Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
33
Tana fita taga ba motan Nur a parking space dan haka ta kirashi a waya..yana dauka yace mata”Lamido kiyi hakuri wani abu ne ya tosomin yanxu nan aka kirani shiyasa na tafi..kiyi mgn da Dr Bobby nasan zai maidaki”..bata iya cewa komai ba har ya gama bayaninshi ya kashe wayar…kuyawa tayi a hankali ta koma office din nashi…ta tura kofar ta shiga kai a kasa..yana zaune yanda ta barshi ya dago idonshi da kyar yana dubanta yace”what?..”tace”provost ne yace mu tafi tare waishi ya tafi wani wuri”..bai iya cewa komai ba ya mike zuwa wani drawer ya dauki drugs dinshi ya 6alla snn yayi dispensing ruwa yasha maganin dashi…duk wnn abun da yake bai sake kallon inda take ba sbd baison ya sake aikata wani abun..yana gama sha ya dauki waya da keys dinshi yace mata”muje..”ba musu ta juya suka fita daga office din…yasa key ya rufe snn suka wuce parking lot…dirver na hangoshi yazo ya bude mishi kofa as usual yana karasowa ya shiga ita kuma Aysha ta bude front seat zata shiga da sauri yace mata”are u mad?..C’mon come back here”..batace kala ba ta maida kofan ta rufe snn ta bude nan kusa dashi ta shiga..shima driver ya shiga tareda tayar da motar suka fita asibitin…ko a hanya Bobby bai kallon inda take..haka nan yajishi duk a takure sbd kusancinda sukayi da juna..gaba daya bai yadda da kanshi bane a yanda yakeji din nan yasan tsaf zai iya sake aikata wani abun kwatankwacin na dazu shiyasa duk yaki ya saki jikinshi ya wani takure can karshe kaman ba motarshi ba…Aysha kuwa bata ma lura da abunda yakeba don duk a zatonta bashida lafia…shiru motar babu mai cewa komai banda sanyin ac ba abunda ke tashi sai Lamido dake dan motsawa time to time…har suka isa FCNM Hostel ba wanda yace qala..driver na gama parking ya bude motar ya fita ya rage su biyu kadai a ciki…a hankali ta kama handle zata bude kofar sai kuma ta juya tana kallonshi nan kuma taci karo da idonshi a kanta kusan a tare kowa ya janye nashi idon…dan murmushi ta saki tana dubanshi tace”sir nagode..sai anjima”..kafin ta bude motar taji shima a hankali yace”am sorry”..sake juyowa tayi tana kallonshi still da murmushi sai kuma ta girgiza kai tana cewa”bakayi laifin komai ba sir..nasan u are a good person and bakayi kama da irin wnn mutanen ba..so u don’t have to apologize”..wani ajiyar zuciya da bai shirya ba ya sauke har dan wani smile yayi sbd samun relieve najin abunda tace…at least dai yasan batayi mashi kallon mutumin banza ba..shi sai yaga yau tayi wani irin nustuwa na musamman kaman dai ba Lamido da kullum suke rigima da ita kan rashinji ba…baisan ko sbd ya fara sonta ne kuma ya fara ganin nutsuwarta ba amma dai yau ta burgeshi fiyeda tunaninshi…bude motar tayi ta fita kafin ta rufe ta sake sunkuyowa tana dubanshi har yanxu da wnn murmushin kan fuskanta tace”thank u so much sir..sai anjima”..kai kawai ya iya dagawa yana kallon yanda murmushin keyi mata kyau kaman wani soko..rufe mishi kofar tayi snn ta juya ta tafi shi kuma hadda su sauke glass yana sake binta a kallo yanajin wani abu kaman maganadisu nason janshi gareta dan haka ya sauke glass din tareda maida kanshi yayi relaxing akan kujera yana cigaba da tunaninta…gaba daya ta mamaye jini da tsokarshi ta yanda bai iya cikakken mintuna 10 ba tareda yayi tunaninta ba…ta 6ata mishi rai jiya amma yau ta faranta mishi matuka..kawai sai yaji dadin yanda yaga ta nutsu da kuka yanda batayi misunderstanding dinshi ba..sai kuma yanda ta damu har saida ta nemo inda yake ta bashi hakuri..she really is amazing and ya tabbata if abubuwa zasu cigaba da kasamcewa haka watarana yana iya samun soyayyarta..tunanin hakan kadai ya sake saukar mashi da wani farin ciki…duk wnn kunci da 6acin ran da yake ciki sai yaji sunyi disappearing..a haka driver ya shigo ya sake tayar da motar suka dauki hanyan gida.

