Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Suna shigowa hospital din Miemie ta fita da sauri zuwa office dinshi ta banka ta shiga ko sallama batayi ba ta fada mashi halinda ake ciki..yanda ya fito a rude har mutane saida sukayi mamaki dan lokaci daya yaji komai nashi yayi tsaye cak..da sauri ya karasa inda motar yake ya bude back seat nan ya ganta jingine jikin seat din idonta na fitar da hawaye..hannu yakai ya ta6a forehead dinta yaji still da zafi a jikin kawai sai ya dauketa a hannunshi ya fito da ita daga motar zuwa cikin asibitin..sauri kawai yakeyi ya karasa office dinshi bai ko damu da kallon da jama’a ke binshi dashi ba..yana shiga ya kwantar da ita kan gado snn ya cire mata hijabin jikinta kawai sai ya tsaya yana kallonta without saying anything..Miemie data shigo office din da sauri yace ta shiga bayi ta kawo mashi warm water da towel..ba musu tayi yanda yace ta kawo mashi yace taje driver ya maidata gida..shi kuma ya fara jika towel din yana shafa mata ruwan a jiki sbd temperature nata ya sauka..bayan ya gama ya fita zuwa pharmacy da kanshi ya kar6o drip da allurai snn ya koma office din nashi..tana ganin drip da allurai hannunshi ta fara kuka shidai bai iya ce mata komai ba ya samu ya lalla6a yasa mata drip din don yasan ba wani abinci zata iyaci ba..yana gamawa ya mata alluran da zaiyi saurin saukar mata da fever din snn yaja seat dinshi ya zauna nan kusada ita yana kallonta..Aysha na kuka sosai tace”partner am so sorry plss”..hannunta ya kama ya rike cikin nashi baidai ce mata komai ba..mikewa ta shiga kokarin yi shi kuma yayi saurin maidata yana nuna mata cannular dake hannunta yace”careful mana”..komawa tayi ta kwanta tanacigaba da kallonshi tana hawaye..shima kallonta yakeyi yanajin wnn abun da yazo ya tsaya mashi a throat dinshi tun jiya yasan indai ba mgn ya samu yayi da itaba wnn abun bazai fada ba dan haka ya dan runste eyes dinshi kafin a budesu a kanta voice dinshi kasa kasa yace”so da gangan kikayi hakan koh?..”da sauri ta hau girgiza kai tace”wlh coincidence ne..i never knew such thing will happen am sorry”..yace”but u even hugged him..why did u do that?..”tace”i thought it was u sbd eyes dina a kulle suke saida naji perfume dinshi ba irin naka ba nasan u are not the one..kayi hakuri ka yafemun dan Allah”..ta karasa mgnr tana kuka sosai..shiru kawai yayi yana kallonta yasan shima yayi over reacting jiyan nn amma it wasn’t his fault..sake matsawa yayi yuana rikeda hands dinta yace”nima am sorry for reacting the way i did..i shouldn’t have done that so kiyi hakuri”..kai kawai take gyada mishi..ganin yanda har jikinta na rawa sbd kukan da takeyi yace she should stop talking zasuyi mgn anjima..sosai ya sake bata hakuri yana cewa yasan bai kyauta ba..itama tace mishi ko dan gaba if wani abu irin wnn ya faru saurin fushi bayada amfani gwara su zauna suyi communicating that communication is a solution to any problem..shiru kawai Bobby yayi yana kallonta dan kunya yaji sosai wai itace take fada mashi what is right..sauka ajiyar zucia yayi yana ayyana idan fa bai dena wnn saurin fushi da zafin ran ba watarana zaiyi dana sani duk sai yaji jikinshi yayi sanyi yace inshaAllah zaiyi kokarin gyarawa kuwa..ita kuma tayi shirun bata sake mgn ba har drip din ya kare zuwa lokacin kuma fevern dake jikinta ya dan sauka shima sai a lokacin ya dan samu peace of mind..a hankali ya mike zuwa inda wayanshi keta ringing ya dauka snn ya samu wuri ya zauna bayan yayi picking call din..a daya bangaren Nur yace”hey are u at the office?..”kmr bazaice wani abu ba sai can yace”what?..”Nur yace”just answer me dan rainin wayo”..lumshe ido yayi yana kallon inda take kwance kafin a hankali yace”ina nan”.. Nur yace”ohk gani nan zuwa”..daga haka ya ajiye wayar tareda mikewa zuwa inda take ya maida mata hijab dinta yana cewa”do u need anything?..”a hankali ta girgiza mashi kai alamar no..yace”bazaki ci komai ba?..”nan ma kan ta sake girgiza mashi yace”bari Nur yazo idan ya tafi sai in maidaki gida tunda zazza6in ya sauka”..kai kawai ta iya