Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Daren ranar daddy har sallahn dare yayi yana rokon Allah ya dorashi kan Lamido ya amince da mgnr da zaije mashi da ita..Ammi dai na kwance tana kallonshi har ya idar snn ta sake tambayanshi abunda ke faruwa…bai 6oye komai ba ya fada mata duk yanda sukayi da Uncle Lukman ya kuma fada mata yanda sukayi da Najeeb daxu..ita kanta Ammi tayi mamaki sosai jin wai sbd ita ma ya kwanta rashin lafia..bawan Allah ashe haka yake sonta ba’a sani ba…ita kanta zataso kasancewarshi sirikinta ko don yanda kullum daddy ke yabonshi yana fadar kyawawan dabi’unshi…tana duban mai gidan nata tace”amma daddy kana ganin Aysha tana sonshi kuwa?..naga wanda tace zai turo ai kmr bashi bane”..daddy yace”rabu da ita ko babu wnn mgnr ma bazata auri wancan din ba..wai ashe tsoho yarinyar nan taje ta dauko kusan age mate dina wai shi zata aura?..”wara idanu Ammi tayi da mamaki tace”u mean wanda tace zai turo din ba yaro bane?..”daddy yace”babban mutum ne wlh..wai sunanshi Professor Ahmad Kurawa”..Ammi tace”amma duk a ina ka samu wnn labarin?..”yace”Bilkisu na kira daxun..na kasa nutsuwa ne tun bayan mgnr mu da Alhaji Lukman sai na kira nace ta fadamun idan tasan wani abu tsakaninsu tace ita bata fada mata yace yana sonta ba ta kuma bani labarin shi wnn da takeso din”..ajiyar zucia Ammi ta sauke mai karfi tana fadin”wnn yarinya dai bansan irinta ba wlh..sbd rashin hankali duk cikin masu sonta ta rasa wanda zata kawo as wanda zata aura sai dattijo?..Allah ka shirya yarinyar nan”..daddy yace”Ameen..gobe in Allah ya yadda zan kai mgnr Attahir wajen Lamido muji ko zai hakura da wancan mgnr”..gyada kai Ammi tayi tana fadin”to Allah ya kaimu..Allah kuma ya tabbatar da alkhairi.

The next morning daddy ko breakfast baiyi ba ya tafi wurin Lamido..as usual ya sameshi tareda jama’a saida ya jira ya gama sallamansu tsaf snn ya matsa kusa dashi yana gaidashi…Lamido ya amsa yana dubanshi cikin mamakin abunda ya kawoshi wurinshi da sassafe haka..mostly sai rana ta farayi yake shigowa amma yau gashi da sanyin safiya…bayan shiru na wani lokaci daddy ya gama tattaro duk wani karfin halinshi kafin ya fara mgn kai a kasa”wata mgn ce dama ta kawoni Baffah”..Lamido yace”dama tunda na ganka wnn lokacin nasan akwai dalili..meke tafe dakai?..”kai tsaye daddy yace”akan batun auren yaran nan ne..kayi hakuri ba nufina inyi jayayya dakai ba amma wata mgn Alhaji Lukman Waziri yazomun da ita jiya wanda yasa nayi tunanin in sake kawota gabanka ko za’a samu maslaha”…kai Lamido ke gyadawa yace”ina sauraronka..wace mgn ce wnn?..”daddy yace”ina wnn yaro dan wajen Col Attahir marigayi?..”Lamido ya gyada kai alamar ya ganeshi..daddy yacigaba da cewa”shine wai ashe yake sonta..ya dade yana sonta fada ne baiyi ba sai yanxun..ranar da sukazo nan tareda waziri mgnr ce ta kawosu sai kuma suka ji cewa ka riga ka fidda mata miji..wnn dalilin nema yasashi rashin lafia har ya kwanta asibiti”..wani irin tsit Lamido yayi kmr baya dakin..tabbas biri yayi kama da mutum..shi kanshi yayi mamakin yanda yanayin yaron ya sauya lokaci guda..tausayinshi yaji ya kamashi meyasa Waziri bai sanar dashi ba?..ga kuma shi wancan yaron Najeeb ya zaiyi dashi?..bayan dogon tunani ya dawo da dubanshi ga daddy dake zaman jiran tsammani yace”shi kuma wancan yaron Najeeb ya zamuyi dashi”..da sauri daddy yace”saida na fara tuntu6arshi kafin na kawo mgnr gareka..ya kuma tabbatar mun da cewa akwai yarinyar da yakeso”…numfashi Lamido ya sauke kafin yace”idan Allah ya kaimu dare kazo mun da iyalan naka gaba daya”..cikeda farin ciki ganin ya kusa cin nasara yace”zan kawosu in Allah ya yadda..na barka lafia”…daga haka ya mike ya sake mashi sallama snn ya tafi…koda yaje gida ya sanar da Ammi yanda sukayi dashi ita kanta ba karamin farin ciki tayi ba..sai a lokacin ya samu yayi breakfast din da bai samu yayishi ba daxu.