Da fara’a ya shigo cikin gidan saidai mutanen daya gani parlon zaune tareda su Mummy yasa yaji new 6acin rai na neman taso mishi…suna jin shigowarshi suma gaba daya suka maida hankali kanshi kaman dai jiran zuwanshi suke…dauke kanshi yayi ba tareda yace qala ba ya kama hanyan flat dinshi Mummy da aunty sumy suka hada ido kafin Mummy ta mike ta dubi mahaifiyar Isma’il grandma din su Miemie knn tace mata”ina zuwa bari inyi mgn dashi yanxun nan”..daga mata kai matar tayi duk jikinta yayi sanyi..ita gani take kaman shi zai hana su samu yafiyar da sukazo nema wurinsu..dukda already sun riga sun gama mgn har Mummy tace itakam bata rikesu ba dama ta yafe musu itama aunty sumy jin Mummy tace haka itama sai bataja zancen da nisa ba tace ta yafe..su Miemie kuwa ya rage nasu su yafe ko karsu yafe amma sunsan komai dadewa watarana zasu yafe musu tunda duk tsiya dai ahalinsu ne…Mummy na shiga dakin ta sameshi zaune gefen gado ya hada uban tagumi kai kace uwa da ubanshi ne suka mutu..yana ganinta kaman jiran shigowan nata yake yace”Mummy why dan Allah?..why?..”kallonshi kawai Mummy keyi dama tasan za’ayi haka..tun kafin suzo dama tasan rana irin wnn zaizo and gashi yayi reacting exactly yanda take tunanin zaiyi…tasan yanxu ko auren sumayya za’a maida daga wurinshi za’a fara samun matsala sbd wnn dan banzan rikon nashi da bai iya mance abu komai tsahon lokacin daya dauka…karasawa tayi kusa dashi ta zauna tana dan murmushi tace”yau an hadu da Lamido knn?..”tana rufe baki yace”Mummy ba mgnr Lamido ake ba meya kawo mutanen can cikin gidan nan dan Allah?..me sukazoyi mana?..”ajiyar zuciya Mummy ta sauke tareda kamo hannunshi still murya kasa kasa tace”yafiya sukazo nema Bobby..sunaso mu yafe musu dukkan laifukansu na baya kuma nidai na yafe musu..itama Sumayyan ta yafe sbd haka dan Allah kar kace zakayi kokarin causing scene a wurin nan dan Allah”..kallonta kawai yake yanaji yanda 6acin ranshi ke ninkuwa ninkin ba ninkin…kamar zaisa kuka yace”yanxu sbd Allah Mummy duk abubuwanda suka aikata har kun manta knn?..kin manta wulakancin da sukayi mata kawai sbd ba ita sukaso ya aura ba shine yanxu sbd sunaso ya maida ita zasu wani kwaso legs dinsu suzo mana gida..Mummy yanxu ko don sbd su Miemie bazaku duba wnn al’amarin ba..sukayi abandoning dinsu for almost seven years shine yanxu zasu wanizi suce ku yafe musu ku kuma ku yadda dasu?..”yana rufe baki Mummy tace”kaine ya kamata ka hakura kodon sbd su Miemie din..duk yanda muka kai da rashin sonsu fa bamu isa mu rabasu da yaran nan tunda jininsu..snn kuma kowa ya kallesu yasan sunyi regretting abunda sukayi so don me bazamu yafe musu ba?..meyasa bazamu yafe musu ba tunda sukazo har gida neman a yafe musun..kada ka manta ubangiji da kanshi yana son masu yafiya..idan ka kasance mai yafiya sai Allah kaima ya yafe maka..baka tunanin ko don wnn ya kamata a yafe musu?..”shiru kawai Bobby yayi yana sauraronta amma shidai harga Allah baiga dalilinda zaisa kawai daga zuwansu su wani ce sun yafe musu ba..juyawa gareta sai yaga ta daure fuskanta tsaf dan haka yayi kokari ya sassauta nashi tareda yin kasa da nashi muryan kafin yace”Allah ya baki hakuri Mummy..ba haka nake nufi ba”..sassauta nata muryan itama tayi before tace”kuma anjima inason mgn dakai”..a hankali ya amsa mata da”toh”..snn Mummy ta mike ta bar masa dakin shi kuma ya rage kayan jikinshi ya fada bathroom yana sake tunawa da Lamido da duk abubuwanda suka shiga tsakaninsu yau..ya lumshe ido yana sakin wani murmushi daya tuna yanda yayi hugging dinta..he felt kaman ya rike ‘yar jaririya sbd taushin jikinta..ga wani qamshi da shidai bai ta6ajin irinshi ba sai daxu a jikinta..baisan lokacinda daria ya su6uce mishi ba daya tuna yanda