gyada mashi shi kuma ya fita daga office din..can parking space yaje ya tsaya tana jiran isowar Nur bai dade da tsaiwa ba kuma sai ga Nur din ya karaso..bai bari ya karaso nan inda yake ba ya nufi wurin motar shi..yana zuwa ya bude ya shiga tareda relaxing yana kallon Nur din a hankali yace”daga ina kake haka?..”maimakon ya bashi amsa sai cewa yayi”wai what’s wrong with ne?..u look disturbed..ina Lamido?..”a hankali Bobby yace”she’s inside”..Nur ya dan wara idanu yace”inside kuma?..yanxu wurin aikin ma saika taho da ita Bobby sbd gajen hakuri”..harara ya watsa mashi mai kyau tareda sakin wani tsaki yace”u are annoying wlh..to batada lafia kuma ni bana gidan shine aka kawota na dubata”..wani murmushi Nur ya saki yana shafa gemu yace”so meke damunta?..”Bobby yace”fever..amma nasa mata drip yanxu fevern ma ya sauka”..Nur na gyada kai yace”Allah bata lafia..amma why ba’a yi mata test ba?..”juyawa yayi ya kalleshi rai a dan 6ace ganin kmr neman zance kawai yakeyi yace”ban saniba”.. Nur ya kwashe da daria yana kallon abokin nashi yace”kaga malam ka maida wukar ka ni bani na kar zomon ba..am only trying to be of help”..a dan fusace Bobby yace”to hell with u and ur help”..kallonshi kawai Nur yake har yanxu bai bar murmushi ba yace”ohk let me keep quiet tunda bakaso..dama cewa zanyi kasa ayi mata pt kilan she’s pregnant”..da sauri Bobby ya juya yana kallonshi idanu a waje yace”what do u mean?..”Nur yace”Ina nufin kilan ciki ne da ita mana..kai ina ka taba ganin anyi haka kawai matarka ba lafia kazo ka wani farayi mata blind treatment baka tunanin ko karuwa ka samu”..wani irin diff Bobby yayi yana bin Nur da kallo kmr bai gane abunda yace ba..tunani ya tafi yi tabbas tunda akayi bikinsu bata ta6a period ba and idan ba wai manta lissafin yayi ba bikinsu saura 2 weeks tayi period and idan akayi adding two weeks to that shine ovulation period dinta kuma a daidai wnn time din akayi bikinsu so there is 90% possibility na zata iya samun cikin within wnn kwanakin sbd time din ovulation dinta ne..nan take fuskanshi ya washe da wani irin murmushi yana sake wara idanu akan Nur hannunshi dafe da bakinshi cikin tsananin farin ciki da kuma mamaki yace”oh my Goddess..why didn’t i think of this?..”harara Nur ya watsa mashi yace”oho banza”..sake juyawa yayi yana kallon Nur da kyau yace”Nur ina kyauta zaton wnn mgnr naka gaskia ne..she might be pregnant oh Allah”..ya karasa mgnr full of excitement kaman an tabbatar mishi tana dauke da cikin already..shi gaba daya tunaninshi baizo nan wurin ba all he was thinking was incident daya faru jiya har ya kulle mashi kai ya kasa zargin cewa cikin ne da ita..”ikon Allah”..ya sake fada out of excitement Nur dai na zaune yana kallon ikon Allah at the same time yana mishi daria..shi kanshi zai so ace yau Lamido tanada ciki ko dan yayi kallon uban rawan kan da Bobby zaiyi akan cikin…bude motar yayi ya fita shima Bobby ya fito da sauri ya kama hanyan cikin asibitin yana fadin”we need to conduct this test now..i pray it turn out to be truth”..Nur dake bin bayanshi ya amsa da”Ameen”..har suka shiga cikin building din..direct office dinshi suka shiga lokacin tana kokarin mikewa tsaye Bobby yayi saurin karasawa inda take yana kallonta full of love and excitement yace”baby where are u going?..”a hankali tace”ruwa zansha”..ruwan ya dauko da sauri ya kawo mata yana cewa”here u go”..ta saki dan murmushi snn ta amsa ruwan tasha cikeda mamakin sudden change din nan nashi?.. it’s like ya gama saukowa completely..saida ta gama Shan ruwan snn ta lura da Nur dake zaune kan sofa yana kallonsu..ta danyi kasa da kanta tace”sir Ina yini”..yace”lafia ya jikinki?..”tace”naji sauki”..yace”to Alhamdulillah”.. Bobby dai drawer ya bude ya dauko duk wani abu da zaiyi amfani dashi snn ya koma wurinta ya shiga lallabata wai zai dauki blood sample..itadai batace komai ba ya dauki sample din snn yaba messenger bayan ya rubuta test din da za’ayi a paper yace ya kai lab yace yana jiran result yanxun nan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button