Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Tun daga wnn rana masoyan suka shirya abunsu..soyayya Kuma sai sake karfi yakeyi a tsakaninsu ta yanda basa iya complete 2 days ba tareda ganin juna ba..abun har mamaki yake bata yanda takejin sonshi a kowane lungu da saqo na zuciarta..kullum yana kan hanyan zuwa ganinta don kullum sai ta fara shiga college ya ganta kafin ya wuce hospital..zuwa yanxu hatta students daidai ne basu san irin soyayyan dake tsakaninsu ba…a daya 6angaren kuma shirye shiryen council sukeyi sosai don few months yanxu ya rage musu su fara..kowa ya maida hankali matuka wajen karatu sbd yayi passing…specialist aka dauko ta fannoni daban daban suke musu extra lesson kullum a cikin college din kan duk wani abu daya shafi council exam tun daga kan theory har zuwa kan practical..sosai Kuma suka maida hankalinsu suna koya wnn dalilin yasa har weekends suna shiga school sbd lessons din da sukeyi.

A 6angaren shirye shiryen bikinsu nan na ba’a cewa komai don both bangarori nata shiri sosai na bikin da baifi saura 4 weeks ba yanxu…su Mummy sun gama hada lefe lokaci kadai suke jira su dauka su kaisu wajen waziri da yace har ita Mummyn yakeso suzo wai da akwai mgnr da zaiyi da ita.

A 6angaren bride and groom Kuma za’a iya cewa ba wani shiri da suke don ita tana fama da karatu exams dinta dake sake approaching yayinda shi Kuma ya maida hankali sosai wajen ganin tayi passing exams din nata..har extra lesson yakeyi musu ita da Billy kan duk wani abu daya shige musu duhu..sosai Kuma suke fahimta dan da gaske ya iya koyarwa..wani lokaci har class din nasu yake zuwa yana koyar dasu wani abun during weekends haka sbd ya taimakawa Nur da shima duk wani attention dinshi ya dawo garesu.

Yau ma kmr kullum bayan sun gama lesson da yayi musu office dinshi Billy tayi sallama dashi ta fita ita Kuma Aysha na zaune tana kallonshi ganin ya zuba mata ido ya kasa cewa komai..turo baki tayi tana rufe fuska da hannaye ta tace”ni ka dena kallona”..dan murmushi ya saki yana shafa gashin kanshi yace mata”gobe zamuje Gombe”..bude idon tayi da sauri tana kallonshi lokaci daya ta kwabe fuska kmr zata sa mishi kuka tace”partner nima inaso inje plss”..girgiza Kai yayi yana cewa”kiyi focussing kan exams dinki dan Allah”..tun bai rufe baki ta make kafada tana turo baki tace”nidai i want to follow u plss”..kama hannunta yayi ya dawo da ita kusa dashi ta zauna yana facing dinta yace”kinga fa bani kadai zanje ba..tare dasu Mummy zamuje..Kuma ba daddy yace ki bari ki gama exams dinki ba”..baki ta sake turowa tace”to shine Kai zakaje ka barni?..”yace”ai ba jimawa zamuyi ba love believe me..ba dan Waziri da kanshi yace yana nemanmu ba da bazan iya zuwa in kyaleki a nan ba kema kin sani”..kallonshi kawai takeyi hawaye na ciko idonta ta dora kanta a shoulder dinshi tana rikeda hannunshi tace”am going to miss u”..shafa kanta yayi yace”nima i will miss u amma ko kwana biyu bazanyi ba zan dawo trust me”..Kai kawai ta gyada mishi tana sake lafewa a jikinshi..hannu yakai ya dagota daga jikin nashi sbd wasu abubuwa da suka fara kai kawo a cikin jinin jikinshi ya shiga goge mata tears dinta yace”to yaushe zamuje kiga kayan naki?..”makale kafada tayi alaman bazata jeba..yace”to gidanki fa shima bazaki je ki gani ba?..”sake makale kafada tayi tana wani turo baki..Bobby daketa kallonta with adoration lumshe ido yayi tareda matsawa yayi pecking forehead dinta kafin ya dago yana rike da hannayenta yace”I love u so much”..murmushi ta saki itama da wet face dinta tace”i love u too”..kallon dimples dinta yayi kafin yakai fingers dinshi a dora both dimples din nata yana kallon tsakiyar idanunta yace”suma ina sonsu sosai”..murmushi ta kara saki dimples din ya sake fitowa baisan time din da ya lumshe ido ya sake pecking cheeks din nata ba..he loves this girl to the core..yana jin sonta a duk wani numfashi da yake shaqa a doron kasa..soyayyarta a cikin jininshi yake.

