Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

kuwa.

A hankali ya bude idonshi daga nannauyan baccin daya daukeshi as a result of drugs dinshi da yasha..duba yakai ga agogon dakin yaga it’s almost five dan haka ya sauka daga gadon da sauri ya fada bathroom yayi alwala ta fito snn ya tada sallah yana jin haushin rashin tashinshi da sukayi har time din sallah ya wuce…yana idar da sallah Sab ya shigo dakin yana dubanshi yace”waziri yace wai ya jikinka?..”mikewa yayi daga inda yayi sallahn yace”da sauki..muje”..tare suka fita zuwa parlon waziri shi da Sab din…yana ganinshi ya saku murmushi tareda furta”jiki yayi kyau knn?..”murmushi shima Bobbyn ya sakar mishi har suka karasa ciki..nan kusada wazirin ya zauna yana dubanshi da murmushi..so yake ya tambayi ko sunyi mgn da Lamidon amma baisan ta yaya ba…bayan waziri ya sallami baqin dake tare dashi ya shiga duban Bobby fuska da murmurshi sosai yace”zaka iya rakani wani waje yanxu?..”a hankali Bobby ya daga mishi kai alaman zai iya..waziri ya maida dubanshi ga Khalid dake zaune parlon shima yace”kaje kace a fitomin da mota”..ba musu khalid ya juya ya fita shi kuma waziri ya mike tsaye tareda kama hannun Sab yace”kaima muje kayi mana rakiya mai sunana”..a tare suka fita duk su ukun zuwa motarshi da har an fito da ita…makullin motar ta kar6a daga hannun driver dinshi ya mukawa Sab yace yayi driving dinsu…ba musu Sab ya amsa key din dukda cewa baisan kan garin sosai ba…ya bude driver seat ya shiga su kuma suka shiga baya snn ya tada motar suka fita daga gidan…saida suka hau babban titi Waziri yace”zaka iya gane Gra?..”a hankali Sab yace”da kyar zan gane gaskia”..gyada kai waziri yayi yace”to muje zanyi directing dinka”..haka kuwa Sab yaja motar suna tafe yana nuna mishi hanya har suka shigo Gra…suprise yakeso yaima Bobby shiyasa bai sanar mishi inda zasuje ba..yaso ace yareda uncles dinsu sukazo amma bazai iya jira har su dawo daga aiyukansu ba shiyasa yaga gwara ya fara zuwa shi kadai suyi mgn gemu da gemu da Lamido inyaso daga baya sai su sake dawowa tareda ‘yan uwan mahaifinshi don kawo dukiyar aure…waziri nacigaba da nuna ma Sab hanya har suka iso Lamido’s Palace…wani irin bugu zuciyar Bobby yayi da yaga an rubuta The Lamido’s 6aro 6aro a can saman gate din estate din…duk fadin Gombe kuma yasan Lamido ne kadai mutuminda yayi suna da sunan sosai dan haka ba tareda wani tantama ba brain dinshi ya fada mashi cewa wnn estate dinsu Lamido ne…lumshe ido yayi tareda jingina da kujera knn hakan na nufin Waziri zuwa yayi suyi mgn da Lamido?..wani irin faduwa gabanshi ya sakeyi daya tuna cewa fa tayi bata sonshi..yanxu idan sukaje ta sake tozartashi tace bata sonshi fa?..hankalinshi yaji ya tashi har wani zufa ya faraji na ba gaira babu dalili amma yayi kokari bai bari waziri ya fahimta ba har aka bude musu gate suka shiga ciki…tafia sukayi ba wani mai nisa da yawa ba suka karaso gidan Lamido…daga nan waje Sab yayi parking motar snn duk suka bude suka fito…suka sanya waziri a tsakiya suka shiga cikin gidan…daidai entrance suka hadu da wani brother din daddy ya fito daga parlon Lamido yana ganin Waziri yayi saurin dunkule hannu tareda risinawa yana fadin”Allah ya taimaki Waziri…barka da zuwa”..Waziri ya amsa da”barka dai Mahmoud..ya iyali?..”Mahmoud Lamido yace”suna lafia lau Waziri..a fito lafia”..Waziri ya gyada mishi kai yana murmushi..sai a snn Bobby da Sab suka