samun matsala shi kuma baison yacigaba da zama yana dorawa Waziri damuwa kada hakan yayi sanadin da hawan jininshi zai sake tashi…gaba daya Gomben ta fita a ranshi and matukar ba komawa Kano yayi ba yana iya samun matsala…da za’a taimakeshi a cireta daga college din ma shi da yafi mashi yanda idan ya tafi ya dena ganinta kenan for good…sake komawa yayi ya kwanta zuciyarshi na cigaba da bugawa da gudu…Mummy takai hannu tana shafa uban gashin kanshi da bai cika askewa ba tace”ko tea bazaka sha ba Bobby?..”gyada mata kanshi yayi alamar bazai sha ba..da sauri Aunty Munubiya tace”aa ya kamata kaci wani abun gaskia..doctor yace kafin medication ya zama lallai kaci abinci”..banza kawai yayi da ita idonshi rufe don gani yake bazata gane halinda yake ciki ba…da kyar da sidin goshi suka samu yasha tea din snn ya sake komawa ya kwanta before time din medication.
Washegari ma haka ya tashi ba walwala dukda cewa fevern da yakeji ya sauka amma har yanxun bai dena ciwon kai da jiri ba…tunda ya tashi baiyi mgn ba duk yanda aunty sumy taso yace wani abu kin kulasu yayi sai binsu da yake faman yi da ido kmr bai sansu ba..fuskan nan nashi kuwa a tamke kamar na shanu shi kadai yasan abubuwan da yakeji a cikin ranshi…da yamma sai ga Lamido yazo dubash tareda daddy da baima san yana garin ba saida Lamido yace yazo ya rakashi duboshi…mamaki sosai ya kama daddy ganin yanda ya koma cikin lokaci kankani dukda cewa a haka kokari yake yaga bai nuna musu asalin damuwar da yake ciki ba..da yake sun samu waziri a asibtin basu suka tafi ba sai dab da magrib…daddy na zuwa gida yace Ammi ta shirya ita dasu Aysha yanaso Najeeb ya kaisu asibiti su dubo jikinshi a daren…haka kuwa duk suka shirya suka fita inda Hamma ke jiransu…tana ganin shine a motar ta wani hade rai tana muzurai..baice mata uffan ba ya bude motar Ammi da su Husna suka shiga baya aka barta a tsaye alamun ita suke nufi ta dhiga front seat knn…budewa tayi ta shiga tana wani kumbura kamar kububuwa..shikam Najeeb daria ma abubuwan nan nata suke bashi wlh…wai shi Maama takema wnn iskancin kawai sbd ance za’a hadashi aure da ita…ya tada motar suka tafi kuma har sukaje asibiti ba wanda yayi mgn cikinsu sai Yusra daketa damun Ammi da tambaya kaman ‘yar jarida…bayan ya gama parking Ammi ta bude mota ta fita yaranta sukabi bayanta…itama hannu takai zata bude yayi saurin danna lock yana kallonta…juyawa tayi tana dubanshi fuskan nan a kwa6e tace”Hamma meye haka?..ni ka budemun mota in fita”..tana gama fadin haka sai kuma ga hawaye ya shiga silalowa kan fuskanta shidai yayi shiru yana kallonta baice komai ba…kamar wanda aka tsikara ta dago tana kallonshi tace”Hamma wai dama kana sona ne?..meyasa Lamido ke cewa zai hadani aure dakai?..dan Allah Hamma kayi wani abu bazan iya auranka ba wlh”..matsawa kusada ita ya kamo hannunta yana cewa”ki nustu mgnr da zamuyi knn amma ki tsaida kukan nan first”..ba musu ta hadiye ragowar kukan tareda kai hannu tana goge hawayenta…saida ya tabbata ta dena kukan snn yace mata”haka kika tsaneni dama ban sani ba?..”da sauri ta hau girgiza tace”ni ban tsaneka bafa”..yace”idan ba tsanana kikayi ba meye wnn?.why kike bani attitude sbd ance zan aureki?..”langabar da kai tayi tana dubanshi a hankali tace”Allah ban tsaneka ba Hamma..kawai ban ta6a picturing kaina matsayin matarka ba..kallon