Washegari da safe suka dauki hanyan Gombe su uku..Mummy,Bobby sai aunty sumy..sai da suka fara tsayawa Police Academy Wudil wajen Sab snn suka wuce Gomben…lokacinda suka isa was around 12..bayan sun isa gidan Waziri yasa aka fito da kayan da suma mota guda akayi musu suka shiga dasu parlonshi..Saida ya gama ganin uban kayan snn yace da Mummy”kunyi kokari sosai Allah ya saka da alkhairi..amma banaso ku sake yin komai kan harkar bikin nan..duk wani abu da yayi saura tun daga kan sadaki har zuwa duk wani abu da za’ayi spending lokacin biki ni na dauki nauyinshi..kaima Attahiru ban yadda ka sake yin komai ba ni da kaina zanyi maka duk abunda ya kama in Allah ya nuna mana”..cikeda farin ciki Mummy tace”Muna godia Baffa Allah ya saka da aljanna”..Waziri yace”Ameen..mgnr kai lefe kuma nayi mgn da Baffaninka da kansu zasu dauki kayan su kaiwa Lamido dan haka ba sai mata sun shiga lamarin ba”..nan ma godia suke sakeyi Bobby ji yayi ya rasa inda zai sa kanshi sbd farin ciki..wato dai zumunchi ba karamin abu bane a rayuwa..dunia mutum baya da tamkar ‘yan uwanshi shiyasa no matter the situation bazaka ta6ajin ance wane ya canxa ‘yan uwa ba..dan uwanka dole dan uwanka ne komai rigimar da zakuyi dai bazai canxa wnn suna ba shiyasa ake son mutum ya kasance mai juria da Kuma hakuri da ‘dan uwanshi..(Allah ka bamu ikon rike zumunchi har karshen rayuwarmu).
Bayan sun dan nisa Waziri ya sake cewa”sai Kuma mgn ta biyu da nakeso muyi”..Mummy ce tace”Muna sauraronka”..Waziri ya gyara zama tareda maida duba ga aunty sumy ya kira sunanta”Sumayya”..a hankali tace”na’am”..yace”kinada masaniyar zuwan tsohon mijinki wajena kan batun maida aurenku?..”girgiza kai aunty sumy tayi alamar aah..Waziri yace”to yazo nan ya sameni tareda wani kawunshi..ya sanar dani duk abunda suka faru a tsakaninku ya kuma bani hakuri tareda neman alfarmar in roka masa ke ki amince ki koma dakinki..nace masa bazan yanke hukunci ba saina farajin ta bakinku dan haka kuje kuyi shawara a tsakaninku idan kun amince ta koma Alhamdulillah idan kuma baku amince ba wanda zaiyi mata dole”..gaba daya shiru sukayi tamkar basuji abunda yace ba..Mummy ce ta fara breaking silence din da cewa”nidai ta 6angarena banida wani matsala da haka domin mahaifiyarshi har gida tazo ta nemi gafarar mu kuma muka yafe mata..dan haka indai taga zata koma din nima zanfi son haka ko don sbd zuri’a dake tsakaninsu”..gyada kai Waziri ya shiga yi yace”wnn haka yake..kai kuma Attahiru menene shawararka akan haka?..”dan murmusawa yayi yana shafa kanshi yace”Baffa nima indai ta amince shknn”..da mamaki aunty sumy ta juya tana kallonshi jin yace ya amince kmr dai ba Bobby da har sim card yake canxa mata sbd Isma’il din ba..lallai Bobby ya canxa sosai ba kadan ba..ta tabbata da ada ne akayi mashi wnn tambayar kanshi tsaye zaice bai amince ba amma wai shine da cewa in ta amince shknn..lallai wonders shall never end..har gobe bata dena mamakin sudden change din nan nashi ba..ta fuskanci tun da ya fara son Lamido zuwa haduwa da Waziri ya sauya daga Bobby mai kafiya,taurin kai da kuma riqo zuwa Bobby mai sauki da kuma sanyin hali kan abubuwa da dama ciki hadda yafiya da kuma mancewa da tarin laifukan mutun da tunawa da alkhairinsa komai qanqantarshi…ganin tayi shiru ta kasa cewa komai Waziri ya sake Kiran sunanta..ta amsa kanta a kasa duk bata San ma amsar daya kamata ta bashi ba..shi Isma’il din na meye zai wani xo har wajen waziri ba tareda ya fara mgn da ita yaji ta bakinta ba..Waziri yace”na baki nan da sati biyu kiyi tunani akai..idan kin amince sai a hada auren naki dana ‘dan uwanki a daura rana daya”..ba tareda ta dago kanta ba tace”na amince Baffah..Allah yasa haka shine yafi alkhairi”..cikeda farin ciki Waziri yace”Ameen Allah ya maku albarka..Allah Kuma yasa ayi lafia a gama lafia”..duk suka amsa da Ameen..daga nan kuma suka shiga cikin gidan don su huta kafin gobe kuma su sake daukan hanya su koma Kanon Dabo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button