ta gwalo idonta a lokacin..yasan she was shocked amma da yake tanada positive mind sai batayi thinking negative a kanshi ba sai ma yabonshi da tayi..shi tunda yake bai ta6a sanin haka mutum kejin dadi idan an yabeshi ba sai yau din nan kuma a kanta..lokacin data yabeshi sai yaji kaman duk dunia ko kowa bazai yabeshi ba nata kadai ya isheshi…nata kadai ya isa yasashi farin ciki…har ya gama wanka ya fito bai dena tunaninta yana sakin murmushi time to time ba…koda ya gama shiryawa sai yayi kwanciyarshi nan cikin dakin yaki fita sbd yasan kilan wadan nan mutanen suna nan basu tafi ba shi kuma baison haduwa dasu dan haka gwara yayi kwanciyarshi a daki…wayanshi ya dauki ya shiga gallery dinshi hoping inama zaiga pictures dinta amma babu..bayada pictures dinta ko daya amma yanada bukatar ya samu ko guda daya ne sbd irin wnn lokacin..kunna data dinshi yayi ya shiga whatsApp wai ko zai ganta online amma she’s offline…ya duba status dinta nan ma batayi updating komai ba sai wani short video na wasan PSG da Manchester..dan ta6e baki yayi cikin ranshi yana ayyana dole ma ya rabata da kallon ball din nan wlh..shi bazai dauki ta wani dinga son ‘yan ball tana supporting dinsu ba..hakan 6ata mishi rai yakeyi sosai…kashe data dinshi yayi ya ajiye wayar ganin har lokaci bata online…yana ajiyewa kuma kiran Nur ya shigo wayan dan haka yayi picking yasa a speaker yana sakin wani murmushi yace”Dr Nuruddeen Ugo”..daga daya 6angaren Nur ya wara idanu yana fadin”ah lallai abu ya tafi yanda ya kamata i don’t even have to ask”…Bobby yace”of course..ka kayuta sosai daka kawomin ita thank u”..da sauri Nur yace”always welcomed angon Lamido..yanxu a bani labari in detail inji abunda ya faru”..murmushi Bobby ya kara saki yana shafa beard dinshi hadda su lumshe ido yace”ka bari kawai Nur..sai yanxu na fara yadda da mgnrka..tanada hankali sosai”..Nur ya fashe da dariya before yace”bana fada maka ba?..tanada hankali wlh kawai idan ba zama kayi da itaba bazaka fahimci hakan ba”..Bobby na gyada kai zai sake wani mgn Ilham ta shigo dakin tace mishi Mummy na nemanshi..sallama yayi da Nur snn ya janyota yana kallon yanda har yanxu bata gama maida jikinta sbd rashin lafiyan da tayi ba yace”mutanen nan sun tafi ko suna nan?..”ilham tace sun tafi dan haka ya mike rikeda hannunta suka fita parlor…Mummy kadai ya samu a parlon ya karasa ya zauna yana kokarin zaunar da Ilham kan laps dinshi Mummy tace”kyaleta taje wurin su Miemie mgn zamuyi ai”..ba musu ya saketa fa nufi parlon aunty…Mummy ta maida hankalinta gaba daya gareshi fuskanta ba yabo ba fallasa tace”ya mgnr zuwa duba Waziri?..”wani irin damm yaji gabanshi ya fadi amma bai bari ta lura ba yace”za..zamu..je mana Mummy..ba kince yana india ba?..”yana rufe baki tace”an dawo dashi jiya..yana nan a Abuja kuma wnn satin nakeso kuje ku duboshi”..Bobby ya hadiye wani irin yawu kafin ya tattaro abunda zai fada mata yace”kenan..Gombe zamuje..mu dubashi?..”kallonshi Mummy tayi rai a dan 6ace tace”bakaji nace yana Abuja bane?..”da sauri yace”yi hakuri Mummy banji ba..amma why not a bari next week sai muje”..tun kafin ya rufe baki Mummy tace”ban yadda ba wnn satin nakeso kuje ku dubashi..idan kuma kanaso ka nunama dunia ban isa dakai bane Bismillah”..kallonta kawai Bobby yake yana mamakin sudden change din nan nata..Mummy ba mace ce mai fada ba sam..zaiyi wahala kaga tana fada musamman ma shi amma yanxu gashi ta daure fuskanta tana mishi fadan akan mutanenda bai daukesu a bakin komai ba..mutanen da basu ta6a kaunarsu tsakani da Allah ba tun mahaifinsu ma yanada rai…yasan duk wnn abun tanayi ne sbd kar yayi mata gaddama kaman yanda ya sabayi a baya amma shidai har yanxu baiji zai iya zuwa wani duba waziri