dan uwa na jini nake maka Hamma ba kallon mijina ba”..sake kama hannayenta yayi ya rike shima yana dubanta da kyau yace”na sani Maama..hasali nima kallon qanwata nake maki ba kallon matar da zan iya aure ba amma ya zamuyi?..idan kaddaranmu yazo a haka dole haka zamuyi hakuri mu kar6eshi tunda bamuda yanda zamuyi”..hawaye na sake taruwa idanunta tace”kai bakada wadda kakeso ne?..”shiru yayi yana kallonta kmr bazaice komai ba sai can kuma yace”inada..akwai wadda nakeso Maama amma bankai ga sanar da ita ba wnn mgnr na Lamido ya 6ullo”..da sauri ta sake rike hannunshi tace”then muyi mgn da daddy plss..ka fada mashi kaima kanada wadda kakeso nasan inshaAlla bazai rasa yanda zaiyi ba”..hannu yakai yana goge mata hawaye yace”naji i will think about it amma yanxu ki bari mu shiga muyi dubiyan nan tukun..kada su Ammi su gama bamu je ba”..da sauri ta shiga gyada kai tana karasa hawayenta tace”toh na dena”..murmushi ya sakin mata tareda bude motar ya fita itama ta fita suka nufi cikin asibitin…saida ta kira Ammi ta fada mata room number snn suka isa zuwa dakin…Najeeb ne ya fara shiga snn itama ta shiga kai a kasa…Bobby idonshi ke kallon kofa tun daxu yana jiran shigowanta kasa dauke idanunshi yayi a kanta..yanajin zuciyarshi tayi wani tsalle ta dire sbd ganinta da yayi tareda wanda yasan shi zai aureta baisan lokacinda ya runtse ido yana salati sbd zafin da yaji ba..ba kowa dakin sai shi kadai don haka Hamma ya kara karasawa kusa dashi yana dubanshi da murmushi yace”sannu ya jikin”..kai kawai Bobby ya iya daga mash ba tareda ko bude idonshi yayi ba..a yanda yakeji yasan tsaf zai iya kasa controlling anger dinshi na ganinsh da yayi tareda ita shiyasa ko idan yaji budewa balle yayi mashi kallonda zai jefashi tunani…Najeeb bai kawo komai ba a tunaninshi ko jikin nashi ne shiyasa daya gama dubashi ya juya ya fita daga dakin…wani irin shiru dakin ya dauka har suna iyajin numfashin junansu…kallonshi kawai take ganin yanda ya kara haske ga dan rama da yayi sai taga kaman karo mishi kyau akai don sosai taga yau dai yayi mata kyau…shiko bude idanunshi yayi jin har yanxu batace komai ba sai gashi karaf idanunsu sun sarke cikin na juna..da sauri ta dauke nata tana zare ido sbd wani irin abu da taji ya shiga cikin idanun nata har zuwa zuciyarta..bata taba jin irin wnn game dashi ba tadai san for sure idonshi na sata jin wani iri amma ba irin wnn feeling din bane kwata kwata…lumshe idon ya sakeyi kafin ya budesu fes a kanta yanajin kmr ya mike ya sanyata a jikinshi ko zai samu saukin wnn ja’iban da yake ciki…idanunshi sun kada sunyi jajir ga zuciyarshi daketa faman bugawa da mugun sauri…ido ya sake lumshewa yanajin yanda gaba daya ganin nata ya dirar mishi da wani kasala na musamman…wani irin weird feeling yakeji irin wanda bai ta6a ji a kanta ba…addu’a ya shiga karantowa a ranshi wai ko feelings din zasu ragu amma kmr sake hankado mishi su akeyi…sun dauki kusan mintina biyar a haka kafin ta karasa kusa dashi a hankali har yanxu bata bar kallon face dinshi ba tace”ina yini”..bai bude idonsh ba kuma bai amsa ta ba..ta sake cewa”Sir ina yini”..still bai amsa ba sai takai hannu ta dora kan nashi da nufi ta jijjagashi wai ko bai jita bane aikuwa ya kama hannun nata da sauri kmr magnet ya damke cikin nashi…wara ido tayi tana kallonshi da mamaki ashe idonsa