gaishe da mutumin snn sukabi bayan Waziri zuwa cikin parlon…Lamido na ganinsu ya fadada murmushin fuskanshi yace”Waziri ne a tafe?..”Waziri daya karasa ciki ya zauna kan one of kujerun dake parlon yace”wlh nine Lamido”..Lamido yace”to barka da isowa”..Waziri yace”yauwa..ga jikokinka nan na kawo makasu har gida”…kallonsu Bobby Lamido yayi yana cigaba da murmushi yace”yaran Attahiru koh?..”Waziri ya gyada mash kai shima yana murmushi…Bobby ne ya fara gaisheshi kai a kasa sai Sab shima ya gaisheshi…bayan gaisuwa Waziri yace”jiya na kira wayarka ai”..Lamido yace”na gani wlh..lokacin ne ina tareda Ahmad kan batun auren ‘yarsa daya taso shiyasa banga kiran naka bama sai daga baya”..waziri na gyada kai yace”ikon Allah watace zatayi aure cikin yaran nashi?..”Lamido yace”babbar ce wai ta turo a sanar dani wani dake neman aurenta yanaso ya turo shine nace ta dakatar dashi dan na riga nayi mata miji tun tuni”…wani irin faduwa gaban Bobby yayi kirjinshi sai up and down yake fatanshi bai wuce Allah yasa ba akanta ake mgn ba…shi kanshi waziri zuwa yanxu gaban nashi faduwa yake yace”wacce daga cikin yaran wai?..”kai tsaye Lamido yace”Aisha mana..ina wnn yaro Najeeb?..”Waziri yace”dan wajen marigayi Auwal koh?..”Lamido yace”yauwa to shine wanda na za6a a matsayin mijin nata..kasan ubanta shi ya rike Najeeb din kuma nasan ba wanda zai iya zama da ita sai shi shiyasa na tarasu na fada musu ko bayan raina ban yadda a fasa wnn auren ba”…wani irin tari ne ya sarke Bobby kaman wanda ya kware da wani abun…hankalinshi yakai kololuwar tashi har wani zufa ya faraji all of a sudden ga kuma coughing da taketa faman yi non stop..nan take hankalin Waziri ya tashi shima..Sab ya rikoshi yana yana shafa bayanshi amma kmr tunzurashi suke don cough din sai karuwa ma da yayi…da sauri Waziri ya mike yana duban Sab hankali a tashe yace”kamoshi muje asibiti”…Lamido ya mike shima yana dubansu yace”ina zuwa”..daga haka ya shiga wani corridor dake nan cikin parlon..bayan few minutes ya fito rikeda goran zamzam da akayima addu’a a hannunshi..yana karasowa ya bude tareda kafa goran a bakinshi nan da nan kuwa ya shiga shan ruwan kaman an aikoshi…saida tasha almost half snn ya cire baki tareda yin kasa da ido yana sauke numfashi…hawaye ne sosai suke cikowa idonshi amma bayason su zubo…bayason ko waziri yaga wnn tears din sbd ya gaji da zubar da hawaye a gabansu…zuciyarshi wani irin rauni tayi mashi wanda bata ta6ayi masa irinshi ba…kokari yake sosai na ganin ya 6oye abunda yakeji amma abun yaci tura sbd bashi keda control din kanshi ba…runtse ido yayi yana maimaita innalillahi a cikin zuciyarshi har yanxu kuma bai denajin hadadden zufa na lullu6eshi ba…kallonshi Lamido yake cikeda mamaki yace”meya sameshi ne haka?..”Waziri ne yayi karfin halin cewa”dama baida lafia don daxun aka sallamoshi daga asibiti..ina ganin zamu tafi kawai a sake maidashi can”…da sauri Lamido yace”a maidashi gaskia don wnn tarin nashi bana lafia bane..Allah ya baka lafia Attahiru”..ya karasa mgnr referring to Bobby dake dafe da chest dinshi da hannu daya dai kuma daya hannun ya dafe head dinshi da yaketa jujjuyashi from side to side…Sab har ya fara hawaye shima a haka ya kamashi zuwa inda yayi parking mota..bude baya yayi ya sashi ciki snn yayi saurin zagawa zuwa driver seat Waziri kuma ya shiga baya suka tafi…kai tsaye asibitin da suka baro daxu ya shiga nuna masa suka maidashi.

