Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Gombe…

Tsaye take a kitchen tana suyan Pancake fuskan nan a tamke kaman wanda aka aikoma da sakon mutuwa…daga gefe kuma Ammi ce tana kokarin hadama Daddy breakfast dinshi a kan tray sai kuma mai aikinsu dake juya pepper soup a kan gas…bayan ta gama hadawa ta dauki tray din kafin ta fita ta dubi Aysha dake faman tura baki tace”kuma wlh idan bakiyi sauri kin gama ba har Lamido ya fita bakuje kun gaisheshi ba zakiga yanda zanyi dake a gidan nan”..mai aikinsu mai suna Asabe tace”da kin barta hajia zan karasa wlh..ita taje tayi shiryawanta”…Ammi tace”bazan barta ba Asabe na lura tunda ta dawo gidan daga kallo sai chatting ta iya bata tsinana uwar komai ko dakinsu saidai Husna ta share..anjima ma ita zaku bawa suyan fried rice tayi ai ba bayi ta ajiye dan sunayi mata girki ba”…tana gama fadin haka ta fita daga kitchen din…ita dai Aysha na tsaye tana aikin gabanta ko juyawa batayi ba amma fuskan nan kaman zatasa kuka…ko Allah yasan ba mai son girki bace ita…gara a bata duk wani aikin gida zatayi amma ta tsani girki shiyasa ko a makaranta Billy keyi musu girki…Asabe na ganin Ammi ta fita ta kashe gas din gabanta snn ta matso inda Aysha take tana amsan spoon din hannunta tace”kawo in karasa kinji indo…ki tsaya daga nan ki huta idan mukaji zata dawo saiki kar6a kicigaba”…nan da nan kuwa ta sakin mata shi tareda matsawa gefe tace”nagode Baaba”…Asabe tacigaba da suyan Pancake ita kuma ta rungume hannu tana kallonta…wayanta dake aljihun jean dinta ne ya fara ringing…ta zaroshi da sauri tana sakin wani smile ganin Prof ke kira tasan yanxu zaiyi flushing wnn 6acin ran da take ciki…saida ta gama kwa6e fuskanta tayi readyn shagwa6a snn tayi picking…a daya 6angaren Professor yace”my baby girl”…ta wani cunno baki sai kace yana ganinta tace”umhhm”…yanajin yanda tayi replying yasan akwai matsala…if u see yanda ya gigice zakasha namaki…fadi yake”my baby please what happened…waya ta6amin ke?..”ta sake narkewa tana tale baki tace”baby Ammi ne”…yace”Subhanallah me Ammi tayi maki?..hope ba dukanki tayi ba?..”tace”cewa tayi sai nayi suyan Pancake…kuma ni baby banason girki fa”…tana iya jiyo sautin dariyarshi kafin yace”eyya sorry my baby gaskia Ammi bata kyautamin ba..why zata turamin mata kitchen?..”tana sake narkewa tace”shi na gani nima baby..aidai in munyi aure bazaka na sani girki ba koh?..”yace”wane ni in saka princess dina girki…duk abunda mukeso ordering zamu dingayi ko mu dauko chefs su dafa mana”…lokaci daya ta wage baki tana smiling tace”yauwa my Professor..my very own baby durling”…saida ya lumshe ido daga can inda yake ya wani dora hannu kan chest dinshi yace”ohhh that sounds sweet baby…i love u”…tace”i love u more baby”…mai aiki dai na aikinta tana sauraron yanda take zuba shagwa6a tana murmushi…ko su da suke aiki gidan sun san Aysha mai son shagwa6a ce duk kuwa da cewa iyayen nata ba shagwa6ata suke ba…haka taciga da wayanta har aka gama suyan Pancakes din snn ta dora wormern da aka zuba kan tray ta fita dashi parlor…dining ta karasa ta ajiye snn ta nufi parlorn daddy…as usual suna zaune dinning suna karyawa shida Ammi…ta karasa ciki bayan ta nutsu snn ta gaisheshi ta bar parlon…tana fita ta samu su Husna a dinning itama ta karasa ta zauna suka fara breakfast…Ammi da daddy suka fito tare bayan sun kammala suma…Ammi na rikeda briefcase dinshi zasuje gaida Lamido shi da yaran daga can kuma zai wuce Abuja wurin aikinshi…su Aysha na zaune parlor suma sun gama nasu breakfast din kowacce sanyeda katoton hijab sbd zaaje gaida Lamido…Daddy ya kalli yanda sukayi reras a parlon kowa tasha hijab kawai ya girgiza kai yasa daria…ya lura har wani nutsuwa na musamman sukeyi duk zasuje wajen Lamido snn kaf jikokinshi ba wadda take zuwa mishi ba tareda hijab ba dan fada yake sosai…bayan ya gama dariyan ya kallesu one by one yace”are we good to go?..”suka hada baki wajen fadin”yes daddy”..snn yace”to ku tashi muje”…gaba daya suka mike suka fita…shima suka fita tareda Ammi…har jikin mota ta rakashi ta bude mishi kofa da kanta ya shiga snn ta ajiye briefcase dinshi..suma su Aysha nasu motan suka shiga tana kallon Ammi tana sallama da mijinta cikin ranta tace” muma dai muzo muyi auren nan wlh..haka zanje inta yima babyna yana lalla6ani”…Yusra dake jikinta tace”Adda me kika ce?..”ta saki murmushi tana shafa kan Yusra tace”ba komai habibty…bance komai ba”…motan daddy ne ya fara fita daga gidan snn nasu.

