Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Lamido na fita daga office din nashi kai tsaye inda classes dinsu yake ta nufa tanata faman kuka kaman wanda akama duka dan bazata iya komawa can wajen ba…a hanya suka hadu da Sa’eed da Billy da suka fito nemanta…tana hada ido dasu ta sake rushewa da kuka…yana mata ciwo that ya kirata da mai biye biyen maza a takaice dai yana nufin ita karuwa ce…tunda take ba’a taba fada mata mgn daya tsaya mata a rai kamn wnn ba…wato dama duk kallon da yake mata knn amma ya cuceta…tambayan dunia sunyi mata amma taki tsaida kukan ballantana ta fadi abunda ke damunta…saida kyar aka samu ta dakatar da kukan tareda yi musu bayanin abunda ya faru…gaba daya sukayi shiru Billy ta juya ta kalli Sa’eed shima ya kalleta suna hada ido kowa ya shiga kunshe daria…dagowa tayi tana kallon Bily ganin yanda daria ke neman kufce mata ta sake juyawa ga Sa’eed shima taga the same thing kawai saita kifa face dinta akan hannayenta ta sske rushewa da kuka…mikewa Sa’eed yayi da sauri ya karasa inda take yace”besty nidai ba ruwana wlh..Billy ce naga tana daria”…tun kafin ya rufe baki itama Billy ta matso inda suke tace”nima ba ruwana wlh..aishi kika ga yana daria”…dagowa tayi tana goge hawayenta bata cewa kowa komai ba kawai ta mike a fusace ta fice daga wurin sukabi bayanta da sauri ita kuma da taga haka kawai ta kwasa a guje ta haura sama…har kusan durkushewa suka kusa yi sbd daria…yanda ta fita a gujen ne ya basu daria sosai ba kadan ba…saida sukayi mai isarsu snn suka haura saman suma…kai class dinsu suka shiga basu sameta a ciki ba…ita kuwa dama tana haurawa can kusada class din karshe taje ta tsaya tana cigaba da hawaye…tana ganin shigarsu class dinsu tabi ta dayan staircase dake nan kusada inda take ta sauka qasa…kai tsaye gate ta nuf ta fita daga makarantan daga ita sai uniform dinta a jiki da wayanta a hannu…tana fita tayi dialing number baby…yana kan hanya shida driver dinshi yaga kiranta…yana dauka kafin yace wani abu yaji sheshshekar kukanta..muryanta na fita da kyar tace”Babyyy…”hankalinshi ne ya sake tashi sosai yace”baby meya faru?..why are u crying?..”da kyar ta sake cewa”baby kazo makarantan mu..ina bakin gate”…tun kafin ta rufe baki yace”gani nan zuwa yanxun nan..just stop crying okay?..”daga mishi kai kawai tayi tana kashe wayan…ganin zasu iya hangota daga nan inda take tsaye sai ta dan matsa gaba kadan ta samu inda ta tabbatar bazasu iya ganota daga cikin school din ba ta zauna…after like 20 mins Prof ya karaso makarantan…tun kafin ya kirata ya hangota nan inda take dan haka yace ma driver dinshi yayi parking mota shi kuma ya bude ya fita ya tsallaka titi zuwa inda take…tana ganinshi ta mike tana sakin wani kukan kaman wanda uwa da ubanta suka mutu…hankalinshi ya sake tashi sosai yana isa kusada ita yayi kasa da voice dinshi yace”baby girl a bar kukan haka mana indai baso kike ki karasar min da dan ragowar nutsuwata ba”…hannu takai ta share hawayen nan yaga idanunta sunyi suntum face dinta yayi jajir sbd kuka…da kyar ya samu ta dakatar da kukan suka tsallaka titi zuwa inda motarshi yake…da kanshi ya bude mata back seat ta shiga shima ya shiga driver already dama yana ciki dan haka ya tada motar suka wuce…bayan