biyu dan rainin hankain…kokarin kwace hannunta ta shiga yi nan take yaji wani karfi yazo mishi kawai sai ya mike zaune yana dubanta da idonshi da ya bata tsoro sbd jajir din da yayi…kallonta yakeyi cikin ido eyes dinshi na shinning as a result of hawaye da cikoshi..tunda abun nan ya faru sai yanxun tears suka samu damar zuwa idanunshi amma jiya sai zafi da idon suke ba hawaye ko kadan…kallonshi itama take tana karantar abubuwa da dama cikin idanun nashi wanda bata ta6a tsaiwa ta karance su ba ada..abubuwa ne masu wuyar karantuwa snn kuma masu wuyar fassaruwa amma dukda haka taji ta kasa dauke idanunta a kanshi…hawayen dake idanuwanshi yayi kokarin maidawa kafin yace”can..i hug..u plss?..”wara ido tayi tana kallonshi without saying anything..voice dinshi na rawa ya sake cewa”for this once Aysher plss..mutuwa zanyi”…lokaci guda itama hawaye suka ciko idanunta ba tareda tasan dalilin su ba…ganin kallon da take mishi ya janyota jikinshi tareda wrapping dinta da hannayenshi ya saki ajiyar zucia mai karfin gaske…tana iya jiyo yanda heart dinshi yake bugawa da mugun sauri nan take hawayen dake idonta suka gangaro fuskanta…Bobby ko wani irin sanyi yaji yana ratsa tun daga kwakwalwarshi har zuwa tafin kafafunshi..idanuwasnhi rufe yayinda hawayen dake ciki suka wanke mishi fuska..ji yake inama zasu dawwama a haka shikam daya gama samun komai na dunia…a hankali yayi breaking hug din tareda kamo fuskanta da hannayenshi ya hada da nashi fuskan still idanunshi rufe saidai ba hawaye yakeyi ba yace mata”ina sonki sosai Aysher..morethan any other thing..you are my whole world..my whole heart..you are my..”kasa karasawa yayi ya sake runtse ido sbd wani abu da yaji ya tokare mishi wuya..sake manne face dinshi yayi da nata yana kallon cikin idonta yace”i will die without you.. i will die for sure”..ya karasa yana sake lumshe ido at the same time yana sauke numfashi…Lamido kuwa kuka ta fara wiwi kai kace uwa da ubanta ne suka rasu suka barta a doron kasa…ita kanta kuma bazata ce ga dalilin kukan ba amma for sure tasan akwai tausayinshi sosai a cikin ranta…ta kuma san da gaske yana sonta fiyeda komai kmr yanda yace…sake rungumeta yayi yana shafa bayanta yace”sorry i made u cry…i just feel like saying what i have in mind but am sorry”..girgiza kai ta shigayi alaman ba reason din kukanta knn ba tace”aure za’ai min”..yace”i know”..tace”Hammana zan aura”..nan ma kai ya sake gyadawa yace”i..know”..a hankali ta bude ido tana kallonshi cikin sigar lallashi tace”am sorry”..yace”u don’t have to..i forgave u already”..kai ta shiga gyadawa tana sakin smile da wet face dinta tace”thank u..thanks for loving me”..kallonta kawai Bobby keyi yanajn wani abu na zagayawa cikin jininshi and he couldn’t help it saida ya kai lips dinshi goshinta ya manna mata peck a wurin snn ya saketa tareda komawa kan gadon ya kwanta yana fadin”thank you”…kallonshi ta tsaya yi tanajin wani bakon abu na zagayawa cikin jikinta…karasawa tayi kusa dashi idonta akan fuskanshi tace”Allah ya baka lafia..zan tafi”..kai kawai ya iya daga mata tareda dan sakin murmushi wanda baikai zuci ba…saida ta juya zata tafi ya bude ido yana kallonta har ta fita daga dakin snn ya sake lumshe idon tareda kai hannu yana dafe saitin heart dinshi dashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button