Kofar gidan Lamido motocinsu sukayi parking…daddy ya fara fitowa suna biye dashi zuwa ciki…katoton parlon Lamido dake daukeda two sets of kujeru suka shiga…yana zaune kan one of kujerun sai wasu mutane biyu zaune a kasa suna gaisheshi…karasawa ciki sukayi daddy ya zauna kasa ta right side dinshi su kuma suka zauna his left side…kyakkyawan bafulatani da a kallon farko da kayi masa zaka gane attajiri ne snn kuma yanada dattako…kamanninsu daya da daddy saidai haske da daddy zai nuna masa shima ba sosai ba…bayan ya sallami mutum biyu dake zaune ya juya yana duban daddy yace”Ahmad har an fito?..”cikeda respect daddy yace”na samu fitowa Baffa…barka da safiya”..yace”barka dai ya iyalin?..”kai a kasa yace”suna nan lafia Baffa…tace a mika mata gaisuwa kafin ta shigo”..gyada kanshi yayi yace”to mashaAllah”…sai kuma ya juya ga su Aysha ya dan saki murmushi yace”mutanen Lamido”…da ladabi suma suka dukar da kai suka gaisheshi…ya amsa tareda tambayansu makaranta sukace Alhamdulillah…idonshi ya tsayar kan Aysha kafin yace”ke saura wata nawa ki gama karatun ne Aisha?..”tace”ba watanni bane Lamido saura shekara daya da rabi”..gyada kai yayi yace”to ba laifi Allah ya kaimu..Allah yasa a gama lafia”..sukace” Ameen Ameen”…sun dan jima suna hira har wani qanin daddy ya shigo shima da ‘ya’yanshi…suka gaisa dashi snn daddy yayi salama da mahaifin nasa suka fita…kai tsaye ya shiga motanshi suma suka shiga nasu bayan ya sallamesu suka koma gida shi kuma suka fita daga Estate din.

Kwanci tashi abun ba wuya har sun cinye sati biyunsu cif sun fara shirin komawa makaranta…tunda satin komawa ya shigo Aysha take kunci tana baqin ciki sam batason komawa wlh especially idan ta tuna wnn dan rainin hankalin inyamurim Proprietorn nasu…sam bata kaunarshi wlh…neman hanyan da zata sanar da Ammi kawa take amma ta rasa dan haka ta tsiri 6ace 6acen rai sai ta zauna a parlor da gayya tayi tagumi wai tanaso Ammo ta tambayeta abunda ke damunta ta fada mata amma Ammi tayi biris da ita kaman batasan tanayi ba…abu daya dake dan yaye mata wnn damuwan shine Prof dinta…zuwa yanxu soyayya sukeyi sosai sai kace wanda sukayi shekara da shekaru a tare…yana mugun shagwa6ata kaman yanda takeso ita kuma tana sake falling mishi.

Kaman kullum yau ma tana zaune ta buga uban tagumi a parlor wai ko Allah zaisa Ammi ta tambeyi meke damunta saidai abunda bata sani ba shine Ammi ta rigada ta ganota tasan duk wnn attitude da take displaying kilan sbd komawa makaranta ne shi yasa taki kulata…Ammi ta shigo parlon waya kare a kunneta tana mgn da Aunty Fiddausi…bayan ta gama ta dauki remote tana kokarin kunna tv Aysha da taga still bazatayi mata mgn ba ta dan marairaice tana dubanta tace”Ammi..”ba tareda ta bata attension dinta ba tace”na’am”…sake narkewa tayi tace”Ammi bazaki tambayi meke damuna ba?..”dan juyawa Ammi tayi tana kallonta kafin yace”what’s wrong..are u sick?..”sake marairaicewa tayi ta koma kalar tausayi tace”Ammi dan girman Allah ki cema daddy bazan koma makaranta ba plsss”…fuska daure Ammi tace”sbd me?..”tace”bana sonta wlh kuma yanxu ba wani karatu akeyi ba sai shegen takurawa mutane”…gyada kai Ammi ta shiga yi tace”dama nasan karshen zancen knn…kilan kinje kinyi laifi anyi miki fada shine zakizo kice mana bazaki komaba kuma kike tunanin zamu yadda dake kaman bamusan halinki ba koh?..to bari kiji in fada maki babu fashi komawa makarantanki gobe idan kuma kika sake kika sake min mgnr nan sai kinci ubanki wlh…daidai nake dake ai kinsani”…nan da nan ta fara hawaye tana cewa”nifa Ammi Allah na gaji da Kano inaso in dawo gida…kuma Proprietor dinmj inyamuri bashida mutunci wlh”…Ammi mikewa tayi zata bar parlon tace”ur problem not mine..nidai na gama mgn kuma Allah yasa kar ki dena kukan nan kiga yanda zanyi dake a gidan nan…shashasha kawai”…daga haka Ammi ta wuce dakinta…ita kuma hajia indo ta rungumi pillow tana sake rushewa da kuka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button