sun dau hanya ya tambayi inda zai kaisu Prof yace”ka kaimu valentino”…ba musu ya kama hanyan Valentino dasu…har suka isa baice mata komai ba banda kallonta da yakeyi yanajin kukanda ta kasa dakatarwa ba ta6a masa zuciya…suna isa ya bude mota ya fita itama ya bude mata ta fito…ya debo kudi masu yawa daga pocket dinshi ya bama driver yace”ga wnn ka samu ka koma gida malam Lukman idan mun tashi tafia zan tuka da kain”..ba musu malam Lukman ya amsa kudi tareda godia snn ya juya ya tafi…shi kuma ya nuna mata hanya alaman ta wuce ba gardama itama tayi gaba yabi bayanta…Vip section yayi musu reserving ba tareda yayi ordern komai ba don duk hankalinshi tashe yake sbd kukan nan da yaga tanayi…bayan sun zauna yayi facing dinta cikeda damuwa yace”baby idan baso kike ki fasamin zuciya ba ki bar kukan”…ba musu tayi kokarin tsayar dashi tacigaba da goge hawayenta…ya zaro handky daga aljihunshi ya shiga goge mata tears din dashi…batace komai ba sai lumshe ido da tayi har ya gama snn yace”now tell me abunda ya faru”…bata 6oye komai ba ta fada masa duk abunda ya faru tun daga ranan da yace bazatayi participating ba har zuwa daxu da maganganun daya fada mata…tunda ta fara mgn Prof yayi shiru yana kallonta har takai aya bai iya cewa komai ba…kallonta kawai yakeyi while gaba daya hankali da tunaninshi suna wani wajen…tsoro yakeji kada ace proprietor din nasu sonta yakeyi don a wnn labarin data bashi yasan definitely akwai lauje cikin nadi..bai yiwuwa ya dinga kishinta kawai sbd mahaifinta ya bashi amanarta…hankalinshi yaji ya tashi sosai sbd baison wani yazo ya kwaceta daga gareshi…ganin yanda yayi zurfi cikin tunani Aysha ta kira sunanshi..ya dago yana dubanta tareda sauke ajiyar zuciya still ya rasa abun cewa…turo baki tayi kaman zataci gaba da kuka tace”yanxu baby bazaka ce komai ba?..”wani ajiyan zuciyan ya kara saukewa kafin a hankali yace”inso inyi mgn da daddynki plss..when zaki hadani dashi?..”shiru tayi tana kallnshi cikeda mamaki tace”is that all u could say?..”kamo hannunta yayi for the very first time a rayuwarshi yace”baby duk wnn abun da kikaga yanayi its all out of love..kishinki yakeyi sbd yana sonki ni kuma banaso wani ya kwaceki daga gareni shiyasa nakeso ki bani dama inje Gombe muyi mgn da daddy”…kallonshi kawai takeyi full of suprise..like how on earth ma zai fara wnn tunanin..how could all that masifa da bala’in da yake mata turned out tobe love…how could this happened?..ina wnn zance akwai gayara cikinshi..sam bazai ta6a yiwuwa ba hakan bazai ta6a faruwa ba…ganin yanda tashin hankali da tsoron rasata ke tubuce kan face dinshi sai tayi kasa da murya tana binshi da kallon daya kusan zautar dashi tace”baby calm down plss…calm down wnn abunda ka fada sam ba haka bane…there is no way da za’ace wnn mutumin yana sona..bazai ma ta6a faruwa bane so relax..babu wanda zai kwaceni daga gareka am only yours”…girgiza kai ya shigayi still hankalinshi ba kwance ba yace”baby you won’t understand..na tabbata ko rantsuwa nayi yaron nan sonki yake bazanyi kaffara ba..idan ba haka ba why zaisa maki ido haka?..why zai hanaki participating kan abunda yasan ba laifi bane”…dafe goshi Aysha tayi tanajin yanda duk ya fadi kalmar son nan takejin wani irin radadi