A can Kano kuwa tunda suka koma Bobby bai sake walwala ba…shi ba mara lafia ba kuma shi ba lafiyayye ba gashi nan ne kawai..gaba daya duniar yake ganin tayi juyin waina dashi daga farin cikin da yake ciki kafin ya santa zuwa baqin cikin da yake ciku yanxu bayan sanin nata…bakin kokarinshi yakeyi wajen ganin bai bar ciwon da yakeji ya kwantar dashi ba amma ko Allah yasan ba karamin wahala yake ciki ba..rabonshi da samun isashshen bacci har ya manta…kullum idan ba sedative yasha ba bai iya yin baccin…yana zuwa hospital dinshi kullum saidai ba wani iya aikin yakeyi ba mostly idan yaje kwanciya yake shima yaji da kanshi…Mummy tayi fadan tayi nasiha tayi magiya kan ya dena dorawa kanshi damuwa amma kwata kwata ya kasa yakice abun a cikin ranshi…kawai imagining yake wai ga Aysha an daura mata aure da wani shikam yasan da kyar idan ba wnn ce ranarshi na karshe a dunia ba…shi kadai yasan halin da yake ciki sai kuma Nur daya fadama duk abunda ya faru…Nur yaji tausayinshi matuka sbd yasan yanda ya kwallafa rai a kan Lamido..ya kuma san irin son da yake mata ba gama garin so bane..so ne wanda zaiyi wahala ta samu maiyi mata irinshi a dunia indai ba iyayenta ba…so ne wanda idan ta kuskura ya su6uce mata to ta tafka babban asaran samun masoyi kamarshi…wnn dalilin yasa kusan kullum Nur na tare dashi tunda har yanxu students basu dawo hutu ba and suna dawowa clinical posting zasu wuce..shike kwantar mashi da hankali tareda assuring nashi cewa komai zaiyi daidai…jinshi kawai yake don yasan zaiyi wahala ace an fasa auren nata.
Yau da wuri ya dawo gida sbd ciwon kai da yake fama dashi…yayi nisa cikin tunani har bai lura dasu Mummy dake zaune a parlor ba kawai ya wuce flat dinshi…gaba daya suka bishi da kallo ganin har yanxu Bobby bazai dangana ya mika komai ga Allah ba…ko Sab da zai koma school wnn karon aunty sumy ce ta maidashi madadin shi da yake maidashi koda yaushe…gaba daya Mummy itama cikin tashin hankali take don ganinshi a wnn halin ba karamin daga hankalinta yake ba…mikewa tayi zuwa dakin nashi..yana zaune kan sofa ya zabga uban tagumi da hannayenshi har ta karaso ta zauna nan kusa dashi baisani ba saida takai hannu ta dafa shoulder dinshi ya dago da sauri yana kallonta…kallonshi takeyi itama kafin tace”so duk mgnn da nake fada maka baka dauka ba knn koh?..”ya wani kwabe fuska yana kallonta yace”Mummy to me nayi?..”tace”kaki ka mika lamuranka ga Allah mana..do u think wnn damuwan daka daurama kanka shi zaiyi sorting things out?..baka yadda da ikon ubangiji ba ne?..”hannayenta ya kama ya rike yana dubanta in a calm voice yace”na yadda da ikon Allah mana kawai zuciata ta kasa daukan rasata da nake shirinyi..inama kokari Mummy Allah kadai yasan halinda nake ciki..ciwo nakeji sosai a zuciata Mummy ban san me zanyi ya dena ba”..kama hannunshi tayi tana cigaba da kallonshi tace”na fada maka ka kwantar da hankalinka jikina yana bani cewa ita din matarka ce..idan Allah ya yadda kuma kai zaka aureta ba wani ba”..kallonta kawai yakeyi kmr bai gane me take fada ba..cikeda assurance ta sake cewa”yes..ina nan ina maka addu’a and bi’iznillah Allah bazaiki amsan addu’a na ba”..dan murmushi kawai ya saki without saying anything..gani yake Mummy na son kwantar mashi da hankali ne kawai amma taya al’amura zasu canxa bayan Lamido da kanshi yace ya tsayar mata da wanda zata aura…shidai fatanshi bai wuce Allah ya cire mashi ita daga zuciyarshi ba koya samu ya huta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button