Aysha kuwa yini tayi daki tana kuka ba wanda yabi ta kanta saida su Husna suka dawo..sune sukaita tambayanta meya faru amma ta kasa ko bude baki balle tayi musu bayani…ganin abun nata bana kare bana kare bane gashi har dare zaiyi bata fito taci abinci ba daddy dake parlonshi ya kira Ammi yace mata”Maimunatu je ku duba yarinyar can don Allah..wnn kukan da take ai saiya haifar mata da ciwon kai”..ajiyar zucia Ammi ta sauke Allah ya sani itama tun daxu takejin kmr taje ta rarrashi kayarta amma sbd kara irin nasu na fulani kasa zuwa tayi…yanxu kuma da daddy yayi mgn da kanshi ko musu batayi mashi ba ta kama hanyar dakin nasu…su Husna na zaune sun sanyata tsakiya tana fada musu cewa Lamido ne yace zai hadata da Hamma Najeeb aure..Husna da bataga wani abun tayar da hankali a mgnr ba tace”to Adda wnn ne abun kuka kuma?..Hamman da kinfi kowa sanin halinshi ne kike kuka sbd zaki aureshi?..ai murna ya kamata kiyi ma”..Husna na rufe baki Ammi data shigo dakin tace”Husna kuje parlor ku jiramu zamuyi mgn”..ba musu Husna ta kama hannun Yusra suka fita…suna fita Ammi ta zauna nan kusada ita tareda kama hannunta ta rike kafin tace”ki tsayar da kukan nan mgn zamuyi”..ba musu takai hannu tana share hawayenta…Ammi na dubanta da kyau tace”bakya son Najeeb din ne?..”da sauri ta shiga gyada mata kai alamar eh..janyota Ammi tayi ta rungume a jikinta tana shafa bayanta tace”to ki dena kukan nan indai baso kike kisama kanki ciwon kai ba..so nake ki kwantar da hankalinki zamuyita addu’a inshaAllah idan ba alkhairi bane Lamido da kanshi zaice ya janye mgnr”..luf Aysha tayi jikin mahaifiyar tata tana sauke numfashi..wato dai duk dunia babu inda ake samun irin wnn nustuwan sai wurin uwa…hankalinta taji ya dan kwanta unlike daxun da take ganin duk tashin hankalin dunia a kanta ya kare…kawai har yanxu ta kasa picturing itada Hamma matsayin mata da miji…jin yanda tayi tsit Ammi ta dagota daga jikinta tana sake rike hannunta tace”kinji abunda na fada maki koh?..”gyada kai tayi a hankali Ammi tace” yauwa kuma banaso shima Najeeb din kice zaki nuna masa wani abu..kucigaba da mu’amalarku kmr da inshaAllah indai ba alkhairi bazaki aureshi ba”..sake gyafa kanta tayi tana fatan Allah yasa ba alkhairi din…mikewa Ammi tayi itama ta mikar da ita tsaye tana cewa”muje to kici abinci..haka nan yau duk kinbi kin dorama kanki damuwa ko abincin bakici ba”…daga haka Ammi ta shiga janta suka fita daga dakin..Lamido dai mamaki fal cikin zuciyarta na ganin yanda Ammi take lalla6ata yau..anya kuwa ba kofar rago ake shirya mata ba?..tasan dai yanda Ammi take da zafi zaiyi wahala tazo ta rarrasheta haka kawai…sai kuma wata zuciyar tace mata kilan sbd tasan ba’a kyauta mata bane shiyasa take haka…ko su Husna dake zaune parlor abun ya basu mamaki ganin Ammi rikeda hannun Addarsu har dinning…ba wai Ammi bata sonta bane no kawai dai basu cika jituwa bane sbd halayen Ayshan da kusan gaba daya basu mata ba..ga kuma kasancewarta ‘yar fari shiyasa abun ya hade mata biyu amma yau ga Ammi rikeda hannun ‘yarta sai sukay kaman wasu qawaye…daddy daya fito don tafia masjid ya hangosu a dinning Ammi na kokarin serving dinta sai ya saki murmushi hade da girgiza kai snn ya fita daga gidan…Maimunatu sarkin kara yau an ajiye karar a gefe knn…yaji dadin yanda yaga Ayshan har ta dan sauko shiyasa akace dai duk fadin dunia mutum baida wanda ya wuce mahaifiyarshi…babu wanda zai soka kaman ita haka kuma babu wanda zai ji tausayinka ya kuma damu da damuwarka kamar mahaifiyarka…itace zata soka kilan fiyema da yanda kake son kanka..(Rabbi ya sakawa iyayenmu da alkhairi ya basu aljannah).????????
Saida Ammi ta tabbata taci abincin da yawa snn tace taje tayo alwala ta sameta dakinta…ba musu ta wuce dakinsu tayi alwalan snn ta fito..su Husna suma duk alwalan sukayi snn suka wuce bedroom din Ammi kamar yanda tace musu su sameta a can…a tare sukayi sallahn nasu gaba daya bayan sun idar Ammi tace duk su sa ‘yar uwarsu a addu’a idan akwai alkhairi tsakaninta da Najeeb Allah ya tabbatar idan kuma babu Allah ya kawo mafita..Aysha dai sam ba wnn addu’an takeso ayi ba tafiso kawai suce Allah ya kawo hanyarda fasa auren inyaso sai kowa Allah ya hadashi da alkhairin nashi a gaba…zata iya hakura da auren baby amma bazata iya auren Hamma da take mishi kallon dan uwanta da syka fito ciki daya ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button