a zuciyarta..ita tanada yakinin ba sonta yakeba kawai yanayi ne sbd daddy ne ya bashi daman hakan amma ita tasan babu wani abu makamancin love a tsakaninsu…ganin yanda tayi shiru ta dafe kanta yace”so yanxun ma bazaki barni inje wurinshi ba kou?..baby anya kuwa kina sona?..”da mamaki ta dago tana kallonta ta wani kwabe fuska kaman zatasa kuka tace”haba baby how could you say this..”tana rufe baki yace”to baby idan bance haka ba me kikeso ince?..idan da gaske kina sona why kike gudun haduwana da mahaifinki?..why bakison inje sbd mgnr auren…”tun kafin ya karasa ta rufe mashi bakin da hannunta tana kallon tsakiyar idonshi da nata idon da har yanxu bai dawo normal ba tace”dan Allah baby stop saying this?..how could you say bana sonka?..wlh ina sonka..i love u sosai”…ta karasa mgnr hawaye na ske ciko idanunta…zuwa tayi gareshi sbd tasan zai share mata hawaye kuma yasa ta manta da damuwan da take ciki amma shima sai gashi yana neman kara mata akan wanda take ciki…hankalinshi ya sake tashi ganin zata fara mishi kuka yace”Noo..karki bari su zubo dan Allah”…ai kamar cewa yayi ma su zubo nan suka shiga sintiri kan fuskanta…sake matsawa yayi jikinta sosai ya lumshe ido kawai sai ya janyota jikinshi yana sauke numfashi…soyayyarta yakeji na sake ratsa ko ina na jikinshi…yana sonta fiyeda tunani amma gashi kiri kiri yana nema ya rasata sbd tsoron ta hadashi da mahaifinta…kuka takeyi sosai a jikinshi tayi wani luff kaman jariria..baiyi yunkurin hanata kukan ba sai shafa bayanta da yakeyi a hankali…saida suka dauki lokaci mai tsaho a haka kafin ya samu ta tsayar da kukan snn ya dagota daga jikinshi ya shiga goge mata hawaye…idanunta lumshe har ya gama snn ya sake yin kasa da murya yana kallon bakinta da take pouting yace”Aysha please!..ki bani dama inje in ganshi kada wani yazo daga baya ya shiga tsakanina dake”…sake kwa6e fuska tayi zatasa wani kukan da sauri yace”dan Allah Noo..why kikeson tayar min da hankali ne..”baki a tunzure tace”ni ka dena mgnr za’a kwaceni daga gareka banaso..mgnr zuwa wurin daddy kuma ka bani lkci in fara mgn da Hammana duk yanda mukayi dashi zakaji”…kallonta yake kafin yace”U sure?..”ta wani langabe kai tana kallonshi tace”yes sure”…murmushi ya saki mai kyau tareda fadi”na yadda dake my baby..yanxu me kikeso a kawo maki kici..”murguda baki tayi tana makale shoulder dinta tace”ooh bazanci komai ba tunda har yanxun baka yadda ina sonka ba”..another smile ya kara saki kafin yace”sam ba haka bane baby kawai dai inajin tsoro ne..kinsan duk lokacinda kake son mace mai kyau hankalinka bazai ta6a kwanciya ba idan ba daura maku aure akayi ba”…dan murmushi itama ta saki murya can kasa tace”to ka kwantar da hankalinka in Allah ya yadda Aysha Ahmad Lamido batada mijinda ya wuce Professor Ahmad Kurawa”…sake fadada smile dake fuskanshi yayi yace”to Allah ya nuna mana ranan da Aysha Ahmad Lamido zata zama property din Prof Ahmad Abdu Kurawa”…murmushi itama ta saki shima yanayi kaman ba sune ke 6acin rai a while ago ba…nima kaina da nake dauko maku rahoto bansan lokacin da na furta”soyayya ruwan zuma”..akace idan kasha kaba masoyi…i hope dai gaba dayanku kunya ba masoyanku?????…lol

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button