ba..Wazirin da shi kanshi ba kaunarsu yake ba…ganin yanda yayi shiru ya wani kafeta da ido tace”bazaka jeba knn?.”da sauri yace”aah ba haka bane Mummy..zanje..amma in…”bata bari ya karasa ba ta dakatar dashi da fadin”kaje ka fara shiru this coming weekend zakuje gaba dayanku ku duboshi”..kallonta yake yace”gaba dayanmu kuma?..wai kina nufin hadda su Miemie?..”kai tsaye tace”ko su ba jininshi bane da baza suje dubashi ba?..”a hankali yace”amma Mummy su meye hadinsu da Waziri da zasuje duboshi”..kallonshi Mummy keyi cikeda takaici tace”kaidai idan bakayi wasa ba sai Allah ya kamaka da laifin yanke zumunta..su Miemien zakace meye hadinsu dashi sbd bakada hankali?..”shiru kawai yayi yana kawar da kai shidai harga Allah wnn abun da Mummy keson tursasa su suyi bai gamsheshi ba..kilan ma suna zuwa Wazirin yasa koresu yace bayaso ya sake ganinsu har abada…ita kuwa Mummy ganin idan tacigaba da zama tana mgn dashi 6ata mata rai kawai zaiyi sai ta mike bayan ta gama mgnrta ta wuce zuwa 6angarenta…sbd iskanci zai wani ce a bari ba yanxu ba sai azumi ya shigo knn yakeso suje dubiyan nashi ko sai bayan sallah?..ta rasa wane irin taurin kaine da Bobby da ko ita data haifeshi watarana bya tankwaruwa ta dadi a wajenta?…yana ganin ta shige ciki shima ya mike zuwa flat din aunty sumy..he need to talk to her about this ko zata iya lalla6a musu Mummy ta bari sai bayan sallah tunda yanxu dab ake da fara azumi…yana shiga kai tsaye bedroom dinta yaje ya kwankwasa kofa ta bashi izini snn ya bude kofar ya shiga…a zaune ya sameta tsakiyar gado tana aiki da system dinta..ya isa ciki ya zauna kusada ita yana dubanta a hankali yace”mgn nakesonyi daks aunty sumy”..ba tareda ta dago ba tace”to ina sauraronka Uncle Bobby”..dan 6ata rai yayi yana kallon kaman zaisa kuka yace”aunty plss be serious mana..please!..”ajiye system din tayi tana dubanshi da murmushi tace”to yi hakuri..ina jinka”..gyara zama yayi kafin yace”Mummy ce take mgnr zuwa dubiyan Waziri”..ajiyan zuciya ta saki kafin tace”kaima ta fada maka knn?..”yace”ta fadamin..yanxu ya kike ganin zamuyi?..nidai bana son zuwa inda suke kwata kwata..bana son ganinsu”..kallonshi aunty sumy keyi kafin ta sake sauke wani ajiyan zuciya tana cewa”na fuskanci wnn karon Mummy da gaske take kan mgnr nan..idan mukace zamuyi kokarin kaucewa umarninta muna iya samun matsala da ita”..shiru Bobby yayi yana nazari shi kanshi yaga alaman hakan zai faru amma ya zasuyi?..yace”yanxu knn kina nufin bamuda wani option dole sai munje?..”gyada kai tana cewa”gaskia dai kamar bamuda wani option din..kasan yanda Mummy take da damuwa Bobby idan bamuyi abunda takeso ba muna iya sawa ta samu wani matsalan kuma kasan yanda bp dinta yake..baason tana shiga damuwa da yawa”…shiru ya sakeyi yana nazari..tabbas mgnr data fada gaskia ne…yasan yanda ta kwallafa rai kan sai sunje din nan idan sukace zasuki zuwa tsaf zata iya sama kanta damuwa har jinin nata yazo yana hawa shi kuma abunda baiso knn har abada…ajiyar zuciya ya sauke tareda runtse ido yasan wnn karon kam bashida wani hanyan tsira..duk wani kauce kauce bazaiyi tasiri akan Mummy ba wnn karon tunda har tasama ranta sai sunje dole…haka nan zai hakura yaje domin mahaifiyarshi amma wlh ba donshi wazirin ko don wani daga cikin ‘ya’yanshi ba…aunty sumy ta dafa hannunshi cikin sigan lallashi tace”haka nan zamu hakura muje wnn karon..koba komai zamu samu ladan da su bazasu ta6a samuba sbd kin nemanmu da sukayi na tsahon shekaru”..gyada kai kawai ya iyayi tareda mikewa ya fita daga dakin…tabbas zasuje amma ba don wani daga cikinsu ba sai domin Mummy..sbd gudun 6acin ranta daka iya haifar mata da matsala amma ba sbd su ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button